37

326 50 19
                                    

Yau ta kasance Asabar, na tashi da wuri saboda zan kai Noorie asibiti kasancewar ciwon pneumonia 'din ta ya shi, Sauri Sauri kawai nake yi, bayan na gama kintsawa ita ma na shirya ta na 'dauki hijab 'dina na saka sannan na 'dauki jaka na da makullin mota na, 'daukar Noorie nayi sannan na zura takalmi na na fice daga cikin 'dakin, 'dakin Umma na nufa ina shiga tace mun

"Yauwa kun fito ko? Ke ka'dai zaki kai ta?"

Cewa nayi

"Eh Umma, Ina so in biya gidan Fadeelah in na fito daga asibitin akan wannan maganar da na fa'da miki"

Cewa tayi

"Toh shikenan, amma ki kiyaye kin san in Abban ki yaji maganar nan ran mu se ya 'baci, zan dai barki kije ne kawai saboda kina so kiji abunda Maheer ze fa'da miki, bayan nan bana son jin wani abun dan Allah"

Ce mata nayi

"Toh Umma Inn Sha Allah, Nagode Sosai "

"Ba damuwa, ku hanzarta kuje asibitin Allah ya qara sauqi"

"Ameen" nace sannan na fice.

A cikin minti 5 har na kawo asibitin tunda asibitin ba nisa da gidan mu, ina shiga wata nurse ta anshe ta a hannu na, yawanci duk ma'aikatan asibitin sun san mu sanadiyyar Adeel, file 'din Noorie aka 'dauko sannan na jira wani mara lafiyan ya fito daga office 'din Doctor sannan na shiga, duba ta likitan yayi sannan ya bata magani ya kuma qara bada wasu sharu'da, maganin na amsa sannan na kai ta akayi mata allura se muka wuce.

A seat 'din baya na aje ta, tea 'din ta na miqa mata ta sha, da yake Allah ya sa ma yarinyar na da juriya shiyasa da wuya ka ga ciwo ya ci ta sosai, ta biyo dauriyan baban ta sosai, dama can babu abunda ta bari na shi, tayi kama da larabawa sosai, fara ce tas ga gashi, ga ta da tsawon qafa, bata cikin yara sirara, za'a sa ka ta a cikin lissafin Chubby kids, dik da nima fara ce kuma ina da gashi sannan nima kyakkyawa ce amma mutane suna cewa kamar ba ni na haife ta ba.

Gidan Fadeelah na nufa, ina isowa na ha'du da Saheeb a cikin parlor yana kallo, da gudu yazo ya rungume ni ya ce

"Oyoyo Mami"

Ce mishi nayi

"Saheebi nah, ya ka ke, ina Mummy?"

Cewa yayi tana cikin 'daki, zama nayi a kujera ita ma Noorie ta zauna ina ta labari da su ita da Saheeb, Fadeelah ce ta fito tana cewa

"Naga Haske, Oyoyo Haske!!!"

Da gudu Noorie taje ta rungume ta, 'daukar ta tayi sama, wasa ta dinga mata ita kuma tana dariya, cewa nayi

"Haske ka'dai ki ka gani kenan, ni baki ganni ba ko? Ko dai ma me ne ne ai ni na haifi hasken"

Dariya muka yi gaba 'daya yayin da ta aje Noorie, tana aje ta Noorie ta je ta zauna kusa da Saheeb ta fara kallo saboda ta ga cartoon, gaisawa muka yi da Fadeelah sosai, sannan muka yi hira, a cikin hirar ne tace mun

"kin fa'da ma Ya Maheer 'din kin qaraso?"

Cewa nayi

"Au ai ni na manta ma, Ina Umar 'din yake shi?"

Cewa tayi

"Bari in kirasu"

Kiran Umar tayi ta shaida mai na iso, nan yace mata zasu zo suma zuwa bayan azahar, tana gama wayar tace mu je Kitchen ta 'daura abinci tinda ba yanzu zasu zo ba, a parlor muka bar su Noorie sannan muka wuce Kitchen

Aiki muke tayi muna hirar mu, Fadeelah tace

"Magani ka'dai ki ka amsan ma Bibinuyi?"

"Sunyi mata allura ai"

"Allah Sarki Allah ya qara lafia, kin san yanzu ana sanyi se kin qara kula sosai dik da nasan kina qoqari"

"Eh hakane kam, se a hankali ai"

"Wai Ina Ameerah ne, naji ance tana gidan ku ko?"

"Tana nan lafia wallahi, anjima ma naji Abba na cewa in Ummi tazo ze sasanta su se Ameerah ta koma gida"

Cewa tayi

"Allah Sarki, wallahi banji da'din abunda ya faru ba, Salma ce ke zuga ta wallahi, yadda bata yi aure ba bata so ita ma Ameerah ta zauna a gidan mijin ta"

Cewa nayi

"Ai Allah dai ya shirya Salma wallahi, na ga ma har yau bata zo gurin Ameerahn ba"

Hira mukayi ta yi har muka kammala girkin, cin abincin mukayi tare da yaran mu sannan muka je mukayi Sallah, muna zaune a parlor se ga Umar ya shigo da sallamar shi, gaisawa mukayi nan yake tambaya na ina Noorie, ce mishi nayi tayi bacci tana 'dakin Fadeelah, Saheeb ma yana 'dakin shi yayi bacci, dama ita Fadeelah qa'idan ta ne bayan sallar azahar se yaro yayi bacci in dai yana gida, 'daki Umar ya shiga, bayan ya fito se yace mun Maheer ze shigo yanzu, yana fita se ya shigo shi da Maheer 'din, zama mukayi gaba dayan mu da ni da Fadeelah da Maheer 'din da Umar, Maheer ne ya fara magana bayan mun gaisa

"Tasneem abunda ya sa na ce mu ha'du anan ba dan komai bane se dan in baki haquri a bisa irin rashin kyautawar da nayi miki, haqiqa na sani cewa na wulaqanta ki sosai, kiyi haquri ki yafe mun"

Cewa nayi da shi

"Ai ni na da'de da yafe maka saboda bana riqe mutum a zuciya, Allah ya yafe muna gaba ki 'daya"

"Ameen" duka suka ce sannan ya cigaba da cewa

"Amma Tasneem ina so in shaida miki cewa ina da dalilin yin hakan"

Kallon shi nayi nace

"Dalilin wulaqanta ni?"

Cewa yayi

"Qwarai kuwa, ina da dalili me qarfi sosai, amma bana so in fa'da miki na fi so Fadeelah ta fa'da miki saboda nasan kin yarda da ita, kuma kinfi yarda da ita yanzu a kai na"

Fadeelah na kalla nace mata

"To Fadeey ina jiki"

Se mun hadu a Page na gaba, ku kula da kanku kar ku manta ina son ku sosai.

Dedicated To Chuchujay

Aisha Ameerah ❤️❤️

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Where stories live. Discover now