3

765 81 20
                                    

Tashi nayi daga inda Maheer ya barni da niyyan zan koma 'daki, na kai bakin 'kofar 'daki na kenan naji muryar Umma tana kira na, amsawa nayi sannan na nufi dakin Umma, zaune na tarar da ita a kan carpet tana duba littafin da take ajiyan lambobi, cewa tayi da ni

"ya kukayi da Abban ki"

"Umma ya sanar da Maheer wata sati me zuwa za'ayi auren mu, wallahi Umma gaba na fa'di yake tayi"

Dogon numfashi Umma ta ja Sannan ta ce

"ki bar ma Allah komai, nasan mahaifiyar Maheer zata amince da izinin Allah dan haka ki daina tada hankalin ki kinji"

'Kara gyara zama nayi sannan nace

"Amma Umma makomar auren ki fa, a gani na Abba ya na nan akan bakan shi, dan wallahi da gaske yake maganar"

Dafani tayi sannan tace

"Allah ya zaba abunda ya fi zama alheri, komai kika ga ya faru to mu'kaddari ne daga ubangiji, irin tamu jarabawar kenan, yanzu dai abunda nake so da ke shine ki wanke fuskan ki, ki shirya ki je gidan su Haajarah , wata 'kila zaki ji sanyi a zuciyar ki"

Murmushi nayi sannan nace

"Toh shikenan Umma ta, inna wanke fuskan zan wuce, 'kila bazan le'ko in miki sallama ba, ba zan da'de ba zan dawo in Allah ya yarda"

Gyada kai tayi sannan tace

"Toh Shikenan ba damuwa se kin dawo, ki gaida min da Hajia Hauwa"

"Zataji Inn Sha Allah, se na dawo"

________________________________

"Amma wannan wani irin hukunci ne Mahaifin yarinyar nan ze yanke, se kace yana neman kai da ita"

Hajia Khadijah tace ma 'danta Maheer

"Haka dai yace Mama, nima dai abun ya 'daure mun kai"

Maheer yayi maganar a sanyaye

"Toh shikenan, babu damuwa, ni na yaba da hankalin Tasneem kuma nasan bazata bamu kunya ba da yardar ubangiji babu damuwa, Alhamdulillahi tinda dama yawanci dik mun gama siyayyar kayan lefen ka, gidan zama kuma ai kana da shi,  yanzu gayyatar mutane ne dai nasan se an ta tsegumi amma ba damuwa"

"Ai mutane ba'a masu dai dai Mama, yanzu dai shirye shirye kawai zan je nayi, zanje na samu Kawu Bala in sanar mai yadda ake ciki"

Tashi Hajia Khadija tayi ta 'dakko bowl (kwano) din fruits (kayan marmari) da ke kan dinning table (teburin cin abinci) ta fara yanka lemu

"Allah dai ya shige mana gaba"

Ta furta sannan ta cigaba da hidiman ta

"Mama wai ina Fadeelah ne?"

Maheer ya fa'da yana dube dube

"ta tafi gidan su Hajja Gana, kasan yau ake Wushe Wushe dinta"

Mama ta amsa yayin da ta ajiye wu'kar hannun ta akan bowl (kwano) ta 'dauki remote

"Mata da biki"

Maheer ya fa'da tare da girgiza kai

**MAHEER YUSUF dan asalin garin Fagge ne dake jihar Kano, shine yaro na farko a gurin iyayen shi, matashin saurayi ne me kimanin shekaru 29, ma'aikaci ne a FIRS dake jihar Kaduna, mahaifin shi Alhaji Yusuf Sulaiman ya da'de da rasuwa tin yana da shekara 19 a duniya, yana zaune tare da mahaifiyar sa me Suna Hajia Khadija Ibrahim da 'kanwar shi Fadeelah Yusuf, Suna zaune ne a Yunus Ustaz Usman Road da ke nan Abakpa GRA, masu rufin asiri ne sosai.

_______________________________

"to ke yanzu ya kk gani Hafsa, kin dai ji abunda tace"

Hajarah ce ke kallon Tasneem cike da tausayawa, yayinda Hafsah 'kawar su ke kusa da Tasneem tana lallashin ta

Hafsa ce tace

"to ni dai a shawara na ki cigaba da addua komai yayi zafi maganin shi Allah"

"haka ne kam, Allah ya sa mudace to, Amma abun babu da'di wallahi"

Tasneem ta numfasa tace

"Wai yanzu sati me zuwa zan auri Maheer, wallahi baba be kyauta mun ba, ni tausayin kai na ma nake ji"

Hajara ce tace

"The Most Important thing shine kina son shi, Amma Tasneem anya kinyi Istihara akan Maheer kuwa? A komai fa ya kamata mu nemi zabin ubangiji, so da yawa mutane suna fa'dawa halaka saboda qin neman zabin Allah, Amma dai to.. Allah dai ya sa mudace"

Mi'kewa Tasneem tayi tare da gyara zaman hijabin tace

"Hmmm Ameen, Hajarah bari ki ga in je gida kar Umma taga na zauna da yawa, Hafsa yanzu zaki tafi ne?"

Tashi Hafsah tayi tace

"mu tafi kawai, na ga yamma ta fara yi kuma ni zanyi girkin dare"

"Yanzu tafiya zaku yi dukanku, ba damuwa, ko dayake ai kunyi qoqari ma, se nazo nima, muje na raka ku, Tasneem zanzo mu ga me ya kamata ayi dik da lokacin dai 'kurarre ne "

Hi❤️
The chapter was boring huh?
Sit back and relax, it's just starting

Let me take a minute and thank
Ameenahtou Jay, Tasneem Ahmad, Fadeelah Yusuf, Khadija Ibrahim Aliyu , Aisha Muhammad Auwal , Ummu Salma Zailani, Qudrah Adam , Aisha Marte , Fatima Ustaz ,Zainab Naseer , Hajarah Abdullahi , Hauwa Haliru , Khadija Kaumee , Fatima Ahmad Hassan , Khadija Sulaiman Thank you for all the love and support , voting da comments ya hau kan ku 😂 For those of you that i didn't mention their name, I did not forget you , You are also in my mind .

Dont forget to vote , share and comment, I love you 😘

Dedicated to Chuchujay

Aisha Ameerah❤️

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Where stories live. Discover now