SHURAKH

533 31 0
                                    

🏅🏅🏅🏅
🏅🏅🏅
🏅🏅
🏅


*_SHURAKH_*

_Daga alk'alamin 📝 jienie ďaya_

® _By_

_Sis Abeedah Tauhtah 😘_

*Da*

_Basira Sabo Nadabo 😘_

*_Anielurv Group Writes_* _{AGW}_

Wattpad @ Basira_Nadabo

I dedicate this page to my self Basira Sabo Nadabo, I really love my self muaahh 💋 and also my sweet sisters Muzeenat, Bilkisu, Ummulkhairi and auta Ni'iema baby nie'nie lurv I love you guys one lurv ❤ #Ana mugun tare wallahi muaaah 💋


@ Page Twenty_Three (23)

*KADUNA*

Yau yan kawo amarya suke haramar komawa karkara kuma abinda ke ďaure musu kai shine tunda aka kawo Shurakh basu taba sa mijin Shurakh a ido ba kai ko irin gaisuwar sirikan nan basu samu ba balle su sami arzikin ganin sa lallai mai gari ya ďibo da zafi wato fa ya siyar da itane Allah sarki Usman yau da shine a raye wallahi bazai wulakanta yaran Sunusi ba amma kullun uwar mijin ke hidima damu cewar wasu matan kauyen da suka rako Shurakh,

To Shurakh in kin gadama ki zauna in kin gadama ki kashe auren ki dawo mu zauna tare nifa daman ba son auren nan nakeyi ba ga malam tanko mutumin kirki ga arziki gashi duk kauyen nan shine mai kuďi ya daďe yana tayin ki naki yarda kuma har kyautar gida yace zai min indai na bashi ke amma ganin Kawu naso ne yasa nayi shuru, kuma ni tunda nake ban taba ganin inda aka kawo amarya ace mijin yaki zuwa ko sau ďaya ne yazo ya gaishe mu amma ina bamu da wannan matsayin kema yaushe ya girmamaki balle mu yan bani na iya ke ni gwara ma da baizo ba don ance ďan yan kan kai ne kar yazo ya yanke kawunan mu kum........ Horn driver yake ta musu shine ya katse mata dogon sharhinta inna Hafsat kenan take wa Shurakh fadan zaman aure

_Hmmm wannan ne fadan zaman aure ko kuma me Ma zan kira shine oho_

To mudai mun tafi Rukiee ta rungume ta tana kuka ta kai bakin ta kunnen ta nima na kara nawa don naji me tace amma duk son jin gulma irin nawa banjiyo komai ba na daiga Shurakh ta daina kuka ta koma dariya, Hajia Ayusha ta musu sha tara na arziki don tun farkon ganin ta da Shurakh taji tana sonta sosai kamar yarta data haifeta a cikin ta, haka suka tafi kowa baki buďe yana murna duk wanda na gani dafaffen hakoran sa zan fara hangowa a haka har motocin su suka fita

_Nace toooh mai kuka ya koma dariya ko menene mu sabbabin dariyar lokaci ne kawai zai iya bamu amsa_

Bayan duk sun tafi ya rage daga ni sai halina na zauna shuru, yau gani a ďakin aure na oho ni Shurakh wani irin aka bani zai soni ko nima yanke kan nawa zayyi kamar yadda kowa kecewa oho nidai tawa irin kaddarar kenan babu ranar jin daďi a rayuwa ta kenan turo kofar da akayi ne ya katsemin tunani na kara gyara mayafina na sunkuyar da kaina tare da rufe fuska ta, sai da ya gama kare min kallo sannan yace

Ke buďe fuskar ki ki kalle ni kina wani tsinne kai kamar munafuka to buďe donni ba amarya aka kawo gidana ba sai baiwa don wata baiwar ma tafiki daraja a idona

Muryar da naji ya mugun razana ni, Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un abinda baki na yake maimai tawa kenan ya ilahi na buďe tare da mai kallon rainin hankali na mike tsaye tare da rike kugu nace kai awa da zaka kirani da baiwa in ka manta bari na tuna maka niba baiwar gidanku bace, wani lafiyyan mari yayi mata ni kaina saida biro na ya faďi



_Kut daga kawo amarya sai duka wannan wani irin miji ne Shurakh ta samu Allah sarki baiwar Allah daga wannan sai wani ita dai bata da ranar farin ciki kenan, yau ya kama ta ace ranar farin cikin ta ne hmm_



_AGW}_

SHURAKH Where stories live. Discover now