41

303 54 5
                                    



"To ki bu'de fuskar mana in ga akan me ne ne yaro na ya dage se ke"

Zuciya ta dukan uku uku take yi, wai dama mamar shi ce? Addu'o'i na dinga yi a cikin zuciyata, bu'de fuskar nayi na sunkuyar da kai na, kallo na ta dinga yi sannan se tace kuma

"Ya ma sunanki?"

Kallon ta nayi nace

"Suna na Tasneem"

Ta'be baki tayi tace

"Tasneem, Ba laifi kina da kyau kuma muryar ki tana da da'di"

Sannan ta cigaba da cewa

"Ni ce Mahaifiyar Jabeer, Suna na Hajia Afiya, waccan kuma da take kwance sunan ta Hauwa Jiddah yarinyar shi ce"

Gya'da kai nayi alamun na gane, sannan ta cigaba da cewa

"Jabeer shi ka'dai na haifa, kuma ina mutuwar son 'dana saboda duk duniya bani da kamar shi, zan gindaya maki sharu'da wa'danda in kika qetare su zan samu matsala da ke, Kina ji ko?"

"Eh Mama"

Cewa tayi

"Ba Mama zaki kirani ba, ki kirani da yadda yaro na ke kira na, Suna na na Maa"

Cewa nayi

"To Maa"

Cigaba da cewa tayi

"Zuwa gobe da safe zan fa'da miki sharu'da na saboda yanzu kika zo"

"Toh Nagode Maa"

Qwala ma wadda naji ta kira da suna Asabe kira tayi, da sauri matar ta zo ta duqa a gabanta tace

"Gani ranki shi da'de"

"Ki nuna ma Tasneem 'dakin ta, ita ce Matar da Jabeer ya aura, wannan bazawarar da na fa'da miki yana nema"

Asabe tace

"Toh ranki shi da'de, amma wani 'dakin da ga cikin 'dakunan za'a kai ta?"

"Ki nemi 'daki me girma ki sa ta kafin in duba sauran 'dakunan in da yiyuwar in chanja mata zan gaya miki"

"To ranki shi da'de"

Sannan tace mun

"Amarya muje ko?"

Miqewa nayi na bita a baya, Maa tace mun

"Tasneem"

Juyowa nayi nace

"Naam Mama"

Gyara mun tayi tace

"Maa"

"Naam Maa"

Sannan tace

"Bana son latti, ki tabbatar kin tashi da wuri"

"Toh Maa, Nagode se da safe" nace mata

Bata amsa mun ba se kawai na bi Asabe a baya, sama muka hau ina ta kallon gidan, dik kyaun gidan mu be kawo qafan wannan a kyau ba, shiyasa Jabeer yace ba se anyi mun kayan 'daki ba, wannan gidan shi ake kira da aljannar duniya, wani 'daki Asabe ta bu'de me kyaun gaske, komai na cikin 'dakin Brownish purple ne, fentin 'dakin ne kadai fari, juyowa Asabe tayi tace mun

"Amarya ga 'dakin ki nan"

Maganar ta ne ya fito dani daga mafarkin tsayen da nake yi, cewa nayi

"Toh Nagode Mama "

Murmushi tayi mun tace

"Ba komai amarya, Allah ya baku zaman lafia "

Har zata wuce se tace mun

"Amarya kiyi qoqarin tashi da wuri kamar yadda ranki shi da'de ta buqata, kar ki samu matsala da ita"

"Toh Nagode Mama "

Cewa tayi

"Sai da safe" Sannan ta fice, mayafi na na cire, wata qofa nagani se nayi tunanin bayi ne, ashe ko bayin ne, shiga nayi cikin dan yin uzuri na sannan na fito, a gefen gado na zauna, waya ta na 'dauka na kira Zahrah, 'dauka tayi sannan muka fara magana

"Hello Zahrah"

"Naam Ukhtieey ya ki ke?"

"Lafia lau Zahrah ya kuka kai gida?"

"Lafia lau Alhamdulillah amma fa muna ta fargaba "

"Fargaban me kuma?"

"Wannan matar mana, wai wa ce ce?"

"Kinji ki dai, Maman Jabeer ce fa"

"Kai haba dai?"

"Wallahi"

"Chab'di jam, I'm sorry to say amma gaskia daga gani bata da kirki"

"Hmm Zarah kenan, kinsan kowa da halin shi ze zauna ai, kuma da kyakkyawa ake gyara mummuna"

"Ukhtieey kenan, nasan zaki iya zama da ita da duk kowani irin hali, amma dai ki rage sanyi wallahi"

"Ba damuwa kar ki damu"

"Angon be shigo bane"

"Eh tukunna, kun tafi gida ne?"

"Aa se gobe Fadeelah dai ta tafi?"

"Ina su Ayaan, Aryan da Noorie"

"Suna wurin Abba, ni ka'dai ce a 'dakin Siyamah tayi bacci a 'dakin Umma, kinsan me qaramin ciki"

"Haka ne kam, ki gaida su"

"Zasuji se da safe"

Bayan mun gama wayar se na rasa me zanyi, knocking naji a qofa, kafin in miqe se ga Jabeer ya shigo da sallamar shi, gyara mayafi na nayi sannan na gaida shi cewa yayi

"Shiru ke ka'dai ko"

Murmushi kawai nayi mai ban amsa shi ba se ya sake cewa

"Bismillah muje 'daki na"

Gaba yayi ni kuma na bishi a baya, 'dakin shi muka shiga nan ya umurce ni da inyi alwala, bayan mun gabatar da Sallah munyi duk abunda ya dace se yace mun

"Kina jin bacci ko?"

Cewa nayi

"Eh ba laifi"

Cewa yayi

"Ki dauko kayan da zaki chanja se ki zo mu kwanta"

'Daki na na tafi na 'dauko kaya na chanja sannan na tafi 'dakin shi na same shi, kwanciya mukayi sannan ya kashe wuta, can cikin dare naji yana laluba na, shiru nayi ban ce mai komai ba, da na ga yana qoqarin saka hannun shi a cikin riga na se na riqe hannun shi, a kunne ya rada mun

"Lafia kuwa?"

Ban ce mai komai ba se ya sake cewa

"Can I?"

Girgiza mai kai nayi alamar A'a, sake cewa yayi

"Toh Meyasa?"

Ban ce mishi komai ba saboda ban san amsar da zan bashi ba, cire hannun shi a jiki na yayi yace

"Don't worry I understand, ki barshi kawai se kin shirya"

Dik se naji babu dadi saboda ba laifin shi bane, ni ce mai laifin saboda ni na yarda na aure shi, Allah ya gani kuma bazan iya yarda Jabeer ya kusance ni ba, nafi so se na fara son shi tukunna, To a yaushe zan fara son shi?

Babu ranar fara son shi Hajia Tasneem saboda tun farko ba kya son shi, amma qila halin shi na qwarai ya sa ki fara son shi.

"Marry someone you truly love, don't get married because you don't have any choice, don't get married because your mates are getting married, don't get married because of your selfish interest, marry because you want to complete half of your deen and for Allah's sake"

Dedicated To Chuchujay

Aisha Ameerah❤️

TASNEEM 1 in TASNEEM Series✅Where stories live. Discover now