SHURAKH

541 21 0
                                    

🏅🏅🏅🏅
              🏅🏅🏅
                       🏅🏅
                                🏅

              *_SHURAKH_*

_Daga alk'alamin 📝 jienie daya_

®  _By_

      _Sis Abeedah Tauhtah 😘_

             *Da*

        _Basira Sabo Nadabo 😘_

© *_Anielurv Group Writes_*  _{AGW}_

In Dedicated to the best and most important person that I love to the button of my heart I love you so much Nurul Qalb, Habibty _Aunt Faty Izland_ ICNDWU Aunt ur A'B love's you much 😘

HML In Advance Sis _Deborah Nnaka Bulus_ thanks for your love and support we really do appreciate thanks once again _Mrs. Bro Samson Loh Dele Niya_ to be, Matar Oga lol

@ Page Twelve (12)

Baba na da tunda kaka ya fara magana in banda hawaye babu abinda yakeyi har saida kaka yace ya tashi ya tafi sannan ya tashi yana share hawaye idonshi har ya kun bura fuskar shi yayi jaa abinka da farin mutun, harya fita ya dawo gaban kaka ya tsugguna shi bai ce komai ba kuma bai tashi ba hawaye ne kawai ke zuba kamar ruwan dutse in ya buďe baki zayyi magana sai kuka ya sarke shi sai da yayi mai isarsa sannan ya ce Ala'raini Don Allah kamin aikin gafara nasan ni mai laifi ne a gurinka ka yafe min dattijo

Usmanu na yafe maka sauran ma duk na yafe musu kuma in banda abinka manu baka 'taba min komai ba harta kai ga nayi fushi da kai Allah yayi mana aikin gafara gaba ďayan mu Don duk kanmu masu laifi ne a gaban Allah fatana a koda yaushe in Ubangiji na ya kirani na amsa mishi ba tare da hakkin kowa a kaina ba amma don tsakani na da Ubangiji na wannan mai sauki ne domin Allahu Gafurur Rahiem ne Allah mai Rahama ne, Allah ya haďa mu da Rahamar sa Amin Ya Allah

Baba na yace Amin,  ya tashi ya fita

A gefen Baba Sunusi kuma cen na hango su tare da waziri suna kus kus kamar zasu koma cikin juna baba Sunusi sai share zufa yakeyi saboda tsabar tashin hankali komu da muke dauko muku rahoto bamu san me suke kullawa ba wani mugun dariyar sune ya dawo damu daga duniyar tunanin da muka tsunduma saboda bamu san me zamu cewa mai karatu ba in suka tambaye mu, kome suke tseguntawa oho lokaci ne kawai zai bamu amsa kudai ku cigaba da binmu

*Kulli Nafsin Za'ikatul Maut*

Hakika dukkan mai rai mamaci ne mutuwa rigar kowa duk wanda yasa saiya cire da misalin karfe 2:30pm ne Allah ya asma aron ran daya bawa Malam Aliyu Mai Garin kauyen marafa  kaka na lokacin babu kowa a gida duk sun tafi masallaci sallar jumma'a bayan an idar ne Baba na yazo domin yayi ma kaka alwala yayi sallah yaji jikin kaka sanyi fuskar shi a sake kamar mai murmushi,  Baba na ya dudduba shi ya kara tabbatar da ya tafi babu dawowa Baba na ya tafi taga taga kamar zai faďi salati da duk addu'an da yazo bakin shi ya keyi ya fito ya shiga gida ďakin Inna Aisha ya tadda ta a zaune ta zabga uban tagumi tun ďazu kirjinta yake bugawa kamar zai tsage kuma ta rasa dalilin bugawar

Baba na ya nemi guri a gefenta ya zauna ya fara mata nasiha kana daga baya ya faďa mata rasuwar kaka

_kun san mutuwa ba yaro ba ba tsoho ba kowaye saiya taba shi balle mutuwar miji,  Allah yasa mu cika da kyau da imani Amin Ya Allah_

Kirjinta ne taji ya mata dauyi idonta yayi jaa tana sonyin kuka amma ta kasa ga zuciyarta na mata k'una kun san auren tun saurayi da budurwa akwai zafi

Baba na ya fita ya faďawa waziri rasuwar mai gari, tuni rasuwar kaka Aliyu ya baza ko ina a marafa da kotar kauyen marafa irin su kauyen malali da anguwar rimi mutuna sun cika kamar me tuni aka mishi sutura aka kaishi gidan shi na asali mutuwar kaka Aliyu ya taba matan kauyen marafa domin shine cin su shine shan su sannan shine suturan su in yau akayi haihuwa a marafa shine kewa yaron hak'ik'a yayi wa mai jego kayan fitar suna shine ke sasanta su da mazajen su in wani abun ya faru tsakanin ma'auratan,  sunyi kuka kamar me....

_Yan Uwa kuzo muyi gangami muje kauyen marafa ta'aziyyar rasuwar mai gari kaka Aliyu_

_Drop ur ta'aziyya here_

_4 ur Comment only 07030515774_

_{AGW}_

SHURAKH Where stories live. Discover now