SHURAKH

1K 44 0
                                    




~My Dedication goes to Aunty Sis and Aunty Anieelurv, Allah ya baku lafia yasa zakkan jiki ne, Amin,  Tnks 4 ur lurv and support dearest Aunties.

9-8-2017

Page Two (2


Don har saida na ƙara fitowa domin na tabbatar da gidan da nake, to banɗakin ne kamar ba'a shigar shi don tsab yake ko warin bayin nan da za ku ga wasu matan sun bar banɗakin su da kazanta ga wari, in anyi magana suce babu kuɗi ko kaji sunce da wanne zasuji da talauci ko da gyaran bayi amma sai muka ga akasin haka a bayin da muke tsammanin kudaje ne zasuyi mana sallama, ( Au ashe rahoto nake kawo muku ).

Wacce aka kira da Shurakh ce ta fito tana kokarin saka hijjab a jikinta, hijjabin dai tsab yake gashi a yamutse kamar an kwato a bakin kura a tunanina tunda aka ɗaura zare da allura gurin ɗinki ba'a taɓa goge shiba wuyar hijjabin tasha ɗauri da zare duk talaucin su bai hanata siyan turare yar ɗuri ba, zanin jikinta duk ya koɗe ya jeme ƙasar zanin har ya fara zare-zare na tsufa, rigar jikinta na zanin ne shima a koɗe yake duk tsufar kayan jikin Shurakh da hasken shi yake harda karin ninki a jikin koɗaɗɗen kayan jikin ta, silifas dake kafar ta a tsinke da zaren buhu na ga ta mishi dabaran ɗinke shi, in ba  shahararren mai sa ido ba, babu wanda zai gane dame aka dinke takalmin,  ɗan kunnen dake kunnan ta yayi baki har tsatsa yayi, doguwa ce wankan tarwaɗa ( chocolate colour )  bata da jiki amma komai ya zauna yadda ake so, tana da manyan ido amma ba masu girma sosai ba,  hancin ta daidai fuskarta bakin ta yana da fadi ba sosai ba, fuskarta da jikinta yayi daidai da shekarunta (22), da sallama ta shiga ɗakin da matar take ciki tare da tsugunawa ta ce.

"Ummata gani."

"Haba Shurakh kin san halin mutumin nan amma kika yi zamanki a daki kina tunanin da babu inda zai kaimu ai gwara ki fito musan abin yi tunda bazan ce ki cika ba don nasan baki da shi amma kije gurin umman rukiee ki ce ta ranta min naira goma sha biyar (15) in shaa Allahu anjima in an kawo wankau ko sirfe zan mai do mata da shi kuma ki ce ta kawo wankin na mata tunda na ga halamun malam audu yau bazai kawo na shi ba ga shi rana ya bullo kai."
      Cewar matar da Shurakh ta kira da Ummata.

"To Ummata zan faɗa mata amma batun aran kuɗin ki barshi akwai sauran canji a hannuna zan cika masa kuɗin shi In Sha Allahu ina fita zan kai masa kudin sa."

"A ina kika samu kuɗin da zaki cika masa? Nidai nasan ko taro bamu kwana da shi a gidan nan ba, sannan inda kina da kuɗi nice mutun ta farko da zan fara sani amma naji kina maganar kudi a ina kika samo kuɗin.?"
       Yaken dole na yi wanda yafi kuka ciwo sannan na ce

"Ummata ai akwai sauran canjin sirfen mu a gidan malam mudi cen zan tafi na karɓo sannan na biya na kaiwa malam tanko kuɗin hayarsa."

"To Shurakh don Allah ki mai da hankali ki kai masa kuɗin saboda gidan nan shine rufin asirin mu,  karki daɗe ki kai masa ki dawo musan abinda zamu tarfa a bakin salati."

"In Allah ya yarda ba zan daɗe ba Ummata sai nadawo."

"A dawo lafiya yarinya mai tunanin arziki, don Allah karki kula kowa duk wanda ya tanka mi ki ki yi banza da shi mun yi imani da Allah muma yana sane damu watarana sai labari."

"Ni dama bana kula su Ummata in ma na kula su suna da gatan da zai karbi bakin su ko da kuwa nice da gaskiya to dan me zan dinga kula su bayan bamu da karfi saina ubangiji."
          Maganar ya fito haɗe da gangaran hawaye.

"To ya isa share hawayan naki yi maza ki dawo yar umma."

"Ummata na tafi."

Basira Sabo Nadabo Ce.
                             

SHURAKH Where stories live. Discover now