30

382 50 18
                                    

"Me ya faru da kai darling, wayyo Allah na Umma me ya faru da miji na?"

Kuka nake yi kaman rai na ze fita, Adeel ne kwance a kan gadon asibiti ana qara mishi jini, qafan shi kuma an na'de mishi shi da bandage, kallo na kawai yake yi amma be ce mun komai ba, Abba na juyo na riqe gam ina cewa

"Abba me ya faru da shi, dan Allah ku ce yayi mun magana"

Shima Abba shiru yayi be ce komai ba, Umma ya kalla ya ce

"Amina ki fitar da Tasneem ki kai ta ta zauna ta huta, ki bata ruwa ta sha Please "

"Toh" ta ce mishi sannan ta jani ta ce mun inzo mu je, kuka me cin rai na fara yi murya na ko fita bata yi, ce mata nayi

"Ni dai Umma ki barni anan dan Allah, ki barni a wurin miji na, ki ce mishi ya mun magana dan Allah, bana son ganin shi a haka, zuciya na tana mun zafi, Umma ki sake ni dan Allah, Allah ka duba ni, Adeel ni ka'dai yake da ku qyale ni dan Allah"

Hawaye ke ta zuba a fuskar Umma amma har yanzu tana ja na, Noor ka'dai nake kallo ina kuka, ya qi ce mun komai amma, da Abba ya ga na qi yarda se yace Umma ta sake ni, matsowa yayi kusa dani yace

"Ambaby kiyi haquri ki je waje ki sha iska kinji, mijin ki ze samu lafiya da yardar Allah, kin ga ma yana ta kallon ki so kike yi hankalin shi ya tashi shima"

Abba na kalla sannan na qara maida kallo na kan Adeel, hawaye na ga yana fita a idon shi, hannu na da Abba ya riqe na kwace sannan na tafi wurin Adeel, hawayen da ke fuskar shi na goge sannan na riqe fuskar shi ina kallon shi, cewa nayi da shi

"Ka tashi mu tafi gida Noor, bana son ganin ka anan wallahi, me ya same ka? Ba Abuja kaje ba? To me ka ke yi a asibiti kuma?"

Hannun shi ya 'daura akan hannu na da yake fuskar shi, kallo na kawai yake yi amma ya kasa cewa komai.

Su Umma sun da'de suna bani baki akan inyi haquri muje waje in sha iska, kuma in kalli yanayin da nake ciki nima, da kyar na bi Umma waje muka zauna a wurin massallaci, kukan da nake yi ya tsaya amma har yanzu hankali na a tashe yake, cewa nayi

"Umma me ya samu Adeel?"

Dafani tayi tace

"Hatsari sukayi da wata mota, wanda suke tare da shi ya rasu, shi kuma ya bugu ne shiyasa aka kawo shi asibiti, Abban ki yayi waya da shi kafin yayi hatsari bayan sun gama waya da kamar minti 10 se aka kira Abban ki aka sanar mai da hatsarin, kiyi haquri kinji ze samu lafiya da izinin Allah"

Kuka na fara yi na riqe hannun Umma nace

"Umma naji a jiki na, wallahi naji a jiki na wani abu ze same shi, Umma yanzu in Noor ya tafi ya barni ya zanyi? Maheer ya guje ni shi kuma Noor na so ya barni, ya zanyi Umma ya zanyi"

Hawaye Umma ta goge tace

"Kiyi haquri kinji, Inn Sha Allah ba ze tafi ya barki ba, zaku kasance tare, zaku raini abunda zaku haifa tare, ki daure ki daina kuka, ke musulma ce ina so ki yarda da qaddarar da ta same ki, ki tashi ga ruwa can a butan can kiyi alwala kiyi Sallah ki roqa ma mijin ki samun lafiya, kinji Tasneem 'dita?"

"Toh" nace mata, da sauri na tashi nayi alwala sannan na kabarta Sallah, na 'dago kenan da ga sujjadan farko se na ji muryar Abba yazo wurin Umma, da kyar na iddar da Sallah naga suna magana shi da Umma, Umma ce ta ce mun

"Kin idar ko? Taso muje mijin ki yana son ganin ki"

Da sauri na miqe na bi bayan su, cikin da ke jiki na ya mun nauyi amma a haka nake ta 'daurewa ina binsu a baya, muna kaiwa cikin 'dakin se na ga wata Nurse a gaban shi, hannu Adeel ya miqo mun yana mun alamun inzo wurin shi, da sauri na isa wurin shi na riqe hannun shi, magana yake mun amma bana jin abunda yake cewa, hankali na ya tashi sosai se nace ma Umma

"Umma bana jin abunda yake cewa"

Fashewa nayi da kuka, Abba ne yazo kusa da shi, sake mai hannu nayi ina kallon shi shi da Abba, Abba ke fa'da mai abu a kunne shi kuma yana ma Abba magana shima a kunne, bana jin me suke cewa se na ga Abba ya 'dago ya ce

"Allah ubangiji ya sa ka tafi a sa'a Adeel, hakika kai mutumin kirki ne, Allah ya sada ka da mala'ikun rahama"

Hankali na qara tashi yayi se nace

"Abba lafiya, ya gaya maka? Kaji abunda yake fa'da?"

Abba ce mun yayi

"Cewa yayi ku fita waje ke da Umman ki, ze aika a kira ki"

"Toh" nace sannan Umma ta ja ni muka fita, kuka Umma take yi yanzu sosai, se nace mata

"Umma kenan, ai Adeel be mutu ba, na ga alaman haka kuke so ku ce mun ke da Abba, na san ba ze tafi ya barni ba, ba ze taba tafiya ya barni ba"

Rungume ni Umma tayi sannan tace

"Se dai muyi haquri Tasneem, Adeel ya riga mu gidan gaskia"

Murmushi nayi hawaye yana zuba a ido na nace mata

"Adeel be rasu ba Umma, cewa yayi mu je mu sha iska a waje"

Kuka Umma ke ta yi, sake ta nayi na shige 'dakin da Adeel yake da sauri, bi na tayi ita ma da sauri, ina shiga 'dakin na ga an rufe mishi fuska, likitocin asibitin sun tsaya sunyi cirko cirko ba me cewa komai a cikin su, Abba ko se waya yake yi, Adeel na je na rungume da sauri, kuka na fara yi ina

"Ya zaka mun haka, Noor alqawari be ce haka ba, dan Allah Ka tashi"

Jijjiga shi kawai nake yi, Umma ce ta shigo 'dakin ta ja ni da kyar suka banbare ni a jikin shi, muna kaiwa bakin qofa da su na yanka wani irin ihu na durqushe a qasa, hankalin su ya qara tashi, kafin ka ce me da gudu aka wuce da ni Labour room.

😭😭😭😭Kuyi Haquri Readers, Masoyin mu Adeel ya tafi ya barmu da kewa, yau ina cikin jimamin mutuwar Noor, Allah ya ji qan Adeel ya ba Tasneem haqurin rashin shi, Allah ya sauke ta lafia kuma, Hakika munyi rashi😭😭😭😭😭😭😭

Dedicated To Chuchujay

Aisha Ameerah❤️❤️

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Where stories live. Discover now