SHURAKH

521 9 0
                                    

🏅🏅🏅🏅
🏅🏅🏅
🏅🏅
🏅

*_SHURAKH_*

_Daga alk'alamin 📝 jienie ďaya_

® _By_


_Sis Abeedah Tauhtah 😘_

*Da*

_Basira Sabo Nadabo 😘_

© *_Anielurv Group Writes_* _{AGW}_

Sadaukarwa ga masoyan littafin SHURAKH a duk inda kuke muna ganin sakonnin ku muna godia sosai Allah ya barmu da masoya nagari a duk inda kuke muma muna sonku ina *UMMU AMATULLAH* Don Allah a duk inda kike ina nemanki ruwa ajallo, Ummu Ama Don Allah ki bayyana min kanki kina nan a cikin group din Aysha Sada Machika ina zaman jiranki. Nagode

@ Page Fourteen (14)

Shima ranshi zafi yake masa kamar ana zuba masa barkono ake shafa man abonoki maimakon yaje gurin zaman makoki kawai muka ga ya canza hanya tun muna binshi har muka gaji da tafiya don daga ganin halama tafiyar ba mai karewa bane muka dawo domin cigaba da kawo muku rahoto wasa wasa magriba yayi malam bai dawo ba kai har bayan sallar isha'i malam bai dawo ba kuma ba tsarin shi bane daďewa a awaje har bayan sallar isha'i na kasa bacci sai juyi nakeyi akan tabarma asubar fari na fita zuwa gidan mai gari ďakin Inna Aisha na gani a buďe na tura tare da sallama na tarar da Inna zaune tana lazimi saboda tun jiya take jin faďuwar gaba da rashin kuzari haka kawai takeji ajikin ta wani abu zai faru da ita, na zauna inata kallon kofar ďakin ko zai shigo saboda al'adarsa ne bayan ya fito daga massalacin sallar asuba ďakin Inna yake fara zuwa kafin ya dawo gida amma yau kam shiru babu halamar shigowar shi

Inna tayi sallama tare da tambayar me yakawo ni da asussubar nan, na fashe da kuka inna tun jiya banga malam ba na duba ko ina baya nan bai kwana a gida ba kuma gashi gari ya fara wayewa babu shi babu halamar shi, duk cikin kuka take magana ta karashe tare da fyace magina

Nima maryama inajin abinda kike ji koma ince nafiki saboda ni ďa nane ke kuma miji ne shine kawai ya rage min a duniya shine sanyin idaniya na shine dariya na shine kuka na maryamu kiyi hakuri mu cigaba da addu'a Allah yasa duk inda yace yasa yana hannu na gari saboda 'batan ďan mutun a wannan lokaci sai dai addu'a to addu'a zamu cigaba mukai kukan mu gurin Allah yana tare damu kinji ko

To Inna Allah ya bayyana mana shi a duk inda yake Amin Ya Allah

Kije gida ki cigaba da rainon abinda ke cikin ki In Shaaa Allah zai zame mana waraka a wannan kullellen al'amarin

Kwana ďaya, sati ďaya, wata ďaya har fin watanni babu labarin Baba na ko kanin wanda yasan inda yake bamu gani ba

Gefen Baba Sunusi shi murna ya keyi da 'batan Baba na kome yasa oho

Yau kwanan kaka mai gari arba'in (40 days prayer) kuma dai dai da kwana talatin da uku (33) da 'batan Baba na , kuma yau ne aka naďa Baba Sunusi mai garin kauyen marafa, kuma har yau ďin babu labarin Baba na babu wanda ya ta'ba zuwa gaida Ummata agefen Baba na ko maganar ma babu meyi

Amaryar Baba Sunusi ce kawai ke taimakon Ummata har cikin ya isa haihuwa duk da girman cikin ta bai hata kula da Inna ba gashi cikin salihin ciki baya bata wahala sosai

Ranar laraba da rana tsaka ciwon nakuda yayi wa Ummata sallama da misalin 3:35pm Ummata ta haifeni tare da taimakon Aunty Amarya, Ummata ta sauka lafiya unguwar zoma tazo ta dudduba Ummata tare da jaririyar duk suna cikin koshin lafiya yan barka sai zuwa sukeyi a dalilin haihuwa ta Ummata da umman Rukiee suka haďa kai suka zama kamar yan uwan juna sai dai mijin umman Rukiee baya son amintakar su saboda shi inda zai karu yake zuwa ba inda za'a rage shi ba

Ranar suna yarinya taci sunan ZAINABA ana mata inkiya da SHURAKH kamar yadda mahaifinta ya bukata Baba Sunusi shine ya siyo ragon suna inna farida da sauran kannenta sune suka kawo masarar da aka sarrafa shi akayi faten suna inna rahina itace ta kawo wa Ummata kayan fitar suna, inna mariya ce ta kawo wa jaririyar kayan suna tun daga wannan har zuwa yau da nake baku labarin rayuwata babu wanda ya ta'ba kawo kwayar gero gidan mu, inna Aisha ma Ummata tana kula da ita gashi duk yaran gidan babu me kula da inna watarana Inna Amina tana taimakon ta shima ba kullun ba

Shurakh ta taso cikin ladabi da biyayya nutsuwa da kamala tun yarantar ta bata da abokin faďa to yaushe ma ta fita balle har ta nemi tsokanar yara, Rukaiya yar attajirin kauyen mu ne islamiyar mu ďaya gurin zamar mu ďaya itace ta dinga shige min har na fara sakin jiki da ita, ganin bata zuwa makarantar boko ne yasa Rukiee ta ďaga hankalin ta har aka sani a skull wannan dalilin ne yasa Abban Rukiee ya tsane ni kuma baya son abotata da Rukiee amma da ya HAĎI DAGA ALLAH (khadijah Al'eeman ) ne shi yasa ya rabu damu amma in yana gida bana shiga gidan

Wattpad @ Basira_Nadabo

_{AGW}_

SHURAKH Where stories live. Discover now