11

435 59 33
                                    

Saurin kashe wayan da take yi tayi, ni ko ina ganin haka se nayi saurin fuskewa tare da fa'din

"Ameerori kina jin da'din ki fa wallahi, ji yadda kika haye gado kina ta waya abunki"

Murmushin yaqe tayi sannan tace

"Hajiya Tasneem saukar yaushe?"

Mamaki nayi sannan nace a cikin zuciya na

"Lallai dan adam akwai iya yaudara" sannan nace mata

"Laaa wai dama baki ji murya na ba, ai tin 'dazu ina wurin Ummi a parlor muna hira, kin ga bari nayi sallah akwai maganar da zamuyi, bari na shiga bayi nayi alwala"

Aje jaka na nayi na cire rolling 'din gyalen da nayi na shige bayi, dik da ina da qyanqyami amma a haka na daure na shige bayin dan Ameerah ta iya kazanta, ga son kwalliya ga rashin tsaftan muhalli, ita matsalan ta kawai ta gyara jikin ta, Ina shiga bayin na rufe qofa na jingina da qofar bayin na yi ajiyan zuciya, hawaye ne masu zafi suka fara bin fuska na, se da na sha kuka na sosai sannan na dauro alwala na fito, Ina fitowa na 'dauki gyale na na yafa sannan na 'dauki sallayan dake kan bed side drawer na shimfida, ko da na fito dama Ameerahn bata cikin dakin shiyasa ban ma damu da tambayan ta hijab ba, kabbarta sallah nayi, bayan na idar da sallah nayi addua sosai na gaya ma Allah dikdan damuwa ta, har na idar Ameerah bata dawo cikin 'dakin ba, wayar ta na gani a kusa da pillow tana ringing, da sauri naga ta shigo 'dakin ta 'dauki wayar, saurin amsawa tayi tare da fa'din

"Hello, I will call you back", juyowa tayi tace mun

"Wai Indomie nake dafa mana Tasneem, na ma gama, bari in 'dakko muci"

Amsa mata nayi da "Toh", nan na tashi na linke sallayan na kuma cire gyalen jiki na, waya ta na 'dauko na duba WhatsApp 'dina, Ina cikin replying messages Ameerah ta shigo 'dauke da tray 'din indomie, ajewa tayi a gaba na tace mun "bismillah", In dai girki ne dama Ameerah ba baya bace, ta iya girki sosai dan a wurin ta na ke ansan cookery book ina ganin recipes 'din ta na abinci.

** Bayan mun gama cin abincin ne na zauna kusa da ita lokacin ta yi nisa a danna waya nace mata

"Ameerori magana zamuyi please "

Aje wayan tayi ta kalle ni tare da cewa

"To ina jin ki"

Numfasawa nayi sannan nace mata

"Dan Allah Ameerah so nake yi ki auri Maheer"

Miqewa tayi da sauri ta tashi tsaye tare da fa'din

"Tasneem kin ko san abunda kike fa'da kuwa?"

Kallon mamaki na bita da shi, a zuciya ta nace

"Lallai Ameerah, se kace ba abunda take so kenan ba", sannan na miqe na dafa ta nace mata

"Kiyi haquri ki rufa mun asiri ki auri miji na dan Allah, mun riga munyi magana da shi, Umma tasani, Ummi ma haka, sannan haka zalika Mamar shi ita ma tasani, dama ke ce nace kema kina da hakki in zo in nemi alfarma a wurin ki tinda ke ce zaki zauna, Inn Sha Allah bazaki samu matsala dani ba"

Zaunawa tayi a kan gado nima na bita na zauna, can dai ta budi baki tace

"Toh shikenan, amma ki bari inyi tinani tukunna dan Allah, anjima da daddare zan kira ki in fa'da miki reply 'dina Inn Sha Allah"

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Where stories live. Discover now