SHURAKH

629 22 0
                                    

🏅🏅🏅🏅
🏅🏅🏅
🏅🏅
🏅

*_SHURAKH_*

_Daga alk'alamin 📝 jienie ďaya_

® _By_

_Sis Abeedah Tauhtah 😘_

*Da*

_Basira Sabo Nadabo 😘_

© *_Anielurv Group Writes_* _{AGW}_

Ern

*_Zamani Writers Association_* _{ZWA}_

Wattpad @ Basira_Nadabo


Hey come here's your dedication my sweetat, my bae, my honey, my apple, my watermelon, my melody, my pineapple you are my everything durlin *_RAMALUV_* I really do appreciate for your love and care, we are together til d world end In Shaaa Allah sweetie durlin




@ Page Thirty_Nine (39)

Last page In Shaaa Allah


Kai wallahi karya ne manu bazai dawo ba yama za'a ce manu ya dawo ina karya ne wallahi a bakin shifa nasaka bari na tashi na tafi gurin boka mai ran karfe, ya tashi da sauri kamar wanda aka tsikara da allura gurin boka ya nufa acen bayan gari yana zuwa ya fara kundumar ashariya, gafara bata tabbata ga makiyin Allah, kaci kutumar ubanka, tun aduniya kasan makomarka la'anannen Allah Ta'ala, kaga wanda yafi sheďen sheďanci kaga ďan....

Cikin tsawa yace Ya isheka haka ka karya mana alkawari, kaki sa layar a bakin mahaifinka ka warware mana kudurin mu to muma baza mu barka ba tare zamu mutu, tabbas la'anar Allah ya tabbata a kaina kuma gafarar Allah baya tabbata gamai zuwa gurin boka Sunusi kaima sai ka ďanďane azabarka tun a duniya hakkin yarinyar yayanka bazai kyaleka ba kaje amma ka tuna wanda yayi maka jagora zuwa gurina yana cen ya mutu nima tawa ta kare kaima kajira hukunci daga Ubangiji mai girma ka fita anan ganin ka karuwar azaba ne a gare ni, wayyo duniya ina sonka zan barka wuta ne yake ci a jikin shi sai ihu yakeyi ni kaina sai da na razana saboda ihun kanshi abin tsoro ne balle kuma ganin shi, da gudu Sunusi ya fita yayo cikin gari yana ihu bai tsaya a ko ina ba sai gidan su Shurakh yana shiga ya tarar da Inna Farida tare da malam sani suna zaune idon inna Farida ya kaďu yayi jaa saboda kuka, yana ganin su ya fara sambatu

Nine wallahi nine kuma ba laifina bane laifin waziri ne shine ya kaini shine kuma yace bazaka dawo ba boka ma ya faďa min haka kuma sai gaka wallahi shine

Malam sani yayi gyaran murya yace Ya SubhanAllah malam Sunusi lafiyar ka kuwa meya same ka ne haka anya kana lafiya kuwa SubhanAllah kaga Manu tashi ka kamashi ya zauna koma menene sai muji

Ni'iema abinma tsoro ya bata sai muka zama yan kallo, Abba na ya kama baba Sunusi ya zauna

Malam Sunusi lafiya kake tafe kake surutu kodai wani abune ya faru

Ya fashe da kuka yace baba sani na cuce kaina nabi son duniya kuma duniya ta nuna min cewa ita ba matabbata bane, nine nasawa Baba mai gari laya a baki yaya Usman yabar garin nan tun Shurakh tana ciki kuma gadon sa da aka raba na hau kai na zauna, na musgunawa rayuwar Zainaba nida Farida muka haďu muka cutar da maryama nine nasawa Inna Aisha maganin bera a abincin da maryama take kawo wa taci ta mutu, naso wahalar da Shurakh ta sanadiyyar haďata aure da Kawu sai wani ďan shan jini yazo yace yana son aurenta to saboda bakin cikin da nakeyi da ita ba tare dana san koshi waye ba na bayar da ita tare da cemin zai sa mata ciwo mai karya garkuwar jiki wallahi duk laifin waziri ne kuma saida boka mai ran karfe yace min duk randa kadawo ďayan mu zai mutu kuma ďaya zayyi hauka mukace mun yarda idon mu ya rufe saboda mulki kuma gashi yau alkadari na ya karye, ya kara fashewa da kuka kaico na Allah wadaran masu irin halina nayi nadama, nadamar da bashi da amfani domin boka ya kone da wuta ba tare da kalanzir ko ashana ba kuma yace min waziri ya mutu nima nasan tawa azabar tana tafe nan bada daďewa ba

SHURAKH Where stories live. Discover now