SHURAKH

579 28 0
                                    

🏅🏅🏅🏅
🏅🏅🏅
🏅🏅
🏅

*_SHURAKH_*

_Daga alk'alamin 📝 jienie ďaya_

® _By_

_Sis Abeedah Tauhtah 😘_

*Da*

_Basira Sabo Nadabo 😘_

*_Anielurv Group Writes_* _{AGW}_


Wattpad @ Basira_Nadabo



*Shafin nan naka ne Alhaji Admin gwarzo uban ragwayen maza, kayi tasu sun kara yin taka baiwar ka daga gurin Allah yake ba daga hannun mutun ba, kunga mai maida sharri ya koma alkhairi, taka sannu sannu mahassadar ka fadawarkau, wallahi kayi gaba sai dai su biyo ka abaya, Alhaji Admin fadawa duniya soyayyarka bata lokaci ne tunda kai kasan inayi shikenan* Nagode kuma ina kara yadda da kalmar _Ana bala'in tare wallahi_ one lurv ❤


Dedicated to my awesome, durlin strawberry, sweetat like know other, a friend like you, you are different among them my sweet_sixteen Fa'iza Sabo Nadabo and Aysher Habib Tall I love you so much dearest Sis 💋




@ Page Thirty_Three (33)


*KAUYEN MARAFA*

Oh ni maryama yau shekara ashirin da biyu kenan da wata hudu da batan malam sannan har yau Abban Shurakh bai bayyana ba ko a mace ko a raye Allah kadai ya barwa kansa sani gashi jaririyar cikin daya bari yau wata1 kenan da auren ta kuma gashi sai nata mafarke wai malam yana kusa da wani nashi to waye kenan kuma me yasa yake shimin albarka a mafarki tunda malam ya bata a yan kwanakin nan ne mafarkin malam ya addabe ni ko baccin rana nakeyi hakan ne ke faruwa oh ni maryama Allah ka bayyana min malam a duk inda yake kasa yana hannu nagari Amin Ya Allah sai ta fara addu'an da yaza me mata ruwan sha kullun sai ga addu'an nan

*_Allaahumma Laa Sahla'illaa Maal Ja'altahu Sahlan Wa'anta Taja'alul-hazna'izan Shi'ita Sahlan_*

Kaman da hausa kace Ya Ubangiji ba wani abu me sauki sai abinda ka maida shi da sauki, kai kake maida damuwa ya zama sauki idan kaso

_Ibn Hibban ya ruwaito (2427)
_Ibn As-Sunni (351)_

Haka ma akwai hadisin da uwar muminai Sayyada Nana Aisha Allah ya kara mata yarda tace
Idan ba'kin ciki ko 'kunci ya samu ďayan ku to yace _ALLAHU ALLAHU LAUSHURIQU BIHI SHA'A_

Ga wacce zata haihu zata iya karantawa, ga wanda yake cikin damuwa shima ya karanta, haka zalika wanda neman abinci ya mishi wahala duk zai iya za'ban ďaya daga cikin addu'oin nan ya rinka karantawa

Sannan duk wanda yake bacin rai ya karanta _A'uzubillahi Minash Shaiďanin Rajiim_

Wallahu A'alam

(wannan addu'an sadaka ne ga duk wanda yake cikin damuwa kuma Don Allah duk wanda yaga addu'an nan ya roma iyaye na gafara a gurin Allah da sauran al'ummah Annabi Muhammad (S, A, W) Nagode )

Wannan addu'oin nake karantawa ba dare ba rana saboda nasan Allah maji rokon bawan sane ko ta ina rahamar sa zai iya sauka min bana gajiya da rokon Allah saboda nasan nima bai manta dani ba watarana zai bani nawa rabon ban taba cire rai daga rahamar ubangiji na ba nasan yana sane dani kuma zai bani duk da a yan kwanakin nan bayan tafiyar Shurakh nasha wuya amma bai sa na rasa abinda zanci a rana ba ko da sau ďaya ne Allah yana hore min

Assalamu Alaikum, umman mu Ina wuniee

Wa'alaikums Salamu Warahmatullahi Wabarakatuhu yar albarka mun wuni lafiya ya gida yasu mamanki

SHURAKH Where stories live. Discover now