KASAR WAJE. 1

7.3K 222 26
                                    

✈️✈️ *KASAR WAJE*✈️✈️

                    *NA*

   *Maryam Abubakar Datti*
      

🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫🛫
🛬🛬🛬🛬
AREWA HAUSA NOVELS
MARYAMDATTI200 =wattpadd

01/04/2020

Page. 1/2
BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

Kawo Kaduna!

Tana zaune 3sitter d'in falonta tanata kallace-kallacen hotuna a Istagram inda ta ga hotonan wasu abokai matasa su biyu sun bala'en had'uwa musamman d'ayan

d'an tsayuwa tayi tanata kallon hotunan inda tana kallon hotonan wani tunani take na burin da suka dad'e suna yi a rayuwarsu

Shiga accnt d'in mai hoton tayi sosai sunansa ta kalla Yasir Mai tumbi

Tunani ta d'an tsaya tana yi a ina take jin sunan tabbas a nan Kaduna ne

Fita daga ista tayi ta shiga Facebk inda ta shigar da sunan ta fara dubawa ay kuwa ta gani ta fara shiga sosai har hotunan da ta gani a ista inda taga hotunan tare da sunan sauran da ke kan hoton

Bibiya ta k'ara yi tana so ta gane wanda hankalinta ya kai kansa shi meye sunansa

Don haka ta k'ara jefa sunan farko dake saman hoton "Yusuf Suleiman"

Ay kuwa shima ta ga nasa accont ta shiga

Tsayuwa tayi ta karanta komai na information d'insa dake accnt saidai babu wani information sosai sai sunansa da origin d'insa da garin da yake yanzu wato "Toronto Canada"

Ajiyar zuciya tayi gaskiya wannan shine perfect miji da suka dad'e suna yiwa HAYFA buri dukda ita hayfar na soyayya da Kamal amma ga wannan da gani d'an wani k'usa ne gashi babu laifi yanada kyaw da kwarjini

Nan dai Aunty ammah ta turawa yusuf friend request inda tayi sa'a tana shirin sauka jin an kira asar shi kuma Yusuf na hawa yana gani haka kawai shima bai saba saurin ansa request ba hasalima shi abokansa basuda yawa sabida baya ansa request

Ganin har ya ansa ammah ta tura masa da gaisuwa

Yusuf bai iya ansa mata ba ya share ya sauka!

d'an shiru tayi na takaici yaga msg d'inta bai ansa ba

Saidai d'an tsaki tayi tace haka suke shegu yaran masu kud'i girman kai amma wlh kaine abinda muka dad'e muna nema ni da goggo da Adda suwaiba kuma IA burinmu zai cika

Kashe data tayi ta mik'e taje tayi sallah kafin su hayfa su dawo tanason yin d'an bacci

MALAM HALADU

Ba barbarene d'an asalin garin maiduguri yawon cirani ya kawoshi kaduna yake gyaran agogo a badarawa

A nan Kaduna ya auri matarsa y'ar garin ancau Hausa-fulani ce dake kaduna, sunanta Aljanna saidai suna kiranta goggo alje da fillanci

sunyi aurensu sunada yara 2 duka mata Suwaiba itace babba sai Amina ana kiranta Ammah kasancewar sunan kakarsu mahaifiyar babansu take ci

Tun bayan haihuwarsu Suwaiba da ammah goggo alje bata k'ara haihuwa ba ana haka wani mak'ocin malam haladu buzu y'an gudun hijiraatarsa ta rasu sai y'arsa d'aya shima baya lafiya sosai ya rok'i malam haladu ya auri y'ar mai suna safiyya

Bayan auren malam haladu da safiyya da kwana tara babanta ya rasu

Itama safiyya shekara d'aya da aure tazo haihuwa ta haifi y'arta mace ta rasu wacce aka sawa suna Hadiza sunan kakarta ta gun uwa saidai ana kiranta HAYFA

KASAR WAJEOnde histórias criam vida. Descubra agora