22

343 51 4
                                    

Muna kwance a 'dakin mu muna hira bayan sallahn magariba se ga mama ta shigo 'dakin mu da sauri cewa tayi dani

"Tasneem yi maza ki sa hijabi muje asibiti dan Allah"

Duk miqewa tsaye muka yi a tare, a firgice nace mata

"Umma lafia, waye bai da lafia?"

Cewa tayi

"Dan Allah ki sa hijabi muje, wallahi yanzu Ummin Ameerah ke gaya mun wai suna asibiti, sun kai Ameerah asibiti tana ta zubar da jini"

Zaro ido nayi nace"Subhanallah", Hijabi nayi sauri na 'dauka sannan na 'dauki waya ta na bi Umma a baya muka fice, driver ne ze kai mu saboda Abba be dawo ba yau da wuri, mota muka shige da sauri sannan driver ya fara tafiya, waigowa nayi na kalli Umma da hankalin ta ke tashe, cewa nayi da ita

"Amma Umma nakuda take yi ko?"

"Ina ganin haka, amma se nake ganin kamar cikin ta be isa haihuwa ba"

Nima da mamaki nace

"Kinsan ko da na bar gidan Maheer cikin ta wata 4 ne, yanzu kuma ina cikin wata na hudu a gida, a lissafe dai cikin ta wata takwas ne, Allah dai ya raba su lafia"

"Ameen ya rabbi"

Sannan ta ce ma driver

"Malam Danjuma yi haquri hankali na a tashe ban gaya maka asibitin da zamu ba"

Malam Danjuma yace

"A'a babu komai Hajiya, ba Garkuwa Hospital bane ai gashi har mun qaraso"

Umma ce tace

"Eh hakane ikon Allah har mun kawo ban ma lura ba, to mu shiga ciki kayi parking"

Amsa mata yayi da "toh hajia" sannan ya shige da mu cikin harabar asibitin, yana parking muka sauka daga motar muka shige ciki, Umma ta kira Ummi ta tambaye ta suna ina, se Ummi ta ce mata mu hauro sama, suna wurin Labour Room

Labour Room muka nufa nan muka samu Maheer da Ummi a tsaye sunyi cirko cirko, gaisawa muka yi da su sannan Umma tace

"Ya jikin nata? Wai me ya faru ne? Labour take yi?"

Ummi ta amsa mata da

"Yaya wallahi ga ta nan dai, nima Maheer ya kira ni yace mun tin da la'asar tace mishi cikin ta yana mur'dawa, To abun be yi tsanani ba se yanzu da ya kirani yace mu ha'du a asibiti, se bleeding kawai take yi, yanzu dai sun shiga da ita Labour Room se abunda Allah yayi"

Umma  tace

"Oh Allah, Allah ubangiji ya fitar da ita ya rabasu lafia"

"Ameen" muka ansa gaba 'daya da shi.

Mun kai kusan awa daya a tsaye muna ta zagaye se ga Mama ta zo ita ma, nan dai aka ha'du ana ta adduoi, ana haka se ga Dr ya fito daga labour room, Dr Adeel na hanga da mamaki na ke ta kallon shi har ya iso inda muke tsaye, har qasa ya duqa ya gaida su Umma nima gaida shi nayi ya amsa sannan ya miqo ma Maheer hannu suka gaisa, Umma tace mishi

"Adeel dama kai ka ke tare da ita? To ya jikin nata?"

Cewa yayi

"Eh Umma ni ne, da sauki Alhamdulillah, mun sa ka mata ruwan naquda kuma Allah da ikon shi ba ta wani jima ba ta haifo shi"

Duka a tare a ka ce "Alhamdulillah"

Sannan se ya cigaba da cewa

"Amma dai akwai matsala "

Mama  tace

"Matsalar me kuma?"

Dr Adeel yace

"Yaron ya koma sakamakon wahalar da ya sha a cikin ciki, tana haifo shi be fi minti 'daya ba ya rasu"

"Innalillahi wainna illaihir rajiun " kawai kowa ke fa'da, haquri ya bamu sannan Umma ta tambaya in zamu iya ganin ita Ameerahn, cewa yayi mu bari har Nurse ta gama kintsa ta in aka maida ta 'dakin hutawa se mu je mu ganta

Dr Adeel ya ja Maheer yace ya zo akwai bayanin da ze mai, nasan bayani ne akan lafiyar Ameerahn.

*** Bayan an maida Ameerah 'dakin hutu muka shiga mu ka same ta, sannu akayi ta mata sannan su Umma sukayi ta bata haquri, bayan an 'dan jima aka shigo da babyn muka ganshi, kyakkyawa ne sosai fari tas yana kama da Maheer amma sai dai farin Ameerah ya biyo duk da Maheer fari ne amma Ameerahn tafishi haske,munyi alhilin rasa shi sosai

Umma tace in zauna da Ameerah mu kwana tare tinda tasan zuwa gobe za'a sallame ta,ba yadda na iya haka na zauna da ita, bayan sun wuce na tashi na je massalacin da ke cikin asibitin na yi sallah, ko da na dawo Ameerah har tayi bacci, wuri na samu na zauna kusa da ita, Ina cikin danna waya ta Maheer ya shigo, cewa yayi

"Sannu da zama"

Na amsa mai da

"Yauwa Sannu"

Ba wanda ya qara cewa komai a cikin mu, waya ta ce ta fara ringing har ta ja Ameerah ta farka, kara wayar nayi a kunne na tare da yin sallama, kasancewar banda number 'din ya sa nayi shiru dan inji me za'a ce, muryar namiji naji, nan yake fa'da mun Dr Adeel ne, cewa yayi dan Allah in fito in same shi yana jira na a wurin zama a jira likita wato reception, amsa mai nayi da "toh gani nan zuwa" , ce ma Ameerah nayi zan fita in dawo "Toh" ta amsa mun da shi sannan na wuce na barta ita da mijin ta.

A tsaye na hango Dr Adeel, ya riqe rigar saman shi a hannu yana danna waya, Dr Adeel dogo ne sosai, kuma kyakkyawa ne me faffa'dan qirji, shi ba siriri bane kuma ba ya da qiba sosai, fari ne tas kuma fuskar shi na da saje wanda ya qara mai kyau, yana hango ni ya fara mun murmushi, ni dai in akwai abunda yake burge ni da shi to be wuce fara'ar shi ba, nima murmushin na maida mai, sallama nayi mai ya amsa sannan yace

"Sannu da zuwa sarauniyar mata"

Amsa mishi nayi da

"Yauwa kai ma sannun ka"

Wuri ya nuna mun ya mun alama da in zauna, Ina qoqarin zama yana mun murmushi se ga Maheer ya fito ze wuce, wani irin kallo ya bi ni na da shi sannan ya kalli Dr Adeel shima ya ja jiki ya wuce yana hararan mu

Hhhhh Wai Harara Lallai Maheer 'din nan😂😂😂😂kadan ka gani ma, bari se an kawo maka IV tukunna ma.

To readers ku taya ni muyi ma Ameerah jaje, Allah ya bata lafia ya kawo rayayye ya sa me ceton ta ne ranar gobe qiyama

#TasDeel our new couple ❤️❤️❤️

Dedicated To Chuchujay

Aisha Ameerah ❤️❤️

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Where stories live. Discover now