28

369 54 22
                                    

Bayan Wata Biyar

"MashaAllah, Alhamdulillah Allah na gode maka, Allah ubangiji ya raya mana, ai ko Noor na dawowa zaki ganni, ki shafa mun kan Baby ta , se nazo ganin ta"

Bayan mun gama wayar na fara rawan jinda'din , yanzun nan Hajarah ke sanar mun cewa ta haihu, farin cikin da nake ciki zaka 'dauka ni ce na haihu, Adeel na kira ma na gaya mai, murna ya taya ni sannan yace in je kawai ze same ni acan tinda ya ga na matsu in tafi ina cikin farin ciki da yawa, keke napep nace mishi zan hau tinda shi ze zo dauka na, fita da mota na be da amfani, da sauri sauri na shirya sannan na kulle gidan na fito, me gadi nayi ma sallama sannan na fita, keke napep na tare sannan na ce mishi zanje asibitin 44, shiga keke napep 'din nayi ko tambayar ku'din banyi ba, muna kaiwa asibitin na miqa me keke napep duba 1, cewa yayi dani ba chanji, murmushi nayi na ce mishi na bashi kyauta albarkacin haihuwa da akayi mun, murna ya taya ni sosai sannan na shiga asibitin, a waje na ga Ahmad mijin ta yana waya, se da ya gama wayar na taya shi murna sannan yayi mun jagora muka tafi, Ina shiga 'dakin ko ta kan ta ban bi ba na je wurin gadon babyn na tsaya, leqa ta nayi nace

"Assalamu Alaikum Sabuwar masoyiya"

Bacci babyn ta ke ta yi hankalin ta kwance, kallon ta nake yi cike da so da qauna, Hajarah ce tace

"Lallai besty kin ce wani abu, ko magana baki yi mun ba kika wuce wurin yarinyar ki ko? Nagode miki"

Dariya nayi nace

"Yi haquri Tsohuwar masoyiya"

Rungume ta nayi nace

"Sannu da qoqari Allah ya biya ki"

Cewa tayi dani

"Ke dai ki ka sani nayi fushi"

"Yi haquri kinji, Ina Mama? Ke da waye anan?"

Ce wa tayi

"Tana cikin toilet tana jinki"

Dariya nayi nace

"Shiyasa na ga Ahmad yaqi shigowa kenan"

Qasa tayi da muryar ta tace

"Ke abun kunya yayi shiyasa yake ta noqewa, da Mama ta fita anso ruwan zafi a wurin nurses se yazo kusa dani yana ta rungume ni, muna cikin haka se ga ta ta shigo, shiyasa tinda ya fita har yanzu be qara shigowa ba"

Dariya muka kwashe da shi gaba 'daya, sannan nace

"Ahhh Lallai anyi abun kunya kam, ga baban nawa da ma akwai kunya"

Sannan na qara cewa

"Ya sunan babyn? Dan nasan ku en gidan ku a randa aka haifi yaro ake fa'dan  sunan shi"

Murmushi tayi tace

"Takwarar ki ce"

Zaro ido nayi nace

"Ban san qarya fa besty"

Mama ce ta fito daga bayi tace

"Ba qarya take miki ba, sunan babyn ku Tasneem, sunan naki akwai da'di ai kuma ke mutumiyar kirki ce Tasneem"

Murmushi nayi ido na ya cika da hawaye ina qoqarin yin kuka, gaisawa mukayi da mama sannan na dinga ma Hajarah godia da irin soyayyar da take nuna mun, a haka dai muka dinga hira har Adeel yazo, shima fa'da mishi nayi anyi mun takwara nan ya dinga ta ya ni murna, da zamu wuce ya cire dubu 100 ya 'daura ma babyn akan jikin ta, godia suka yi mishi sannan muka tafi, muna cikin mota ya kalle ni ya ga ina ta farin ciki se yace

"Ikon Allah kenan ga Tasneem babba ga Tasneem qarama"

Murmushi nayi cikin jinda'di nace

"Kuma sunan baban mu 'daya fa"

Cikin mamaki yace

"Ai kuwa wallahi, sunan ki TASNEEM AHMAD ita ma babyn sunan ta TASNEEM AHMAD, gaskia dole kiji da'di, ai ko dole mu zage muyi abunda ya kamata"

____________________________
Ranar suna ko na nuna bajin ta, saboda ni na 'dauki nauyin dik snacks da drinks da ruwan da aka sha, anyi gagarumin suna anci an sha, ba bu wanda ze ce be ci ya qoshi ba, qawayen mu su Hafsah dik sun halarta, Ina waigowa na ga su Chuchu, Fadeelah, Ayush Marte, Hajja Gana, Meenah, Zeey Lalan, Ummi, Fateeteey,Maryam, Maamah,Fati Ustaz da su Khadeeyjah ba'a cewa komai, ita Khadeejah har da qanwarta Zarah tazo shima yayan su Ahmad da ya kawo su se da ya aiko a bashi na shi rabon, akwati 'daya nayi ma Baby na kayan saka wa, sannan na siyan ma me jegon ita ma Super wax da wani Lace me tsada, Hajarah taji da'di sosai tana ta yi mun godia, yarinya ko taci Suna na TASNEEM amma ana kiranta FARHA, ranar sunan a gidan su Hajara na kwana dan Adeel da kanshi ya ce in kwana, Ina riqe da Tasneem Farha se ga text message ya shigo waya ta karantawa nayi na ga an rubuto mun

"Assalamu Alaikum masoyiya ta, Ina taya ki farin cikin samun takwara, Allah ubangiji ya raya muna TASNEEM ya yi mata albarka, daga masoyin ki na har abada"

Ni dai mamaki kawai nake yi kuma abun da yake bani haushi shine yadda ake boye number 'din da ake mun message da shi dik da an dade da akayi mun irin text 'dinnan, Tin ranar 'daurin aure na da akayi mun to ba'a qara yi mun ba se yau, ko ma dai waye shi ya sani.

Ya kamata mu je mu taya Tasneem murnar samun takwara, Allah ya raya muna Baby TASNEEM AHMAD (FARHA)

Dedicated To Chuchujay

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Where stories live. Discover now