25

384 46 11
                                    

"Saaaheeb! Saaheeb!, Lallai yaron nan, da na kira sunan shi se ya fara dariya"

Wasa nake yi ma Saheeb yayin da yake ta dariya, Fadeelah na yanka alaiyahu, cewa tayi

"Ai akwai wayau Tabarakallah"

"Gashi ya koma sak baban shi"

Dariya tayi tace

"Haka dai kowa yake cewa, nima dai zanyi zuciya in haifi me kama dani"

Dariya nayi nace

"Hehehe gaskia ne, ya kamata kam kin ga se mu daina miki gori"

Wanke Alaiyahun tayi ta zuba a cikin shinkafan da take dafawa, cewa nayi da ita

"Ki yanka albasa mana se ki zuba, se ya tirara da shi kinsan albasa na qara qamshin abinci"

Cewa tayi

"Ai kuwa, To bari na yanka amma ni matsala na da albasa se ya sa idon ka yayi ta ruwa"

Dariya nayi nace

"Lallai sannun ki, To ke ba mace bace? Kin san yadda zakiyi?"

Se tace

"A'a"

Ce mata nayi

"Ki sa ka albasan a cikin ruwan 'dumi kafin ki yanka, in kika yi haka ba zaki ji yajin ba"

Yadda nace mata tayi haka tayi se da ta gama yanka albasan sannan tace

"Ai kuwa gashi banji yajin ba wallahi, ai ko nagode wallahi, da'di na da ke kin san Kitchen tips sosai"

Dariya nayi mata sannan na tashi tare da Saheeb a hannu na na ce mata

"Bari muje parlor mu jira ki tinda kin gama ma"

"Toh" tace mun sannan muka wuce, bata jima ba se gata ta fito daga Kitchen 'din 'dauke da warmer 'din abinci a hannun ta, ajewa tayi akan dinning table sannan ta yi arranging wurin, cewa tayi in zo muci abinci, Saheeb da tuni yayi bacci na aje akan Mat 'din shi na wasa sannan na je mu ci abinci, jellof rice ta dafa na mangya'da wanda yaji busasshen kifi da dankalin turawa da alaiyahu, abincin yayi da'di sosai ga kuma orange drink 'din da tayi me sanyi da muka ha'da shi muka ci abincin, bayan mun gama cin abincin taje ta 'dauraye kwanon ta dawo ta same ni a parlor, zama tayi sannan tace

"Wai ni kam Ukhtieey Neem ya kuke ciki ne ke da yaya Maheer"

Cewa nayi da ita

"Kamar ya fa?"

Qara cewa tayi

"Ki yi haquri ki koma mana"

Dariya nayi sannan nace mata

"Ai ni ba daga wuri na bane, a shirye nake da komawa 'daki na kawai dai shine yace baya da ra'ayin maida ni har Abba yaji haushi yace ko da yace ze maida ni shi ba zai yarda ba"

Da mamaki tace mun

"Ni na rasa me ke damun Yaya wallahi, dik Ameerahn nan ta bi ta hargitsa shi"

"A'a Fadeelah kar ki ga laifin ta, ko ma me ne ne shi yaso ai"

Ta'be baki tayi tace

"Haka ne kuma wallahi, Allah ya sa mudace, Allah ya baki wanda ya fishi "

"Ameen" nace mata, Dr Adeel ne ya fa'do mun a rai se na tuna cewa na ce mishi zan kirashi, 'daukar waya ta nayi na kira shi, bugu 'daya ya 'dauka, kafin inyi magana se naji yace

"Assalamu Alaikum Habibtee, da fatar kina lafia"

"Waalaikummusalam, Lafia lau nake , Ina wuni"

"lafiya lau wallahi, ya kike?"

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora