.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
             Ikon ALLAH ne kawai yakai Safna gida, tana shiga d'akinta tanufa Dan falo babu kowa tasan ummi tana barci k'ila.
   Tafad'a kan gado jagwaf kamar wadda akacema Abba yamutu haka tashiga kuka rurus, saidai tayi mai isarta sannan tayi shiru danba mai lallashi, yauce rana tafarko dataji kewar Rahma, Dan dukda tsangwamarta datakeyi indai yarinyar taganta cikin damuwa ita take lallashinta da kwantar mata da hankali, amma yau tamata nisa.
      Tacije le6enta tana k'ara zubda kwalla masu zafi, ta ce, ''nad'au alk'awarin kota halin k'ak'a saina auri guy d'inanan, kuma saina rabashi da matar tasa Dan bazanyi shearing d'insa dakowacce maceba, banta6a Neman Abu narasaba a duniyar nan, nasan kaima bazan rasakaba bobona.
   Ban ta6a bin malamaiba ko bokaye, bammasan inda sukeba, amma awannan karon duk inda suke saina nemosu, kuma zan kashe konawane Dan in mallakeka mijina, wasu zafafan hawaye suka zubo mata, kuka takeyi sosai da zuba sambatu harma da sa6o.
 

( Na ce, "hummmmm safna kenan, duk d'an daya hana uwarsa barci tofa shima bazai yiba).

------------------------:::::::::::
    Agidan Bobo kam Rahma da Nawal ne suke wasan 'Yar 6oye, Rahma tarufe ido da k'yalle Nawal kuma ta6uya Rahma na nemanta, Nawal ta ta6ata tana fad'in momy kin ganni, da Sauri Rahma tajuyo inda taji maganar Nawal.
   Bobo yashigo da sallama wadda babu Wanda yajita, tsayawa yayi yana kallonsu cike da burgewa, Rahma dake laluben Nawal tak'aro inda yake tana laluben Nema, jitayi ta damk'i wani hannu mai laushi da santsi.
   Da sauri tacire k'yallen data rufe fuska danjin Nawal tana tafa hannu tana dariya dafad'in shikenan baby zai goya momy.
  Kallon ido cikin ido sukaima juna shida ita saikuma suka dawo da kallonsu kan Nawal.
   Baby ka ajiye jaka ka goya momy kawai.
  Da sauri Rahma ta ce, " nikam Nawal na yafe.
  Nawal ta k'ya6e fuska tana fad'in um um nidai sai yayi miki goyon, saikitacewa kin yafe kullum kullum.
   Kan Rahma ak'asa ta ce, "toki bari yahuta kinga yazu yadawo daga aiki, tajawota jikinta tana lallashi.
  Bobo yawuce d'akinsa yana murmushin darun Nawal.

Bayan yayi wanka yafito sanye da wando iya guywa da Riga k'arama, Rahma tamik'e kanta ak'asa ta ce, " ga abincifa.
   Baice mata komaiba yanufi dinning, itama baya ta take masa, bayan ya zauna tafara had'a masa komai, sai satar kallonta yake k'asa k'asa, tagama takoma falo taja Nawal suka koma tsakar gidan dansu sha iska.
   Bayan kamar minti 30 suka dawo, sannan bobo ya kammala yanazaune da jaridar tasa ta fama.
   Nawal ta ce, "yauwa baby tashi kagoya momyn to.
  Da sauri Rahma tanufi d'aki dantaga rigimar Nawal bazata k'areba.
   Bobo yajawo Nawal yad'ora kan cinyarsa, kinga babyna kibari zan goya momynki  amma ba yauba, kinga yau nagaji, yak'are maganar da sumbatar kumatunta.
   Nawal ta k'ya6e fuska ita adole bata yardaba.
   Ganin zata takura masa, shikuma soyake yahuta saboda yagaji sosai, ya ce, "to tashi muje na goyata, tamik'e yarik'e mata hannu suka nufi d'akin Rahma.
    Tana zaune bakin gado tana wasa da wani d'an babyn Nawal, suka shigo, ta d'ago kai tana kallonsu, suna had'a ido da bobo ta kauda idonta.
   Nawal ta ce, " momy tashi baby yamiki goyonki.
  Rahma tabud'e baki zatayi magana Bobo yad'aga mata hannu, karki damu yarinyar nan taki ba k'yalemu zatayiba inhar ba'ayi goyonnanba, Dan haka taso kawai nayi muhuta.
   Da sauri Rahma takallesa danjin furicin bakinsa, yama za'ayi harta iya yarda ya goyata saikace wata yarinya.
   Bata ankaraba taga ya tsugunna yana jiran tahau kenan.
   Cikin sanyin murya ta ce, "Dan ALLAH kayi hak'uri bazan iyaba.
  Juyowa yay yana kallonta fuska a d'aure, ya ce, "amma dai kinsan Nawal dashegen naci, indai ba goyonnan nayiba ba barina zatayi na hutaba, nikam natsani adameni da hayaniya.
   Ganin yanda yake magana cikin fad'a amma hakan baihana muryarsa fita cikin nutsuwa da taushiba yasa dole tasakko daga gadon, amma tayi tsaye takasa hawa saboda tana matuk'ar jin kunyaarsa.
  Momy kihau baby yana jiranki Nawal tafad'a tana kallonta.
  Hararar da Bobo ya watso matace tasata saurin d'anewa bayansa.
   Shikuma yamik'e yanufi falo da ita, Nawal nabiye dasu tana dariya.
  Yajuyo yana kallon Nawal to nagama ko baby?.
    Lah baby saikaje d'aki da'ita sau uku kana dawowa, haka yayta zarya daga falo zuwa d'aki harsau uku, ana ukunne yadireta saman doguwar kujera yana fad'in wash bayana, wlhy momyn Nawal kincika nauyi.
   Rahma tayi k'asa dakai cike da kunya, yabata dariya wlhy, sai wani yatsine fuska yake da rik'e k'ugu tamkar zaiyi kuka, amma saita gimtse, wai yau itace namiji yagoya, da gudu tabar wajen tanufi bedroom.
   Shikam dariyama tabashi Dan haka yad'an murmusa tareda zama saman kujerar, wani nishad'i na musamman yatsinci kansa aciki, yajingina kansa da kujera tareda lumshe fararen idanunsa yana cigaba dasakin lallausan murmushi.

Har aka kira sallar magriba yafita Rahma bata sake fitowaba, gani take bazatama iya had'a ido dashiba aii.
    Saida akayi isha'i yashigo gidan dakayan kwalam da mak'ulashe, Rahma najin motsin dawowarsa ta tura Nawal itakam tayi kwanciyarta tak'i fita.
      Nawal taje tafad'a jikinsa tana masa oyoyo, shima rungumeta yayi yana fad'in babyna kinyi sallah?.
   Eh nayi nida momy, harta koyamin karatu.
   Ya ce, "iye kaga 'Yar gatam momynta, ina momyn taki to?.
   Tana d'aki wai zatayi barci, nikuma nazo wajenka nayi fira.
     Murmushi yayi Dan yagano tanajin kunyane dankarsu had'u, ya ce, " jeki kiramin ita.
   Da gudu tanufi d'akin, tafad'a saman Rahma dake kwance kan gado, momy kizo baby na kiranki.
   Rahma tadafe kai banace kice masa ina barciba?, kuma daga yau kiringa cemasa dady ba beby ba kinji babyna.
    To momy zandinga fad'a tashi muje to.
   Badan Rahma tasoba tasakko suka nufi falo itada Nawal.
   Yana zaune idonsa akan Tv yana kallon labarai ta ce, "sannu da dawowa.
  Yauwa yafad'a batareda ya kalletaba, ya ce, "ga wannan yamik'a mata ledan kayan motsa bakin.
   ALLAH yasaka da alkairi tafad'a tana kar6a, kicin tanufa itada Nawal suka juyo afilat, wad'anda bazasu ciyuba tasaka afirij.
   Takawo masa nasa itakuma tad'auki nasu danufi sutafi d'akinta suci, ya ce, " ina zakuje kuma?.
   Kanta ak'asa ta ce, "d'aki.
       sabodani zakuje d'aki cin abinci?.
   Dawowa tayi tazauna batareda tabashi amsaba, saidai akunyace takeci, shikuma yana satar kallonta har suka gama tashige d'aki tabarsu shida 'yarshi.
     Shirin barci tayi tai kwanciyarta, dama kayan barcine ajikin Nawal.

Yana gama kallon labarai shima yamik'e da Nawal ajikinsa datai barci, yakashe komai sannan yanufu d'akin Rahma.
    Ahankali yasauke Nawal akusada ita, yay musu addu'a sannan yaja bargo yarufesu idonsa akan Rahma, yanda take barci hankali kwance sai fuskarta tayi wani wasai.
   Jiki asanyaye yanufi d'akinsa yay shirin barci shima yakwanta...............

[14:23, 10/09/2017]

ABDUL-MALEEK (BOBO)जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें