SHURAKH

530 22 0
                                    

🏅🏅🏅🏅
🏅🏅🏅
🏅🏅
🏅

*_SHURAKH_*

_Daga alk'alamin 📝 jienie ďaya_

® _By_


_Sis Abeedah Tauhtah 😘_

*Da*

_Basira Sabo Nadabo 😘_

*_Anielurv Group Writes_* _{AGW}_

Ern

*_Zamani Writers Association_* _{ZWA}_


Wattpad @ Basira_Nadabo


Dedicated to _SKOLAK RESOURCES INFORMATION TECHNOLOGY CENTRE KADUNA_ my deep appreciation to Mr Ola Bunmi and also to my instructors; Sir Sunday, Sir Jerimaya and others to numerous to mention, for their support in ensuring that all that I need to be successful in life is provided. Thank you once again




@ Page Thirty_Seven (37)


Sai ta kara sumewa

Ba karamin tashin hankali Adams ya shiga ba

Malam isah ne yake ta mata fifita Baba mai gadi dai yana tsaye a rakube saboda yasan ba shiri yakeyi da yan gidan ba kuma yana tsoron yayi wani abun a mare shi da girman sa da furfuran sa

Falie ba karamin tashin hankali ta shiga ba ganin Shurakh ta kara sumewa sai kuka takeyi don ba karamin tausayi Shurakh ta bata ba, tama manta da abinda Adams yake fada saboda yanzu ba lokacin tunani bane

Baba mai gadi Don Allah ka karaso ku cece rayuwar ta Don Allah Baba

Abin sai yazo mishi banbarakwai wai namiji da sunan hajara wai yau shi Adams yake kira da baba tab cikin sanyi yake karasowa ya rasa me yasa gabanshi yake faďuwa gashi tunda ya shigo ďakin yakejin wani irin faďuwar gaba addu'a ne kawai yakeyi koma dai menene Allah ya kawo mishi shi cikin sauki

Ummata, Abba Don Allah kuzo zan mutu ga wutar tana matsowa umm.... Sai ta kara sumewa

Tunda ta fara magana Baba mai gadi yakejin wani iri wannan muryar dai ta maryama ce Allah mai hikima, da sauri ya karaso kusa da ita ya fara mata topi ko fiskarta bai kallah ba har dai cikin taimakon Allah ta farfaďo, tayi hamdala tare da kallan mutane dake ďakin a jikin Adams ta ganta tayi saurin tashi tare da cewa

Waya baka izinin taba jikina ko nima zaka min wulakancin daka saba yiwa Baba mai gadi ne

Don Allah zainaba kiyi hakuri yanzu ba lokacin tashin hankali bane kinga baki da lafiya ki tashi ki shiga ďaki ki ďauko mayafinki muje asibiti a dubaki

Bazani ba ai gwara na mutu wallahi kuma yau zan koma kauyen mu tunda daman zaman wahala nakeyi

Sai da Adams ya ambaci sunan Zainaba sannan ya juyo yana kallon ta tunda ta fara magana yake kallon ta tabbas wannan dai 'yarsa ce zainaba to me ya kawo ta kaduna kuma gidan da yake gadi ya kara maimaita sunan ashe a fili yace Zainaba

Da sauri ta juyo tana kallan sa gashi dai kammanin su ďaya to a ina tasan shi tayi nisa a tunani cen ta tashi da gudu ta shige ďakin ta

Sudai yan ďaki kallon su kawai sukeyi Baba mai gadi ma yayi shuru kome yake tunawa oho

Cen ta fito da gudu da hoto a hannun ta sai faman kiran Abba takeyi da gudu ta karasa gurin shi ta faďa jikin shi tana wani irin kuka mai tsuma zuciya shima kukan yakeyi tare da dariya yana rike da hoton a hannun sa yana kallo yana kara maimaita wannan addu'an da mutun zai faďa idan wani al'amari yazo masa na farin ciki sai yace

_Alhamdulillahil-ladhi bini'imatihi tatimmus-salihat__

(Godiya ta tabbata ga Allah wanda saboda ni'imarsa ce kyawawan ayyuka suke ciki)

Tace Abba na kaine a ina kake muke ta nemanka nida Ummata munsha wahalan rayuwa saboda rashin ka Abbana Don Allah kace baza ka kara tafiya ka barmu ba Abba ta kara fashewa da kuka

A'ah babu inda zani Zainaba ina tare dake nadawo kanwata bazan tafi ba kuma wancen ma kaddara ce kuyi hakuri ki daina kukan nan kar yasa miki ciwon kai

Abbana ina kaje ka barmu to Don Allah Abba a ina kake muke ta cin talaucin mu Abba Ummata tana cen cikin kuncin rayuwa kazo muje ka ganta Abba duk cikin kuka take magana

Yi shuru mana gani nadawo gare ku babu inda zani kiyi shuru mana

To nayi shuru Abba na daina kukan

Assalamu Alaikum, Aunty Shurakh gamu munz ..... Maganar ya kasa fitowa saboda ganin Shurakh a jikin Baba mai gadi kuma ga mutanan ďakin duk sunyi cirko cirko Adams sai gumi yakeyi duk da ac dake ďakin, feedie me yake faruwa a gidan nan wai

Kinji ki nie'nie da wani magana tare muka shigo fa kuma kina tambaya ta mu kara ciki mana sai muji koma meye, suka kara kusa da malam isah suke tambayan shi abinda yake faru, ya kwashe duk abinda ya faru ya faďa musu

Daman wallahi nasan a runa kullun in zan faďa miki sai kice na cika surutu yanzu ma a hanyar zuwa gidan nan me nace miki ki kula da Aunty Shurakh zakiga kamanin da takeyi da baba mai gadi kika ce ke baki iya sa ido ba ai gashi nan

Abba na a ina kake zaune duk wannan daďewar ina kake kullun sai nayi mafarkin ka Abba Don Allah ka faďa min inda kake da zama

Zainaba ai muna tare dake a cikin gidan nan ni ban sani ba kema baki sani ba

Abba gidan nan kuma to a ina kuma baka taba shigowa gurina ba

Haba Shurakh ya akayi nasan kina gidan nan balle nazo, aida na sani da tuntuni nazo gurinki ďiya ta


Ai nine mai sai wayar shi ta fara kukan neman agaji

Kirjin Adams ya bada wani sauti haďe da kugi a cikin sa

Yana dubawa yaga ashe flashing akayi masa yace

Ai nine mai gadin gidan nan

Adams jin maganar yayi kamar an soke shi da kibiya a kahon zuciya

Kaine Baba mai gadin gidan nan Abba?






_{AGW}_

_{ZWA}_

SHURAKH Where stories live. Discover now