SHURAKH

643 31 0
                                    

🏅🏅🏅🏅
🏅🏅🏅
🏅🏅
🏅

*_SHURAKH_*

_Daga alk'alamin 📝 jienie daya_

® _By_


_Sis Abeedah Tauhtah 😘_

*Da*

_Basira Sabo Nadabo 😘_

© *_Anielurv Group Writes_* _{AGW}_

In kina / kana neman labarin Shurakh daga farko via my Wattpad @ Basira_Nadabo
Mun gode

_Humaira Humaira Humaira Melody Wow mungode sosai I can express how happy I am for your marvelous deduction to us A'B wallah muna sonki Sis you are not a friend you are like a sister to us,Tnchu so much we're really do appreciate lurv_
#munga kauna

Dedicated to my 1 and only ma Habibty Zarah Bukar, beb am in lurv wif you and ICDWU ILVSM Dear

@ Page Eleven (11)

Uwar mijinta tana sonta ta dauke ta y'a ba sirika ba, akasin wasu iyayen mijin su basu ma dauke su a sirikai ba sai dai kishiya wanda kuma hakan mai dace ba kema uwa ce in baki haifi mace ba kanwarki ta haifa ko kaninki ko kuma acikin danginki baza a rasa mace ba yadda kika tafiyyatar da yar wani haka kema za'ayi wa taki d'iyar Don Allah iyayen mu mata mu gyara Allah ya hadamu da sirikai nagari masu tsoran Allah Amin Ya Allah

Wasa wasa Ummata harta kusan shekara daya bata taba 'batan wata ba tun abin yana damunta harta barwa Allah komai tana jiran ikon sa a kanta

Inna Hafsat tasa Ummata a gaba da gori wai itah juya ce, Ummata bata taba damuwa ba saboda tasan duk daran dad'ewa itama Allah yana sane da ita kuma zai bata itama

Sannu sannu kwana nesa jikin tsufa ya motsa wa kakana harta kaiga baya iya magana baya cin komai sai dai in lokacin sallah yayi ya musu halama da suyi mishi alwala su fuskantar da fuskan shi zuwa alk'ibila ahaka yake sallah tunda tunda ya fara ciwo kullun Baba na ne ke kula dashi shine yake mishi komai

*MAFARIN LAMARI*

Yau jumma'a kaka na ya tara yaranshi gaba daya da nacikin marafa da wanda suke birnin kaduna cikin ikon Allah ne kaka na yake magana bayan yayi sallama da yabo da jinjina ga fiyayyen halitta _Annabi Muhammad (S,A,W)_ ya kira sunayen yaranshi gaba daya harda Baba Ahmad da Baba Abubakar da Inna Zainaba yace su zama shaida yau ni Aliyu nayi muramus na naďa daya daga cikin yara na shugaban wannan kauye namu mai albarka na naďa....... Sai tari ya tsarke shi Baba Sunusi har yana murna yau zai zama mai garin wannan kauyen shima za'a fara damawa dashi yau mafarkin shi zai zama gaskiya yau kam burinshi zai cika, suna ta mishi sannu Baba na ya bashi ruwa yasha sannan yayi hamdala kana ya ďaura da cewa ni Aliyu na naďa USMAN mai garin kauyen nan jama'a ku shaida daga yanzu Usman shine shugabanku, wani irin faďuwar gaba ne ya sauka a zuciyar Baba Sunusi sai kallan juna sukeyi da waziri saboda yaji zancen kamar saukan aradu, Baba na yana shirin yin magana kaka ya dakatar dashi yace bana son jin komai kuma ba shawarar ka nake nema ba, waziri kayi hakuri karka ce naki maganar ka sannan yace kowa ya watse aka bar waziri

Waziri kayi hakuri na yanke hukunci ba tare da shawarar kaba kuma karka ce naki maganar ka ni kaďai nasan me yasa nayi haka Don Allah waziri ga amanar yarana duka a hannunka ka rike minsu tsakani da Allah kai kanka sheda ne nafi son Usman amma nake nunawa Sunusi ne ďan gata saboda bana son ya lalace ka rike su amana amana, amana Don Allah waziri na hada ka da Allah

Waziri ne ya gyara zama don shima zance bai mishi daďi ba ba ya share zufa tare da cewa ai duk yanda kayi dai dai ne Allah ya baka lafiya kuma zan rike mana bilhakki da gaskiya

To Allah yasa zaka iya fita ka turo min Manu

To atashi lafiya, yana ta share zufa kamar wanda ya haďiye kwaďo

Da sallama ya shiga cikin ladabi ya tsugguna a gaban mai gari, gani Alasaini

Amm Manu kayi hakuri da hukuncin dana yanke ka amshi sarautan nan saboda nasan ko bayan raina baza ka wulakanta jama'arka ba kuma In Shaaa Allah inaji a jikina jinin ka shine abin alfahari a garin nan ka kara hakuri komai yana da lokaci karkabi zigan mata su kullun basu da hankali sai kaga karamin yaro ya fisu tunani Usman kayi hakuri da duk yadda rayuwa tazo maka ka rike Allah duk rintsi karka sake Allah kuma karka zama ďaya daga cikin mutane masu yima Allah gatse, kayi hakuri da rayuwa kayi hakuri da duk inda ka tsinci kanka wannan gurin anan rahamarka zata same ka, kayi hakuri da duk wanda yake karkashin ka karka zalinci wani kabari shiya zalince ka Usman duk inda ka tsinci kanka ka zauna a gurin rahamarka yana gurin kuma zai same ka Manu Allah yayi muku albarka karkayi kuka Manu nima ina jin wannan zafin ka tafi Usman in lokacin sallah yayi kazo kamin alwala....

_haba kaka Aliyu irin wannan dogon bayani harka tsinke min gaba ke dai Sis Basira bari ni kaina na koka, readers da fans kuma ku taya mu kuka Allah zuciya na ya karye sis_



_{AGW}_

SHURAKH Where stories live. Discover now