40

344 59 10
                                    

Sanye nake da lace maroon wanda aka ma 'dinki doguwar riga A-line, lace 'din ya sha adon stone work har qasa, 'dankwali na ka'dai na 'daura na saka sarqa da 'dan kunne golden, mayafi milk na yafa, hannaye na da qafa na sun sha lalle ja da baqi, na zauna a bakin gado kamar wacce babu rai a jikin ta, zazzabin da nake yi ne ya sa ko make up ba'a yi mun ba, Yau ta kasance ranar juma'a, ranar kuma 'daurin aure na a qaro na uku, ranar da zan auri Jabeer a matsayin miji na na uku, tun ranar da mukayi meeting ni da su Fadeelah ban qara jin sauki ba, daurewa kawai nakeyi ina qarfin hali, na buqaci da kar ayi mun taron biki shiyasa daga ni se Qanne na ne se kuma se kuma Fadeelah, qawaye na na kusa dani basu sama daman zuwa ba saboda Hajarah ta kusa haihuwa Hafsah kuma sunyi tafiya da mijin ta, su kuma sauran qawaye na ban gayyaci kowa ba wasu ma ko sanin zan qara aure basuyi ba, Ummi da Ameerah ma sunzo, se wasu ka'dan daga cikin qannen Ummi, Zarah da Fadeelah suka shigo a tare suka ce

"Yana waje, muje ko?"

Kallon su nayi nace

"Ni fa tsoro nake ji, in wani ya ganni ina magana da Maheer fa? Kuma kinsan a qofar gidan nan za'a 'daura aure ko"

Zarah ce tace

"Karki damu ai ta gate 'din baya zamu fita, kuma tare zamu shiga motar yayi miki magana, kinga ai alfarma ya roqa ko?"

Cewa nayi

"Muje To"

Fita mukayi daga 'dakin cikin ikon Allah ko babu wanda ke parlor saboda duk suna gaban gida, fita muka yi muka samu Maheer a cikin mota, har ze fito se Fadeelah tayi mai signal da ya zauna a cikin motar kawai, shigewa sukayi yayin da ni kuma na zauna a gaba, Ina shigowa yayi mun murmushi yace

"Amarya ba kya laifi, kinyi kyau abunki"

Murmushin qarfin hali nayi nace nagode, qiris nake jira hawaye ya zubo a ido na, gaisawa mukayi sannan yace mun

"Nazo taya ki murna ne, Allah ya sanya alheri ya baku zaman lafia ya kawo zuri'a dayyiba"

Kasa amsa mai nayi se su Fadeelah ne suka ce "Ameen"

Nan ya cigaba da cewa

"Allah be nufa zan qara zama mijin ki ba, amma ina roqon Allah in hakan ne mafi alheri kuma shi ze saki farin ciki to Allah ya baki zaman lafia, ga wannan kiyi manaji ba yawa gudunmawa ta ce"

Hannun shi na kalla na ga ya miqo mun envelope, Zarah ce ta taya ni amsa yayin da nace nagode, cewa nayi dashi

"Wallahi Maheer naso..."

Dakatar dani yayi yace

"Karki ce komai, kar ki damu nasan abunda zaki ce, wallahi Tasneem ko da wasa banjin haushin ki ba, amma innace bana jin zafin auren da zakiyi ba to nayi qarya, ina sonki kuma bazan daina sonki ba har iya qarshen rayuwa ta"

An ta'ba mun inda yake mun qaiqayi kawai se na fashe da kuka, hankalin su duka ya tashi, nan sukayi ta bani haquri, bayan na dan tsagaita kukan se Maheer yace musu su shiga dani cikin gida, cewa nayi da shi

"Maheer kai ma ka daure kayi aure dan Allah, Kuma ka sani ni masoyiyar ka ce ta har abada "

Murmushi yayi yace

"Karki damu kinji, ki daina kuka dan Allah, Ina miki fatan alheri"

Ban tsaya amsa mai ba na bu'de motar na fice ina kuka, su Zahrah suma suka biyo baya na, ina shiga cikin gida na nufi 'daki, su Zahrah na shigowa ita ma Siyamah ta biyo bayan su, Fadeelah ta rufe qofar 'dakin da key, haquri suka dinga bani, sannan suka ce in kwanta in huta.

Baccin awa 1 na samu, ina tashi na ga duk basa cikin 'dakin, toilet na shiga na wanke fuska ta, ina dawowa se na lura da wani paper, 'dauka nayi na ga wasiqa sukayi mun na in na tashi in kirasu a waya suzo su bu'de qofar, kiran su nayi a waya, basu 'dauki lokaci ba se gasu sun shigo dukan su ciki har da Noorie, da yake zazzabi yana damun ta shiyasa bata hayaniya sosai, haquri su Siyamah su ka yi ta bani suna mun nasiha.

____________________________
Qarfe 8 na dare Abba yace mu fito ze kai ni gidan miji na, na buqaci da Abba ya kaini da kanshi, Jabeer ma ya yarda da hakan yace ba se 'yan uwa shi sunzo 'dauka na ba, Siyamah, Zahrah da Fadeelah ne ka'dai zasu rakani, sallama mukayi da su Umma, ban tafi da Noorie ba saboda Umma tace se bayan sati biyu za'a kawo mun ita.

Muna isa gidan Jabeer su Zahrah suka raka ni ciki, gidan beyi kama da wanda akayi biki ba, saboda shiru gidan yake kamar babu mutane, qwanqwasa qofa su Zahrah suka yi, se da aka 'dan 'dauki lokaci sannan aka zo aka bu'de qofar, wata dattijuwar mata ce tazo ta bu'de qofar amma dai daga alamu ba Mahaifiyar Jabeer bace saboda wannan bata isa haifan shi ba, sannu ta yi muna sannan ta tarbe mu da fara'ar ta, iso tayi muna zuwa cikin gidan, ni dai fuska ta a lullube take amma ina kallon komai ta cikin gyale na, zama nayi a qasan carpet su kuma su Zahrah su ka zauna a kan kujera, wata yarinya ce wadda nake tunanin ita ce Jiddah na ga ta kwanta ta cukurku'de a kan kujera tana bacci kamar wata mara galihu, shiru muna zaune amma babu wanda ya zo wurin mu, Abba tuni ya fara kiransu Zahrah a waya akan su zo su tafi, muna nan zaune shiru babu me cewa komai se can mukaji taku daga matakala, taku akeyi 'daya 'daya cikin qasaita, muryar me tafiyar ce ta doki kunne na yayin da tace

"Ku kuma fa?"

A zuciya ta nace "ba'a ma san su waye mu ba kenan" gaida ta su Zahrah sukayi, amsa su tayi ciki ciki kamar ba zata yi magana ba, Zahrah ce tayi qarfin hali tace

"Mun kawo amarya ne"

Matar ce ta sake cewa

"Wace amaryar?"

Fadeelah tace

"Amaryar Jabeer"

Dariyar rainin wayau matar tayi sannan tace

"Ai ni a sani na wadda Jabeer ya aura bazawara ce, To me ne ne wani abun amarya a ciki"

Duk jikin mu yayi sanyi, babu wanda ya iya amsa maganar, can dai se ta sake cewa

"Mungode to, tare zaku kwana da ita ne?"

Cewa sukayi da ita yanzu zasu tafi, zama tayi a kujera tace musu

"Toh sai da safen ku"

Nan dai da suka ga babu sarki se Allah se suka miqe, sallama sukayi mun sannan suka tafi, gaba na se fa'duwa yakeyi dan na rasa wacece wannan, maganar ta ne ya fito dani daga tunanin da nakeyi

To wa ce ce wannan kuma? Zamu gani a Page na gaba, Tasneem dai ta sake aure a qaro na uku, wannan shine qaddarar ta, Allah dai ya bata zaman lafia.

Banda ni wa ya tausaya ma Maheer da Tasneem?

Kuna so ku ga wacece wannan matar kuma me ze faru a Page na gaba? To ku cigaba da bi na

Don't forget to vote, share and comment

Dedicated To Chuchujay

Miss Sparker loves you all❤️❤️

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Where stories live. Discover now