SHURAKH

536 30 0
                                    

🏅🏅🏅🏅
🏅🏅🏅
🏅🏅
🏅

*_SHURAKH_*

_Daga alk'alamin 📝 jienie ďaya_

® _By_

_Sis Abeedah Tauhtah 😘_

*Da*

_Basira Sabo Nadabo 😘_

*_Anielurv Group Writes_* _{AGW}_


Dedicated to *YAR ALJANNA CE KE In Shaaa ALLAH* ina sonki sosai, Nagode da soyayyarki gare ni, Allah yabar so da kauna Amin Ya Allah #One Lurv❤

Wattpad @ Basira_Nadabo

@ Page Twenty-One (21)

Hmmm Rukiee ni tawa kaddarar kenan amma na yarda da kaddara me kyau ko akasin hakan Rukiee kedai ki tayani da addu'a amma wai Kawu ne zan aura mutumin dako alwalarsa bayayi dai dai amma ace shine mijina yanzu innayi ba dai dai ba a addini nah wazai min gyara nasan shi kuma bazai yarda na koyar dashi ba

Hmm aida abin arziki ne kawun bake zasu aura mawa ba amma da yake abin tsiya ne an nemeki bakomai akwai Allah kuma shine maganin kukan mu kuma baza muji kunya ba kuma In Shaaa Allah tsiyarsu zai dawo kansu Allah baya bacci yana sane damu kiyi hakuri Shurakh kiyi musu biyayya inma sunyi niyyar cutar dake sai muga Allah ya musanya da alheri

Kayya! Rukiee bazaki gane bane to Allah ya yarda

Bari na aika a siyo min lalle na miki anjima sai muyi kitso kinga in bakiyi ba yan kauyen nan zasuyi zinďenki da nuna ki kinga gwara a tura musu a niyar su ki nuna kina son auran duk da a zuciyarki ba haka bane

To shikenan zanyi ne kawai don na kwantar ma Ummata hankali saboda itama hankalin ta ba a kwance yake ba

Anata hidima nidai nawa ido ne har ya kawo yau da za'a ďaura min aure da kawu nidai gani nan ne mutum mutumi kowa sai hada hada sukeyi ni kuma in banda kuka babu abinda nakeyi Rukiee ta bada hakurin tayi faďan tayi nasihar amma duk abanza dole ta kyale ni ta cigaba da harkarta amma karkashin zuciyarta itama kamar ta fashe da kukan take ji amma ba dama saboda zata kara karyar da zuciyar Shurakh ne karfin haline kawai takeyi Ummata ma duk wani motsina tana kula dashi tayi biris da kukan ne saboda bata son jama'a su fahimci halin da suke ciki,, dubban mutane ne keta shigowa kauyen marafa ku kunce kauyen tashi zayyi kowa sai ya zubawa sarautar Allah ido Kawu kuwa sai washe baki yakeyi za'ayi bikin da ba'a taba yin irinsa a kauyen ba donshi a wautar sa duk mutanen nan saboda shine suka zo, karfe 2:30pm dai dai ne dubban mutane suka shaida ďaurin auren Adams Abdullahi Mai Naira tare da amaryar sa Zainaba Usman Aliyu Kawu nagani warwas a kasa saka makon sunan da aka ambata kuma shine mallakin Shurakh sai cece kuce akeyi gari ya dauka mai gari ya siyar da yar yayansa saboda yaga yayan sa baya raye wasu suce ya siyar da da itah daman ya tsane tane shiyasa ya tsiyar da ita maganganu kala kala har zuwa gidan mu maimakon nayi bakin ciki wallahi wani irin farin ciki nakeji sai hamdala nakeyi saboda nasan Allah bazai taba barin na wulakanta ba saboda na yarda da Allah shine maiyin yadda yaso kuma Allah baya ba wanda ya dogara dashi kunya koma waye mijina zan amshe shi hannu biyu haka Ummata tana ta walwala saboda koma waye mijin Shurakh zata taya ta rokan Allah akan shi duk da wani zuciyar inajin tsoron wannan haďin nasan badon Allah bane amma kuma ai babu abinda ya gagari Allah la'asar nayi yan daukan amarya sukazo ďaukar amarya amanya manyan motoci masu alfarma ai sai fitowa akeyi kallon motar da sukazo dauka na gulma da tsegumi sai karuwa yakeyi nidai na toshe kunne na da duk abinda zai fito daga bakin mutane wasu suce ďanyan kan kaine wasu suce kyauta aka badani nidai nayi shirin yiwa koma waye biyayya da kyar aka babbare ni a jikin Ummata ina kuka sosai kamar raina zai fita saboda yau shine rana na farko da zanyi nisa da Ummata ko tafiya nayi bana kwana biyu zata ta aike har saina dawo, a haka na cigaba da kuka saboda ban san wani gari zani ba, Rukiee ce ke mijin fa ba ďan kauyen mu bane kodai maganar mutane gaskiya ne mai gari ya siyar dake daman yan kwanakin nan mai gari sai wadak'a da kuďi yakeyi nifa wallahi na fara tsorata gashi ji motarta da akazo daukarki a ciki gasu mutanen yan gayu ne masu kuďi, wani tsoro ne ya dirar min sai yanzu nake dana sanin bin yan daukar amarya yanzu ya zanyi amma bakomai akwai Allah a haka muka isa gidan driver yayi horn mai gadi yazo da gudu ya bude yana cikin budewa wayar dake aljihu sa yayi kara (ringing ) ya juya baya don ya duba me kiran shi yana ďagawa yaji company ne suke kiran shi yayi tsaki ya rufe gate ďin kafin ya gama har sun gama shigewa cikin gida ya koma ďakin sa gaban shi yana ta faďuwa ko menene dalili oho yana ta addu'a har ya samu faďuwar gaban ya ragu



Hmmm Allah yasa alkhairi ne dai Amin Ya Allah



_{AGW}_

SHURAKH Where stories live. Discover now