SHURAKH

555 28 0
                                    

🏅🏅🏅🏅
🏅🏅🏅
🏅🏅
🏅

*_SHURAKH_*

_Daga alk'alamin 📝 jienie ďaya_

® _By_

_Sis Abeedah Tauhtah 😘_

*Da*

_Basira Sabo Nadabo 😘_

*_Anielurv Group Writes_* _{AGW}_


Wattpad @ Basira_Nadabo


Allah ya taimake ki a jarabawar da kike shirinyi Allah ya duba miki ya daukake ki kawata _Maryam Ameen Musa_ Amin Ya Allah

@ Page Twenty_Nine (29)

Ina komawa ďaki na faďa banďaki na wasa ruwa tare da alwalar la'asar ina fitowa naga mutun zaune a bakin gado na har yaso ya bani tsoro amma na dake tare da ďauko da darduma na fara sallah na idar na shafa addu'oina yana zaune inda yake sai dai duk inda nabi yana bina da ido na buďe sif na ciro kananun kaya masu kyau duk acikin wardrobe ďina suke a zuciyata nace _Oh Allah ka sakawa ummun da alkhairi ka kare ta daga dukkuan abin ki saboda nasan duk aikin tane wannan_ na shige banďaki don naga bashi da halamar fita daga ďakin na gama saka kayan na fito tun a banďakin nake ta jujjuya jikina saboda ni kaina nasan kayan sun min kyau, yau na ďauki niyyar zama a parlour duk abinda zai faru sai dai ya faru, ina fitowa muka haďa ido kamar daman yasan zan fito na harare shi tare da murguďa baki nace

Mallam meye na zuwa min ďaki ba tare da izini na ba kuma duk parlour mai isheka ba har sai ka shigo min cikin ďaki dame kazo kuma yanzu don nasan arziki bazai kawo ka gurin ďiyar talakawa ba me ya kawo ka

Me kike faďawa yaran cen eh daga zuwanki gidan nan har kin fara kai 'kara na gurin yan uwana so kike ki shiga tsakani na da yan uwana ko toko kinyi kaďan baki isaba wallahi bazaki rabani dasu ba kuma daga yau karki karawa Falie rashin kunya ta faďa min duk abinda kike mata ko kin manta matsayinki a gidan nan ne

Yako zanyi na manta bayan wanda ya ajiye ni ma bai manta ba, ina sane da matsayi na baiwar ka a matsayinka na mijina amma ba baiwar gidan kaba ina fatan kaima ka tuna matsayi na a gurinka

Ke ni kike faďawa magana a fakaice ni sa'an wasan kine

A'ah ya za'ayi ka zama sa'an wasa na koka manta ne nice fa Shurakh yar kauye yar talakawa wanda baka ďauke ta a bakin komai ba

Ke ya isheki haka inba so kike bakinki yayi jini ba

Tab jienie fa kace haba sai kace a film ai Shurakh ta daina ďaukar wannan dukan duk abinda zaka sani zanyi amma banda duka don wallahi ka daina duka na kum..... Wani razanar nan ihu mukaji da gudu muka fito har na rigashi fitowa naji daga ďakin Falie ihun yake fitowa da gudu na karasa cikin ďakin da gudu yana shigowa ya fara tambayar ta

"Falie me yafaru, me yasa meki?" eh kiyi magana mana cikin tsawa yake magana

Wayyo Allah baby mutuwa zanyi Allah kuwa mutuwa zanyi don Allah ka fitar min dashi baby wayyo daddy, mummy kuzo zan mutu wallahi na ganshi ya haumin kafa don Allah Adams ka fitar dashi ku taimaka min Shurakh ki taimake ni don Allah, kuka takeyi kamar wacce aka aikowa da sa'kon mutuwa

Wai me kika gani ne kina kara ruďani kiyi magana mana Falie kina sani a duhu fa Don Allah ki faďa min menene me kika gani meye ya hau miki kafa

Yana ciki ka shiga zaka gan shi wallahi katon kwaro ne a cikin bamďaki na Don Allah kafitar min dashi yana ciki Allah wayyo baby zan mutu inna kara ganin shi (a rayuwar Falie tana mugun tsoron kwaro (kyankyaso) koda kuwa karami ne bata son ganin abin koda kuwa a mace yake)

Kwaro kuma to shikenan yi shuru bari na fitar dashi Don Allah ki daina kukan ya'isa haka mana shima kamar zai tayata kuka, ya shiga banďaki ya kashe kwaron don karya dawo yasa a kwandon shara ya fitar dashi waje yaba Isah driver ya jefar a waje don karya kara dawowa

Ni abinma kamar drama ya zame min wallahi yanzu wannan katuwar ce take tsoron kyankyaso aiko a film ne nasan wannan wasa ne amma gashi ganin idona tab amma anyi katuwar kwabo naja tsaki na koma ďaki na dana san wannan abin takewa ihu bazan fito ba wallahi

Ya dawo ya fara aikin lallashi har tayi bacci

Ina zaune a ďakina na zabga uban tagumi yau watana uku kenan rabona da Ummata ko wake bata abincin da zata ci waye zai biya mata kuďin haya ko kuma mallam tanko ya kore ta a gidan oh Ya Allah ka kawo mana agaji a rayuwar mu duk halin da Abba na yake ciki duk inda yake Ya Allah ka bayyana mana shi in kuma mutuwa yayi Allah ka nuna mana wanda yasan inda aka birne shi Allah kasa Abba na yana raye Ya Allah ka nuna min Abba na ka amsa min addu'oina Ya Allah duk cikin kuka take magana sai da tayi kukan ta ya isheta zannan ta share hawayen ta, ta fita domin ďaura abincin dare a parlour ta tarda Adams da Falie suna kallo suna cin abincin da yayo musu a takeaway, tab aiko za'ayi ta a gidan nan nima ai matar gidan ce takeaway ďinda suka ajiye a kusa dasu shine na ďauka nima shi zanci saboda zaman shi nakeyi ai

Baby kana ganin ta ko kace ta dawo dashi nawa ne fa kuma a ciki aka min haďin da nake so please ta dawo dashi dear

Wallahi bazan dawo dashi ba shine zanci ba baby ba ko bomboi ne babu wanda zaisa nadawo dashi nima ai matar gidan ce hakkina na ďauka saboda bana son Allah ya kamaka da laifi ko bomboi

Abinda tayi yayi mugun bashi mamaki lallai yarinyar nan tanan kuma ta 'billo, yanzu za'a fara kuwa








_{AGW}_

SHURAKH Onde histórias criam vida. Descubra agora