SHURAKH

686 36 0
                                    

🏅🏅🏅🏅
🏅🏅🏅
🏅🏅
🏅
*_SHURAKH_*

_Daga alk'alamin 📝 jienie d'aya_

® _By_

_Sis Abeeda 😘_
*Da*

_Basira Sabo Nadabo 😘_

© *_Anielurv Group Writes_* _{AGW}_

_Wannan shafin naki ne Aunty Sis, wallah Allah ne kadai yasa irin son da muke muki kuma matakin da kika taka a birnin sararin samaniyar zuciyar mu babu wanda ya taba hango kurar gurin mudai fatan mu Allah ya raya mana Sultiee boo muzo katsina musha biki har mu gayyato JOHN-LEGEND ya rera mana All-Of-Me domin ranar ta masoya ne, muna sonki sosai Aunty Sis_

@ Page Six (6)

Ranar asabar ranar na fara zuwa koyarwa a islamiyar mu na fara cikin yardan Allah kuma duk wata ana biya na dubu biyar (5000) yanzu munfi karfin kudin haya da abinda zamu ci Rukiee ma tana iya bakin kokarin ta don tallafawa rayuwa ta duk da taso mu koma makaranta tare amma abin ya gagara don Abba yaki, da kudin albashin da ake bani na d'inka kaya kala biyu (2) don nima na dinga shiga cikin mutane da kyau Ummata kala uku (3) na siya mana dan madina wanda zamu dinga zuwa biki ko suna watarana nice nake sawa naje biki wasu lokutan kuma Ummata, muna cin abinci dai2 gwargwado har mu ajiyewa dan malan dake d'ibo mana ruwa a tuka tuka,

Yau tunda na tashi nakejin faduwar gaba na rasa meke damuna tun ina boyewa harta kaiga Ummata ta fahimce halin da nake ciki kuma ko za'asa wuka a wuyana bazan iya fadan musabbabin faduwar gaban ba, mai makon abin yayi sauki sai karuwa yakeyi naje na dauro alwala nayi sallah raka'a biyu nayiwa _Annabi (SAW) salati, nayi istigfari d'ari (100) saina fara karanta wannan tasbihin SUBHANALLHI WA BI'HAMDIHI WA SUBHANALLHIL AZIM_
_Ma'ana Tsarki ya tabbata ga Allah, tare da godiya gare shi' tsarki ya tabbata ga Allah mai girma_
*(Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi yace; Akwai wasu kalmomi biyu masu saukin fad'a a harshe kuma masu dauyi akan mizani na ayyuka ranar k'iyama, masu soyuwa ga _Allah_ mai yawan jin kai)* _Allah yasa mu dace Amin Ya Allah_

( Yar Uwa kema ki gwada wannan tasbihin wallahi tun kafin ki kai iya inda kike son kaiwa zakiji damuwarki ta yaye kunga riba biyu kenan gashi damuwar ta yaye kuma munyi ajiya mai nauyi a mizanin ayyukan mu _Allah_ yasa mudace Amin Ya Allah)

Tun kafin na karasa d'arin (100) naji faduwar gaban ta ragu ba kamar daa ba har wani farin ciki nakeji wanda ban tab'a jin irin saba nayi hamdala na karayiwa _Annabi (SAW)_ salati nayi addu'a Allah yasa alkhairi ne Amin _(Jienie d'aya ma munce Amin Zainaba)_

Shurakh fito kije gidan innarki ki amso min sako

Na fito ina gyara daurin zani na nace gani Ummata

Yauwa yar albarka jeki maza ki dawo kinga magriba ta kawo kai kice ta baki sakon yi sauri kinji d'iyar albarka wacce aka haifa tsiya na bacci ko tace ki kwana karki kwana ki dawo gida kinji ko Zainaba

To Ummata sai na dawo

Na fita ina tafiya ta cikin natsuwa Ahmad dan gidan mai gari wanda ake kira da kawu ne yasha gabana

Ke Shurakh dan wulakanci kina jina ina kiranki shine kikayi banza dani ke ba yar kowa ba a garin nan amma sai ki dinga jawa mutane aji ga wani girman kai kamar yar mai gari ko mu da muke y'ay'an sarauta bamuyi girman kaiba saike yar talakawa wacce ubanta ma ya gudu saboda bakar kafar mamanki wallahi kina cin darajan mai gari da saina sauke miki wannan girman kan nan kuma naga uban daya tsaya miki...

Kuyi hakuri da wannan wallahi na dawo daga skull ne yau nagama exams duk na gaji don karna barku shuru shine yasa na rubuta muku, kuyi min addu'a Allah yasa na fito da fly colours result nagode readers and fans.

_4 ur comment only 07030515774_

_{AGW}_

SHURAKH Where stories live. Discover now