4

596 82 25
                                    

Na kai minti biyar ina 'kara kallon kai na a madubi, wallahi na chanja sosai, sanye nake da lesi me kalan sararin samaniya da ratsin ruwan toka, gwargwaron kai na shima kalan ruwan toka, na saka sarka me kalan ruwan toka yana ta wal'kiya, mi'kewa nayi na 'kare ma kai na kallo sosai daga sama har 'kasa, hannaye na da suka sha lalle ba'ki da ja nake kallo, nayi musu ado da warwaro da zobe me kalan ruwan toka masu wal'kiya, 'dayan hannun kuma agogo ne ruwan toka me duwatsu 'kirar Versace, na kasa 'dauke ido na akan kafa na, da ma Allah ya bani arzikin 'kafa me kyau MashaAllah, to yanzu ko da aka masu lalle ja kuma na sa takalmi me kalan ruwan toka  me duwatsu se suka qara kyau, abun ba'a cewa komai ni kai na nasan nayi kyau to ballantana ma wani in ya kalle ni, Nafeesah ce da ke zaune a bakin gado tace

"Kai Tasneem wallahi ban taba sanin haka kike da kyau ba se yau, kin ganki kuwa kamar wata sarauniya"

Ni kam murmushi kawai nake yi dan na kasa magana ma, Haajarah ce ta amsa da cewa

"Uwar gida kuma Amarya a gidan Maheer Yusuf, Sauraniyar Zuciyar Brave"

Nan na 'kara fa'da'da murmushi na, har yanzu dai ina ta kallon irin halittar da Allah ya mun, Ina cikin haka se ga Umma ta shigo hannun ta 'dauke da mayafi kalan ruwan toka, ita kuma 'yar uwa ta Ameerah dake bayan ta ta ri'ko wata 'karamar jaka  me kalan ruwan toka me kyau

"Wai yanzu yaran nan tin 'dazu kun kasa tashi ku fita ku samu ba'ki, kun zauna se kallon juna kukeyi kamar baku san kanku ba, kun dai san cewa ana idar da sallahn juma'a za'a daura auren nan kuma ana gamawa zaku ga angwayen nan sunzo 'daukar hoto ko"

Umma ce ke fa'da kamar tana fa'da amma a zahiri ba fadar take yi ba

"To Umma yanzu zamu tafi"

Inji cewar Zahrah

Umma bata amsa ta ba ta mi'ka ma Hafsah mayafi na tayi ficewarta, Se a yanzu na 'kare ma 'kawaye na da 'kanne na kallo, 'kawaye na sun sa atamfa kalan ruwan toka me ratsin kalan sararin samaniya , 'kanne na kuma yadi ne kalan shu'di a jikin su, kowa yayi kyau yadda kuka san za'a je gasar sarauniyar kyau, dik sun gama shiryawa, Zee Gidado da Zee Bakori ne suke nan suna 'kara yi ma fuskar su kwaskwarima, so sukeyi se sun fi kowa kyau

'Karar waya ta na ji me 'kirar IPhone X Max, Siyama ta mi'ko min tare da sakawa yadda kowa yaji, muryar masoyi na ce ta doki 'kunne na

"You are officially Mrs Maheer Yusuf, Congratulations Amarya ta, yau dai kin zama mallaki na"

Nan 'dakin ya kaure da gu'da

"Ayyiriri yiriri yiriri !!!!!!"

Kashe wayar yayi ni kuma murmushi nakeyi ido na na 'ko'kari cika da hawaye, su ko se maimaitawa sukeyi

"Alhamdulillah MashaAllah, Officially Mrs Maheer!!!!!!"

Ameerah cewa tayi cikin jinda'di

"Dalla kar ki 'bata fuskar ki da hawaye, yau ranar farin ciki ce"

Fa'din hakan da tayi ne maganar Abba ta fa'do mun a rai, yanzu in Abba be chanja hukuncin shi ba yau Umma zata bar gidan nan, samun wuri nayi na zauna, Haajara ce da ta gane halin da nake ciki ta ce ma sauran 'kawaye mu dik kowa ya fita, yanzu muma zamu fito, 'dakin ya rage daga ni se ita se Hafsah da Ameerah da kuma 'kanne na guda biyu,
Dafa ni Siyama tayi yayin da sauran duk suke kallon mu, ta goge mun kwallar da ke 'ko'karin fita a ido na tace

"Ukhtieey kiyi haquri nasan tinanin da kike yi, Allah yana tare da mu, kuma komai yayi farko ze yi qarshe, wannan jarabawar ubangiji ce, fatan mu Allah ya baki zaman lafia, ya kuma karkato da zuciyar Abba ya gane gaskia"

Kallon Zahrah nayi ita ma, gyada kai tayi alamar maganan Siyama gaskia ce, dik da Zahrah tayi fushi da qin fasa aure na da nayi amma daga baya ta gane cewa wannan abun muqaddari ne, nan tausayin su ya qara kama ni

Kafin in bu'de baki inyi magana Umma ce ta shigo tare da fa'din

"Gaskia nagaji da muku magana, tin 'dazu nake ta safa da marwa a dakin nan, wai dan Allah ba zaku fito bane, ga angwayen can sun qaraso"

Dik se muka fara murmushi dan bama so mu tada ma Umma hankali dik da mace ce jaruma me tawakkali

Zahrah ce tace

" Ohh Ummata tsufa ya kama ki, tin safe kike ta mita"

Daka mata duka Umma tayi tare da fadin

"Qaniyar ki, ni ce tsohuwa"

Duk muka kwashe da dariya, Dan Umma da Zahrah sun iya abun dariya

Miqewa muka yi gaba 'daya da niyyar fita, Hafsa ta yafa mun mayafi na a saman kai, tasa abun kama mayafi ta kama mun gyale ne da gwargwaro na tare, ta iya harkan gayu, ko dayake me make up ce.

________________________________

Ango na na hango sanye da  Shadda me kalan sararin samaniya, yayi kyau kamar a 'dauke shi a gudu, Murmushi kawai yake yi ya qura mun ido yana ta kallo na, nan dai muka qarasa inda suke tsaye, ana ta barkwanci da raha, hotuna ko da akayi har sai da na gaji da ma camera murmushi, mun burge kowa saboda dukan mu ba baya bane wurin kyau duk da dai shi Maheer 'din ya fini haske amma kyau kam se dai ya biyo ni a baya.

Bayan an gama 'daukar hotunan 'dakin Umma na nufa dan sauya kaya yayin da tsofaffin da ke tsakar gidan suke ta zolaya na, a na ta shagalin biki masu cin abinci na ci masu hira nayi, masu gulma ma ba'a barsu a baya ba.

A bakin wardrobe na samu Umma tana ta dube dube, shigowa ta ya tsayar da ita daga abunda take yi, nan ta mun alamar inzo kusa da ita, a bakin gado muka zauna, da fa ni tayi ta fara cewa

"Yau kin shiga sabuwar rayuwa 'ya ta, kiji tsoron Allah, ki sani cewa yau zaki fara sabuwar rayuwa, zaman aure ibada ne, ki sa a ranki aljanna ce zaki je nema kuma ba'a samun aljanna da sauqi, kar ki yi wasa da ibada, Allah ze taimake ki in har kika bi dokokin shi kuma kina ibada, nasan ba kya wasa da sallolin ki da azumi da azkar, ki qara akan wanda kike yi, na yarda da ke ta bangaren gyaran gida da tsafta da iya girki, ki zama me biyayya ga mijin ki, ki maida gidan ki tamkar wata dausayi, kar ki bari mijin ki ya samu abunda ze kushe ta wurin 'dabi'un ki da sauran ayyukan ki na gida, kiyi haquri kuma, wanda ya biki da sharri ki maida mishi da alheri, ki zauna da maqwaftan ki da danjin mijin ki lafia, ki kama Allah shi ne gatan ki, ki zama me riqe sirri, Tasneem Allah ubangiji ya miki albarka"

Kuka kawai nake yi yayin da na rungume Umma, Wallahi Allah ya azurta ni da mahaifiya ta gari me tsoron Allah, Baiwar Allahn nan Allah ne kawai ze saka mata da gidan aljanna, tana cikin damuwa amma ta danne saboda farin ciki na

"Tashi muje ki wanke fuskar ki, ki chanja kaya, kin san dai ba da jimawa ba za'a zo daukar ki gara a gama walimar nan da wuri.
____________________________________
💝💝💝💝💝😘😘😘😘😘😘❤️❤️❤️❤️
This chapter is for you My two sweethearts Shout Out To You Sister Hannatu Haliru Sunusi (Yaya Baybie) I love you so much wallahi, you are very special,and Sister Nafeesa Abubakar writer of Hafsa, Hayrah, the love story of basma, married to the love of my life and many more

Please click the star ⭐️ below, it means a lot to me, share and comment I will also appreciate that.

Dedicated to Chuchujay

Aisha Ameerah Loves you all

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu