SHURAKH

553 24 0
                                    

🏅🏅🏅🏅
🏅🏅🏅
🏅🏅
🏅


*_SHURAKH_*

_Daga alk'alamin 📝 jienie ďaya_

® _By_

_Sis Abeedah Tauhtah 😘_

*Da*

_Basira Sabo Nadabo 😘_

*_Anielurv Group Writes_* _{AGW}_ en _{ZWA}_


Wattpad @ Basira_Nadabo

_Alhaji Admin wallahi kai daban ne a duniyar mutane ban taba ganin irinka ba, ina gwanin wani ni Basira ga nawa kayi tasu har yau sun kasayin irin taka, gwani na kafi gwanayen maza, Allah ya kara basira yasa HAL'KAR BAN DARIYA ya shiga kasuwa a sa'a sai nazo amsan nawa copy ďin, Nagode Alhaji Admin Allah yabar so da kaunar mu har karshen rayuwa Amin Ya Allah_


*_Another dedication to you my durlin Aysher Habib Tall and my sweetat M'D Habib Tall, Habibullah Habib Tall My big brox Yaya Tiee Habib Tall Allah ya kara barin mu tare har karshen rayuwan mu Amin, My M'D Allah ya dawo da kai lafia. One lurv ❤_*



@ Page Thirty_Four (34)

Gafara dai matar gidan nan

Allah yayi mana aikin gafara a'ah yaya Farida ce a gidan mu da yamman nan shigo daga ciki ga tabarma zauna mana kina tsaye kamar ba gidan kiba don Allah zauna a kawo miki ruwan leda me sanyi kisha kin san na siya firiji nima zauna mana yaya Farida kinyi tsaye wallahi yanzu nadawo daga gidan malam tanko

A'ah basai na zauna ba ba zuwa nayi domin zama ba saboda banga gurin zama a gidan nan ba

Haba yaya Farida duk me yakawo haka kuma koma dai menene don Allah kiyi hakuri mu zauna sai muyi maganar da zamuyi amma dai kiyi hakuri mu zauna

Ke maryama nace ba zama nazoyi ba zuwa nayi naji inda kika samu kuďaďen da kike siyan kayan masarufin cen ta nuna da kartaceccen baki, yanzu maryama muna garin nan a ce mijin yarinyar nan ya kawo mana kuďi kiyi babakere akai amma muna gari ďaya ki kasa kawo mana muma musa albarka

Yanzu zuwa akayi akace miki mijin Shurakh ne ya bani kuďin da nake siyar da kayan nan haba yaya farida kiyi tunani mana akai ai inma shi ďinne bani zai kawowa ba ku zai kai mawa saboda tunda akayi auren nan ban taba sa mijin zainaba a idanuna ba amma kuma yanzu ace miki ya kawo min kuďi ki yarda kefa babba ce

Ke bafa tuni nazo kimin ba zuwa nayi akan ki bani kayan cen tunda babu kuďin kin cinye in tafi dasu don wallahi baki isa ba dole a raba kayan cen damu mune ai iyayen Shurakh don haka dolen dole ki bani kayan cen maryama cikin fada take magana kamar zata duke ta

Hehehehe kin gama nace kin gama to wallahi bari kiji babu uban da zai fitar da kayana a gidan nan da kike maganar kune iyaye au daman kune iyayen Shurakh aini ban sani ba sai yanzu da tun zuwanki kin kara tunatar da matsayi na kinga bazan manta ba duk abinda kuke min ina ďaga muku kafa ne saboda malam amma tunda kunce hakane za'ayi shikenan tun randa na haifi yarinyar nan kun taba siyo pant na naira goma kunce asa mata ko da sunan kun kawo a matsayinku na iyayenta ko kuma kun san yadda zainaba ta girma kun san cinmu balle shanmu ko ya muke bayar da kuďin haya, ko kuma kun san yadda yarinyar nan tayi karatun addininta har zuwa na zamani to bari kuji daman rage muku nakeyi saboda darajar zainaba to yanzu na kauda ita a gabana babu mai ďaga min yatsa wallahi ya mayar dashi lafiya ke farida daga ke har kanin ku sunusi babu wanda zai kara takani ya kwana lafiya yadda na kauda Shurakh haka na kauda kawaicin da nake muku babu ragi a tsakanin mu tunda baku da mutunci har yau baku san Annabi ya faku ba marasa imani wallahi farida kinci daraja yau kuma kije ki faďawa wanda ya aiko ki ke kinyi kadan dashi zanyi wawiya ya maidaki doki shi yana zaune kece mai mishi hidima, babu abinda ban sani ba wanda kuke kullawa amma ki sani watarana asirinku zai tonu ranar na damarku yana nan zuwa tare da tashin hankali kuma ki fata min agida tunda ba naki bane ki fita nace ko

(Tab lallai kuwa ni Basira har ta bani tsoro daman haka fushin masu hakuri yake tab an kure mai hakuri kuwa wai )

Tsum-tsum-tsum Inna Farida ta fita don naga maryama harda lakuce min hanci lallai maryama tayi kauri wato ni Farida takalla idona ta faďamin magana tab lallai maryama hmm a haka harta karasa gurin mai zaman jiran tsammani (wato mai gari ) tana zuwa ta fasa kuka sai da tayi mai isarta sannan tayi shuru ta zayyane wa mai gari yadda sukayi ta kara da cewa harda mari sannan ta hankaďoni waje

Wato mu maryama zata wulakanta ko to yanzu zan nuna mata karshen ta a cikin garin nan gidan da take takama dashi da har kika shiga ta hankaďo ki to baza ta sake zama a gidan ba kuma yanzu zan kawo karshen komai yanzun nan ba sai anjima ba bari na aika a kira min tanko ya amsa gidan a hannun ta harmu za'a nuwa gadarar gida, kai bala yaka, ya yafito bala da hannu (Bala kanin kawu ne ) bala ya karaso ya tsaya kikam akan mai gari babu ladabi balle tarbiyya

(hmm wasu mutanen sai a slow wai mutun sai ya dinga abu kamar shi yayi kanshi ji yadda mai gari yake magana kamar lamuran rayuwarsa da al'muran kauyen a hannun shi yake, kai Allah ya kyauta ya rabamu da duhun jahilci Amin )

Kai yane ina cikin abokai na zaka wani kirani da bala nifa na canza suna daga yau duk uban daya kirani bala Allah saina rabashi da ranshi kuma da yau sunana Falke don yanzu in farke cikin mutun ba karamin aiki na bane kagane ai dagus

Iye falke, falke fa kace to bala au yi hakuri falke don Allah ruga ka kira min tanko yi maza falken baba

Aha yanzu naji batu duk wanda yamin e yane kagane ai zan farke shi danma fa kaine kagane ai danma kaine zanje aiken nan inba haka ba babu uban da zai aike ni a kauyen nan kuma kagane dagus daga yau karka kara kirana a cikin abokaina in ba hakaba Allah zanyi maka eyane kagane, sai tura tsumma yakeyi a baki

Haka suka sake baki suna kallon shi wai yau abinda ake kawo mishi fada yayi hukunci a kai wai yau gashi a cikin gidana eh Farida

Kai dai ka sani duk yaranka haka suke babu tarbiyya nima yaushe yaushe kawu yazo har gidana ya gama wanke ni soso da sabulu kuma wai ina matsayin sirikarsa kuma yayar ubansa kanku dai akeji

Gafara dai mai gari mun wuni lafiya yanzu a kan hanya bala dan gurinka ya tareni yace kana nema inata addu'a Allah yasa dai lafiya

Tanko daman ba komai yasa na kiraka ba sai akan maganar gidan da maryama ke haya ne shine muka yanke shawara da yar uwata farida tunda kawu yayi aure tare da yar gurinta halimatu to muna son amfani da gidan ina son kaje ka fitar da maryama a gidan kuma ai daman jinginar sa na baka ina fatan ka fahimceni tanko

Yauwa tanko kamar yadda kaji daga bakin sunusi hakan muke so ya kasance kuma yanzu basai anjima ba

Malam tanko ya gyara zama tare da lankwashe kafa yace duk naji bayanin ku amma mai gari kamanta na kawo maka kuďin gidan har da ďoriyar dubu goma ni yanzu gida ba nawa bane yan zun nan na kaiwa masu gida takardun gida

"Ka siyar?" suka hada baki, waye ya siya don Allah kaimu gurin mutumin ko nawa ne zamu kara masa, wai menene dalilinka na siyar da gidan ba tare da sanina ba a matsayi na na mai gari yanzu dai tashi muje gurin wanda ya siya, wai waye ma ya siya gidan, duk cikin tashin hankali yake magana

Allah ya karamaka girma wato ďazu ina zaune bani dako sisi shine wannan baiwar Allah tazo min da maganar tana son ta siya gida to da mukayi ciniki naga ta kara min kashi tamanin a cikin ďari to kasanni da son kudi indai zan samu riba to zan siyar shine na siyar mata yan zuma daga gidan ta nake na bata komai na gidan yanzu ma gidan ya fita a hannu na ya zama nata Allah ya kara maka nasara

Wacce mata ce tashi muje gurinta ko nawane zan kara

Tashi muje Don Allah tanko sunusi tashi muje ai zama bai ganmu ba ku tashi mana

Ammm yallabai ku zauna ai duk karuwar kune ba wata bace illah maryama yar gidan malam mamman abokin mai gari mai rasuwa matar margayi usman yayan ka mahaifiyar Shurakh






_{AGW}_

_{ZWA}_

SHURAKH Where stories live. Discover now