SHURAKH

543 29 0
                                    

🏅🏅🏅🏅
🏅🏅🏅
🏅🏅
🏅

*_SHURAKH_*

_Daga alk'alamin 📝 jienie ďaya_

® _By_

_Sis Abeedah Tauhtah 😘_

*Da*

_Basira Sabo Nadabo_

*_Anielurv Group Writes_* _{AGW}_

Wattpad @ Basira_Nadabo


_Shafin nan naka ne Yarima (Prince Adams Sunusi) wallah ina jin daďin kulawarka gare ni Allah ya kauda idon makiya a masarautar ku, ya kara daukaka masarautar ku ina godiya kuma naga sakon ka Allah yabar so da kauna_



@ Page Twenty_Eight (28)

Abinci ne kuma kai kace nayi don haka abinda nake sonci shine zan dafa, ke kuma da kike magana daga ke har mijinki bakwa gabana kuma gulmar me zamuyi anan abu ba fasali ai wanda ya isa ake gulmar shi toke baki isaba kuma gulmar me zamuyi me kike takama dashi ni banga abin gulma a tattare dake ba ni bance mijinki ya aure ni ba shine yace yaji ya gani kuma ya rabani da masoyina ni dama zaki burgeni da kince ya rabu dani na kara nanatawa a gaban shi in kin isa kice ya bani takarda na bana sonshi baku san darajar kowa ba balle kuji imanin mutun ke ni bani da lokacinki fita min a ďaki kafin a fitar dake ta nuna mata hanyar fita

Adams yaja hannun ta suka fita

Yanzu baby babu abinda zakayi ko ta face da kuka

Ta rufe kofar tare da zama a kujera ta sake kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro

Don Allah kiyi hakuri kibar kukan muma zamu iya kuka cewar feedie

Firdausi mutanan nan basu da imani basu san darajar Dan Adam ba ranar nan wallahi kamar ance in buďe window naga yayan ku yana marin Baba mai gadi shi kuma sai hakuri yake bashi amma kamar kara zuga shi yakeyi wallahi mari uku yayi masa suka haďu shida matar shi suka cima tsohon nan rashin mutunci haba aiko don tsufar mutumin nan da girmama furfuran shi sun raga mishi ai, na gaji da zaman gidan nan ban san ranar hutuna a rayuwar nan ba kullun da irin bakin cikin da nake kunsa, ni daman zai sani a makaranta da naji daďi taja majina amma don Allah karku faďawa ummun halin da ake ciki In Shaaa Allah zai gane kuma kuyi hakuri da rashin kunyar da nayiwa yayan ku

Wallahi kin min dai dai hakan da kikayi ya burgeni da ni nice wallahi marin zan mata ta fada tare da share hawayen ta tun lokacin da Shurakh ta fara kuka itama take taya ta, aunty Shurakh ummun baza taji maganar nan ba wallahi duk wanda ya takaki kema ki murkushe shi ki amsarwa kanki yanci kuma kina mugun kama da ba........

Dallah kiyi mana shuru kin fiya surutun tsiya ke da zaki bata hakuri amma kece mai ce mata tayi aunty Shurakh Don Allah kiyi hakuri In Allah ya yarda _Ke Alheri ce (Sis biebee Isa )_ a gidan nan kuma sai sun dawo suna baki hakuri a lokacin da hakuri bazayyi tasiri ba nasan halin bro kila akwai wani abunda kikayi masa ne ya kasa yafewa nasan shi da kullatan abu a rai amma In Shaaa Allah watarana sai labari kiyi hakuri aunty Shurakh

Bakomai feedie ya wuce amma ki sani _Bazan Barshi Ba(Sis Billy Giro)_ in har ta tanka min nima zan tanka ta yayan kune kawai zan ďagawa kafa saboda shi miji nane amma bazan kara bari su wulakanta ni ba na riga da na birne duk wani hakuri na a kauyen mu babu mai takani na barshi kowaye kuwa kuma Don Allah karku fadawa ummun komai ni ďin nan zan amsa 'yancina da kaina a gidan nan

Aunty Shurakh kiyi hakuri Allah yana tare da masu hakuri kuma zanma ummun magana tayiwa brox magana ya saki a makaranta tunda kila kin ďanyi nisa

Eh nayi nisa nie'nie a Jss3 na tsaya

Yauwa to kawai sai kiyi jsce ki fara daga Ss1 kinga in kina zuwa makaranta zaki koya yadda zaki zauna da duk wani kwaro dake gidan nan cewar ni'iema

Nine kwaro ko ni'iema to ku tashi kubar min gidana tunda abinda ya kawo ku kenan harda ke ko feedie ke da nake gani mai hankali kin zauna kuna biyewa wannan 'yar kauyen ko ke kuma rasa kunya 'beran tanka zan haďu dake ku fita nace kucewa ummun ina nan zuwa, ya juya ya fita rai a bace wato yarinyar nan sirrin gidana take fadawa su feedie ko Allah yasa kar baki abin maganar cen ta faďawa ummun ta 'ballo min ruwa haka yake ta magana a zuciyar shi har ya shige ďakin Falie domin cigaba da lalla shinta

Muka fito tare suna kara bani hakuri sannan suka kara jaddada min da yardan Allah na kusan fara zuwa makaranta na rako su har bakin kofar parlour nasa kafa kenan zan fita na tuno da maganar Adams _(kuma ko kofar parlour ban yarda kije ba)_ sannan Ummata tace _(Kizama mai biyayya ga mijinki da bin umarninsa Shurakh)_ nayi saurin dawo da kafata kamar wacce ta taka allura tare da cewa kunga nayi mantuwa zan ďaura abinci zan bark daga nan sai mun kara haďuwa kuce ina gaida ummun gobe da misalin karfe 2:00pm a turo driver zan bashi sako ne don naga kamar babu driver

Akwai driver mana

To shikenan In Shaaa Allah gobe yana nan zuwa

To aunty Shurakh mun tafi sai anjima mun gode sosai

Haba mana bakomai feedie ai yiwa kaine kuma ai gidan yayan kune kuna da iko da duk abinda ke gidan bama niba ku gaida min da ummun

Ina tsaye a bakin window sai da naga tashin su na koma ďaki na don yau babu abinda zanyi koba komai yau ina cikin nishaďi kai mutun rahama ne





_{AGW}_

SHURAKH Where stories live. Discover now