SHURAKH

525 26 0
                                    

🏅🏅🏅🏅
🏅🏅🏅
🏅🏅
🏅

*_SHURAKH_*

_Daga alk'alamin 📝 jienie ďaya_

® _By_

_Sis Abeedah Tauhtah 😘_

*Da*

_Basira Sabo Nadabo 😘_

*_Anielurv Group Writes_* _{AGW}_


Wattpad @ Basira_Nadabo


*Allah sarki rayuwa wato in ALLAH yace Eh babu wanda ya isa yace A'ah haka in ALLAH yace A'ah babu wanda ya isa yace Eh, Allah ya jikan ka Ya Yunus Allah yayi maka rahama yasa mutuwar hutu ce a gareka ya Allah kasa hanashi ganin gudan jinin sa alkhairi ne a rayuwar sa ta lahira, Yan uwa yau ake sunan yaron brother na daya rasu yabar matar shi da ciki, hukuncin Ubangi baya karewa wato ranar alhamis on 16th Febuary uban yabar duniya haka kuma satin daya wuce ranar alhamis on 20th April ďan yazo duniya kuma sunan mahaifinsa aka sa masa, Ya Allah ka albarka ci junior Yunus kasa ma rayuwar sa albarka kasa mahaddacin littafin kane ka kare shi daga dukkan abinki, yan uwa ina barar addu'oin ku ga Uba da Ďa, Allah kayiwa Ya Yunus kyakkyawan sakamako ranar Kiyama Amin Ya Allah 😭*


Dedicated to my bastie one and only friend, my mentor, sister I really love you dear _Ummie Jafar_

@ Page Twenty_Four (24)

Kut ka mare ni, to wallahi zakayi dana sanin mari na, na faďa niba baiwar gidanku bace, ya kara zuba mata marin da yafi na karfon zafi yace

In har bakinki bazaiyi shuru ba nima hannuna bazai bar dukan ki ba kuma yanzun nan zaki fita kitchen ki dafawa matata abinci

Bazan dafa ba ko kashe ni zakayi bazan dafa ba

Honey ya nakejin hayaniya lafiya kuwa cewar Falie

Baby nida wannan jakar ce kuma in baki fita ba zan tattakaki ai daman na faďa miki zakiyi dana sanin zagina

Bana dana sanin zaginka inhar ka cigaba da zagina kuma bari na faďa muku daga kai har wancen abin (wato Falie ) babu wanda zan raga mawa acikin ku zanyi maka biyyaya ne kawai saboda niba jahila bace nasan hukuncin aure kuma bari kaji wallahi duk randa hannun ka ya kuskura ya kara taba jikina kaima sai kayi dana sanin duka na don akan waccen zan rama amma ku ruke wannan sai kun girbe abinda kuka shuka don wallahi nima ba tayar baya ce na ruga na birne hakuri na tun a kauyen mu, amma kai da kake matsayin mijina duk abinda kace nayi zanyi babu gadda ma a tsakanin mu saboda zamanka nakeyi amma banda waccen abin

Baby kanaji tana cemin waccen abin yanzu har kayi auren da a gaban ka matarka zata ringa cimin mutunci, tayi maganar kamar zatayi kuka

Ya matso kusa da ita yace haba sweetheart waye matata aini bani da wata mata saike kiyi hakuri kuma ta dinga ganin azaba kenan kala kala daga yau itace komai na gidan nan komai ina nufin komai da ya shafi cikin gidan nan amma bari kiji ban yarda ki leka kofar parlour ba balle kije ga farfajiyar gidan nan kin gane ai, yanzu ki fita zaki wanke min kaya na daga yau duk J'Cn da yan training dinmu suka sa kece mai wankewa babu sassauci a tsakanin mu zan tabbatar miki dake baiwar gidan muce

Zanyi koma meye ina nufin komai ka gane ai amma duk ranar da matar ka ta shigo gona na to wallahi baza ta fito ba sai ta girbe abinda taje cirewa gwarama kaja mata kunne niba baiwar gidan nan bace zaman aure ya kawo ni dole a kirani da matar gidan

Ke ki kama kanki niba sa'arki bace karki sake ki kawo min raini zan zaneki ne banza yar talakawa

Hhh zana Allah sarki ko zaki gwada ne, naji ni yar talaka ce kuma an bani tarbiyyar girmama bawa ba irinki ba da baki san darajar _DAN ADAM (Sis Rufaida Omar)_ ba kuma karkiyi gigin taba jiki na shima don miji nane kuma yayi na farko yayi na karshe ni ďin nan zan amsa yanci na a cikin gidan nan

Baby Don Allah zo mufita a ďakin nan don naga kamar ciwon hauka yana damun yarinyar nan

Amma baby kanajin abinda take faďa min baka ďau mataki ba ta fita tana kuka




_Kuyi hakuri nasan babu yawa wallahi na gajine da magriba na dawo kuma ga ruwa wannan ma nayi ne saboda bana son barinku shuru Nagode masoyan Shurakh, Shurakh tace na gaishe ku_





_{AGW}_

SHURAKH Where stories live. Discover now