1

2.8K 146 26
                                    

"Wallahi Amina in dai har Tasneem ta auri yaron nan to a bakin auren ki" Abba ya fa'da cikin fushi

"Kana nufin auren Tasneem Da Maheer shi ze kawo rabuwa ta da kai?"

Takowa Umma tayi  zuwa gaban Abba cikin bacin rai take maganar

" Tabbas! Na yarda Tasneem ta auri Maheer amma abunda zan tabbatar miki da shi shine tana sa 'kafa ta bar gidan nan ke kuma zaki sa 'kafa ki tafi gidan iyayen ki, tinda har ni ubanta zan bata yaron aboki na ta aura ke kuma ki watsa mun 'kasa a ido, kin zauna kin hure mata kunne"

"Amma dai na ga ..... " umma ta bu'de baki zata yi magana Abba yayi saurin dakatar da ita da fa'din

"Dakata!!! Ki saurara mun Amina, In har kin yarda da wannan hukuncin nawa da na yanke ranar jumma'a me zuwa 'yar ki zata gidan mijin ta" se a yanzu na 'dago kai na,  da kuka a ido na na ke fa'din

"Dan Allah Umma da Abba ku daina maganar nan, In dai dan ni ce a ke maganar nan to wallahi na hakura, Dan Allah Abba kayi haquri kar ka saka ummata"

Umma ce tayi saurin katse ni da fa'din

"Ki yi shiru wannan ba maganar ki bace Tasneem, ki tashi ki wuce dakin ki, kuma ki ja 'kannen ki "

Sannan ta juyo ta kalla gefen da 'kanne na suke ta ce masu

" Zahrah da Siyamah ku bi yayar ku 'dakinta zanzo in same ku"

Da gudu na shige 'daki na na fa'da akan gado tare da 'kara sautin kuka na, zuciya ta zafi take mun, wallahi har cikin zuciyata bana so Abba na ya rabu da mahaifiya ta amma ina 'kaunar Maheer bazan iya rabuwa da shi ba, Siyamah ce ta dafa ni bayan sun shigo ita da Zahrah tana fa'din

" Ukhtieey, Dan Allah karki bari iyayen mu su rabu saboda ke, kar ki bari soyyayyar Yaya Maheer ta ru'de ki har tayi sanadiyyar rabewar iyayen mu"

Tashi nayi daga kan gado na mi'ke ina kallon ta cikin tausayawa ita da Zahrah nace

"Siyamah, wallahi ina son Maheer, samun namiji irin shi a duniya ze yi wuya, Dan Allah 'kanne na kar ku yi fushi da ni, ni ma bana son rabuwar iyayen mu amma ina matukar son Maheer har cikin rai... "

Kafin in qarasa Zahrah tayi saurin katse ni da cewa

"Haba Ukhtieey, wannan wani irin magana ne, ai wannan ba magana bane, yanzu kina nufin kin fi son rabuwar iyayen mu saboda son zuciya irin naki, a gaskia ki chanja tinani, har yanzu kina da damar da zaki cewa Abba kin fasa auren nan"

Tana fa'din haka tana watso mun harara

Kafin in bude baki in amsa mata Umma ta shigo dakin tare da fa'din

"Wannan auren kamar anyi shi ne an gama, dan kuwa bazan taba yarda Tasneem ta auri wanda bata so ba, kuyi ha'kuri yara na Allah yana tare daku kunji, kuyi ta Addu' a Allah ze kawo muku 'dauki, kar ku sa abun nan a ran ku, In dai har baban ku ya dage akan hukuncin da ya yanke to ba makawa auren mu yazo 'karshe"

Umma tana fa'din haka na sake fashewa da kuka na tashi na je na rungume ta, Ina kuka tana bani ha'kuri, jawo ni jikin ta tayi tare da janyo Zahrah da Siyamah ta rungume mu muna ta kuka tana lallashin mu .

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah,
This is my first book on Wattpad, I hope you'll like it, please come closer and take your chocolates and kisses 😘, I hope we will get along, give a chance to this book and I promise you won't regret it, it's gonna be written in Hausa, yes Hausa cuz it's my first language, pardon my errors please, you might encounter some mistakes, I am not perfect but I will try my possible best to write something nice for you all, It's not your regular love story, it comes with a lot of twist, Follow me on this ride and let's see where it ends .

I love you all❤️❤️❤️❤️

Dedicated to Chuchujay

Aisha Ameerah❤️

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Where stories live. Discover now