5

527 60 9
                                    

Da misalin qarfe 6 dangin Maheer da abokan sa suka zo dauka na, sanye nake da atamfa Ash me zanen Red a jikin ta, riga da skirt ne wanda ya sha 'dinkin stone work, mayafi Red aka rufe mun fuska da shi, nayi kyau sosai dik da banyi make up ba,Ina zaune a bakin gado dik munyi shiru babu wacce ke magana, ko wacce da abunda take saqawa a cikin ranta, Hajia Maryam yayar Abba nake jira ta qara shawo kan Abba domin Abba yace ba ze mun nasiha ba ai bana buqata, zuciya ta zafi take mun inna tuna yadda Abba ya dizga ni a gaban qawaye na bayan an kai ni wurin shi ya mun fa'da, ya bar mun abun magana saboda wasu qawayen nawa basu san me ake ciki ba tsakanin Umma ta da Abba na, Hafsah da Haajarah ne kadai suka sani, sallamar Hajia Maryam ne ya fito dani daga cikin tinanin da nake yi

"Tasneem tashi mu je wurin Abba naki, nayi nasarar shawo kanshi, tashi ki gani kar mu 'bata ma dangin mijin ki lokaci, tin 'dazu suna ta jira"

"Toh" na amsa mata da shi, sannan ta sake cewa

"Hafsah da Hajara ku taso muje ku rakata"

****A zaune muka samu Abba ya tamke fuska, ta cikin mayafi na nake kallon shi, Umma dai ba ta zo wurin ba, tana can ta tsaya ta bayan qofa, zaunawa mukayi gaba 'daya a qasa yayin da na sunkuyar da kai na qasa ina ta saqe saqe a cikin rai na, nasiha Abba ya mun a gurguje kamar wanda aka sa dole, hawaye na tayi ina tuna yau zan bar gidan iyaye na, amma abunda yafi damu na shine dik yadda nake shiri da Abba na ba da son ranshi zanyi auren nan ba, yana gama maganar yace muna zamu iya tafiya, har mun kai bakin qofa ina qoqarin saka takalmi na kenan se Abba yace

"Dakata Tasneem, Hafsah da Haajarah ku jira ta a waje Please, Hajia Maryam kema ki dawo akwai maganar da zamuyi, sannan ki mun magana da Amina"

Gaba na ne ya fa'di, Innalillahi nake ta furtawa a cikin zuciya ta, komawa nayi na zauna, Hajia Maryam ce ta kira Umma, Umma ta shigo ita ma ta zauna, Abba ya fara magana tare da fa'din

"Hajia Maryam kinsan cewa akwai yarjejeniya tsakani na da Amina"

Hajia Maryam qasa tayi da muryar ta tare da fa'din

"Haba Abban Tasneem, meyasa ka ke qoqarin maida qaramin abu babba, tin da an riga an daura auren nan ka haqura mana"

Abba ya qara 'bata fuska tare da fa'din

"Ni bana magana biyu, sanin kanki ne tin da muke yara bana fa'din abu ban aikata shi ba, dan haka Amina kije na sake ki saki 'daya "

Salati Hajia Maryam ta fara, yayin da Umma ta miqe tsaye ta dafe kirjin ta, hawaye suka fara sauka a idon ta, ni ko fashewa nayi da kuka tare da fa'din

"Innalillahi wainnan illaihir rajiun, wayyo Allah na ni Tasneem, na shiga uku ya zanyi da rayuwa na"

Tashi Abba yayi ya fita, riqe Umma nayi ina ta ruzgar kuka yayin da Hajia Maryam ke ta lallashin mu, sake mu Hajia Maryam tayi tare da fita waje, shigowa tayi da Hafsah Da Haajarah sannan ta umarce su da su fitar dani mu tafi, riqe Umma gagam nayi naqi sakin ta, da qarfi Umma ta cire mun hannu na a jikin ta sannan ta nufi 'dakin ta tana kuka.

_______________________________
Ko da muka isa gida na kuka nake ta ke yi, mutane na ta cewa wai kukan da nake yi kaman anyi mun mutuwa ko kuma auren dole, in da nagode ma Allah shine Zahrah ta gaya ma Maheer halin da ake ciki shiyasa yace ma abokan shi babu siyan baki, qarfe 9 Maheer ya shigo gida bayan abokan shi sunyi mishi rakiya zuwa bakin qofa, nan ya tsayar da su da su tsaya su tafi da Hajara da Hafsa, dubu 50 ya miqa masu tare da yi musu godia, Hafsa da Haajarah sun tafi sun barni cikin wani irin yanayi, na sha kuka sosai har na gode ma Allah, hakika na da'de banyi irin wannan kukan ba, ina ta tinanin wani irin hali Zahrah da Siyama da Umma ta suke ciki, bazan taba mantawa da wannan ranar ba, tabbas Abba ya yanke mummunan hukuncin da dole yayi nadama, amma wai abun mamaki shine qara son Maheer ma nayi a maimakon inji haushin shi tinda a sanadiyyar shi mahaifiya ta ta bar gidan Mahaifi na.

Shigowa Maheer yayi tare da yin sallama, wuri ya samu ya zauna a gefe na tare da rungumo ni jikin shi, mun kai kusan minti goma a haka kafin ya juyo dani na kalle shi, nan ya fara da cewa

"Habibtee kiyi haquri kinji, komai ya samu bawa muqaddari ne daga ubangiji, nasan kina da juriya to ki qara akan wanda kike da shi, Inn Sha Allah Umma zata koma gidan Abba, gobe da safe zamu kira ta muji lafiyar ta Inn Sha Allah, yanzu ki tashi muje muyi alwala muyi sallah"

Gya'da kai nayi tare da miqewa

"Yauwa Baby nah ko ke fa, kar ki zama cry cry baby"

Riqe mun hannu yayi muka je ban 'daki muka 'daura alwala ya ja mu sallah, bayan mun idar ne ya juyo ya dafa kai na tare da yi muna addu'an samun zaman lafia

"muje mu ci abinci ko"

Yana murmushi ya 'dago ni na tsaya a kan qafa na sannan ya rungume ni ta gefe muka tafi parlor dan cin abinci, shi ya dinga bani a baki har na qoshi, muna gamawa ya tattara komai ya kai kitchen sannan ya dawo muka tafi 'daki, kayan jiki na na sauya sannan na hau kan gado, kashe wutar 'dakin yayi ya jawo ni jikin shi, nan take bacci yayi awon gaba dani.

Hajia Tasneem Dai Ta Isa Gidan Ta, Se kuzo muje gobe dan cin chin chin da dubulan 'din amarya😁😁😋😋😋Nasan dama abunda Hajja Gana Da Ayush Marte suke ta jira kenan😏😏

Se mun hadu a page na gaba.

Dedicated To Chuchujay

Aisha Ameerah❤️

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Where stories live. Discover now