42

307 56 14
                                    

Qarfe 5:30 na tashi, alwala nayi sannan nazo na tashi Jabeer ya tashi yayi Sallah, shima alwalan yayi sannan ya fita daga 'dakin domin zuwa massallaci, 'daki na na tafi nayi Sallah sannan na shiga bayi nayi wanka, na gama saka kaya kenan Jabeer ya shigo 'dakin, cewa yayi

"Har kinyi wanka?"

"Eh wallahi ina kwana"

Cewa yayi

"Lafia lau Alhamdulillah, kin tashi lafia?"

Amsa mishi nayi da

"Lafia lau Alhamdulillah"

Cewa yayi

"Madallah, Bari inje in kwanta zan koma bacci"

Murmushi nayi nace

"Toh shikenan"

Qara cewa yayi

"Do you care to join?"

Se nace mishi

"Aa, ka dayyi baccin ka"

"Ba kya so kiyi bacci kenan, Anyways, se na tashi ko"

"Toh" nace mishi sannan ya tafi, dubu agogo nayi na ga qarfe 6:40, kwanciya nayi da niyyar in qarfe 8 tayi se in fito in je wurin Maa.

A zabure na farka saboda kwankwasa qofar da naji anayi, duba agogo nayi na ga qarfe 9 har tayi, da sauri na sauka a kan gadon na je na bu'de qofa, Maa nagani a tsaye a bakin qofar ta sha toka, ran ta a 'bace yake, cewa nayi da sauri

"Maa Ina kwana "

Harara ta banka mun tace

"Da ban kwana ba zaki ganni? Yanzu Qarfe nawa?"

A daburce nace

"Qarfe 9, kiyi haq.."

Katse ni tayi tace

"Ki same ni a Kitchen 'din qasa"

Sannan ta wuce, da sauri na koma 'daki na shiga bayi na wanke fuska na sannan na sauka qasa da sauri, tsayawa nayi ina ta kalle kalle saboda bansan ina ne Kitchen 'din ba, qarar abu ya fa'di qasa naji, bin inda naji qarar nayi sannan na tura qofar na shiga, Maa na gani a tsaye ita kuma Asabe ta na share in da Glass Cup ya fa'di ya fashe, cewa nayi

"Maa gani"

Ce mun tayi

"Ai na ganki"

Sunkuyar da kai na qasa nayi sannan tace

"Jiya ban gaya miki sharu'da na ba amma yau zan gaya miki, na farko bana son latti, bana son raini, bana son qazanta, sannan kuma daga yau duk wani abinci da za'a dafa a gidan nan ke zaki dafa shi, ba'a ba ma'aikatan gidan nan abinci saboda duk cikin su ba wanda ba na biya, kowa da ku'din shi ya ke siyan abinci, ba'a yi mun albazaranci, duk abunda zaki dafa ze zama karkashin umurni na, bana son yawo, bana son mutane suna zuwa gida na, kinji ni ko?"

Cewa nayi

"Eh Maa, Inn Sha Allah zan kiyaye"

"Allah ya sa, Asabe zata fa'da miki abunda za'a girka"

Cewa nayi

"Toh Maa"

Sannan ta fice, tsayawa nayi kawai saboda na kasa cewa komai, Ya Allah me na jawowa kai na, nan gida ne ko kurkuku, Jabeer nake aure ko Maa?, Tambayar da na dinga yi ma kai na kenan, Asabe ce tace

"Amarya bari in nuna miki inda abubuwan suke"

Cewa nayi

"Toh Nagode"

Nuna mun inda komai yake tayi, sannan ta fa'da mun abunda za'a girka, gaya mun adadin abunda ake dafawa tayi sannan ta matsa gefe ta samu kujera ta zauna ta raku'be tana kallo na, bayan na kammala komai se na fara tunanin abunda Maa tace na ba'a ba masu aiki abinci, abincin da na dafa iyakan shi na bakin mutum hu'du ne, ni, Jabeer, Maa se Jiddah, bayan na gama ha'da duk abunda zan kai dining table se Asabe ta taso da niyyar 'dauka ta kai, cewa nayi ta barshi zan kai, plate na 'dauka na iban mata abincin sannan na ce mata

"Mama ga wannan abincin kici "

Zaro ido tayi tace

"Hajia ai ni tun da nake ban ta'ba cin abincin gidan nan ba, ruwa ka'dan nasan ina sha a wannan gidan"

Ce mata nayi

"Maa 'din zata zo kitchen 'dinne ?"

Cewa tayi

"Aa ba zata shigo ba, Yau ma nayi mamakin ganin ta a Kitchen 'din saboda ta kai wata shida bata shigo ba"

Zaro ido nayi nace

"Wata shida??"

"To wa yake dafa abinci?"

Cewa tayi

"Jiya ta sallama me dafa abinci kafin a kawo ki"

Cewa ta sake yi

"Bana ta'ba abincin saboda ina tsoron Allah kuma duk wayau na Maa ta fini, tana da wanda yake duba mata yawan abincin store 'dinta"

Girgiza kai nayi sannan na ce a cikin zuciya
"Lallai wannan Maa din ba mutuniyar arziki bace" sannan a fili nace

"Toh Allah ya kyauta, kar ki damu a cikin nawa na 'diban miki"

Godia ta dinga yi mun sannan na fice da tray 'din na kai inda na ga inda shine dining table 'din, Maa ce ta sakko ta bu'de abincin ta duba sannan tace zata je wanka in ta fito zata zo ta karya, Jiddah ce na ga ta sauko, Ina ganin ta na fara mata murmushi har qasa ta duqa ta gaida ni, amsa mata nayi da fara'a sannan ta samu wuri ta zauna a kan 'daya daga cikin kujeran dining 'din, Jabeer ma saukowa yayi ya zauna shima, 'daukar serving spoon nayi da niyyar zuba musu abinci se Jiddah tayi saurin cewa

"Mama se Maa ta sakko ake cin abinci "

Kallon ta nayi sannan na kalli Jabeer, be ce komai ba se ya cigaba da kallon wayar shi, shiru shiru har kusan awa 1 ana ta jiran Maa ta sakko amma bata sakko ba, Jiddah ko se hamma take yi alamun tana jin yunwa, tausayin ta ne ya kama ni gashi kuma banda yanda zanyi, se bayan kusan minti 30 Maa ta sakko, zama tayi tace in zuba mata abinci, bayan na zuba mata se na 'dauki plate 'din Jabeer zan zuba mai abinci se ya ce

"Se Maa ta gama ci tukunna"

Jiki na a sanyaye na aje plate 'din na rufe warmer 'din na zauna, a hankali take cin abinci hankalin ta kwance tana danna wayar ta, tana gama cin abincin se ta tashi ta wuce, ce musu nayi

"Zan iya zuba muku? "

Se Jiddah tace mun "eh", zuba musu nayi suka fara ci, Jiddah ko se loma takeyi kamar bata ta'ba cin abinci ba, Ina cin abinci amma ina ta satar kallon su ita da Jabeer, Lallai a gidan nan na lura akwai azabtarwa.

Dedicated To Chuchujay

Aisha Ameerah ❤️

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Where stories live. Discover now