SHURAKH

900 44 0
                                    



*Dedicated to our Habibty, Swt lurv, Swthrt, Durlin Ayusha Iliasu Musa, we are really do appreciate for ur  lurv and support, lurv U dear 😘

10-8-2017

Page Three (3)

"To Ummata na tafi."
           Ina fita gidan su rukiee na shiga.

" Assalamu Alaikum!!! , Ah lafiya ina ta sallama shuru kodai mutanen gidan basu tashi daga bacci bane amma bari na leƙa ɗakin rukiee yanzu haka tana nan tana sana'ar da ta ɗaurawa kanta."
      Ina shiga ɗakin kuwa na ganta kwance ɗa ka mata duka na yi sannan na ce

"Ke wallahi ban san wacce irin mutum ba ce tun daga kofar gida nake sallama amma bakiji ba wataƙila da barawo ne har zai gama satar komai na gidan har da ke baki sani ba kina kan littafin hausa, nasan ko aikin da Malam Nura ya bayar ba ki yi ba anjima duk ki isheni da aramin Shurakh kafin Malam yazo don Allah!"
       Na faɗa tare da kwaikwayon muryan rukiee.

"Kuma ba badawa zanyi ba ehe."

"Haba ƙawalli romon jaɓa kin san ni da ke babu mai jin kanmu wallahi littafin ne in ban karanta ba ji nake kamar mara lafiya amma in ina karantawa har wani nishadi nakeji amma ki yi hakuri ƙawata."

"To nidai ba wan nan ya kawo ni ba zuwa na yi ki ran tan min naira goma sha biyar (15) in kina da shi."
       Rukiee ta bata rai har sai da gabana ya fadi ta ce.

"Shurakh wallahi ba za ki taɓa canjawa ba yanzu don girman Allah naira sha biyar (15) ne zan baki aron sa duk ƙawancen mu na rasa abinda zan ranta miki sai sha biyar (15) ni wallahi baki taɓa ɓata min rai irin na yau ba haba Shurakh me amfanin abotar mu? Na daɗe ina rokon Allah ya kawo min wannan ranar da kina cikin matsalar da zan iya taimaka miki,  na rasa gane ke wata irin yarinya ce Shurakh in abinci na kawo muci sai ki ce kin koshi Shurakh mun zama daya fa, ki daina boye min damuwar ki ko kin manta da Hadisin Manzon Allah (SAW) da ya ce

       "Allah ya yi alkwarin zai sa wanda suka yi abota don Allah a ƙarƙaashin inuwar Ar'arshi. Don Allah Shurakh mu zama wannan abokan da Annabi (SAW) ya faɗa ina neman alfarmar hakan don Allah Shurakh."
         Rukiee ta haɗa hannunta biyu tana rokon Shurakh, sauke ajiyar zuciya ta yi.

"Rukiee bawai bana sonki bane wallahi nima ina son mu zama wannan abokan kawai bana son sabawa kaina ne da buɗe sirrin cikina, gwara na tauna na haɗiye babu wanda ya sani,  Rukiee ko kudin makarantar da Abbanki ya ɗauke mana ya'isa mu yi muku godiya kuma darajarki nake ci kin san Abbanki baya son ganinmu tare,  yanzu dai mubar maganar nan bani kuɗin kafin Malam Tanko ya je gidanmu kuma nace wa Ummata zan kai masa kuɗin hayar sane."
          Rukiee ta yi saurin cewa.

"To muje na rakaki kafin Abba ya tashi."

"A'a bani kawai na tafi ai zan dawo Ummata ta aikoni gurin umminki."

"To ga shi ki rike sauran canjin ko koko da kosai ne ki siyawa ummanmu."
           Ta miko min tare da dunkule hannunta,  na amsa tare da godiya ta ce.

"Don Allah karki buɗe har sai kin fita kuma bana bukatar godiyarki."
       Na amsa domin burina ta bani kuɗin kafin Malam Tanko ya rigani zuwa gida.

"In ummi ta tashi ki ce ta haɗa min kayan wankin inna dawo zanzo na amsa."
       Ina faɗar haka na yi saurin fita ko sallamar da Rukiee take min ban ji ba, ina fita na hango Malam Tanko ya shanyo kwanar gidanmu da gudu na karasa gurin shi da ganin fuskar shi babu imani, ko gaisuwar da nake masa bai amsa ba ya ce.

"Ke Don butar gidanku jira kike nazo na amsa kuɗin ne ko? To gani nazo bani kuɗina wallahi ko naira biyar (5) ne yayi ciwon kai ba amsa zan yi ba yau dai kam sai dai wasu amma baku ba,  don kun samu na barku a gidan kuke zaune a ciki kuma wallahi badan inajin kunyar mai gari ba da tuntuni na koreku na saka wasu har riba na samu akan gidan nan amma mai gari ya hanani siyarwa,  muje zuwa watarana sai nayi fatali da kayan gidan saboda gida dai nawa ne amma ana nuna min fin karfi wallahi nakusa kwace gidana."
       Duk cikin masifa yake magana.

           ( Uhmmm na ce ka ce gidan duniya bana lahira bane Ya Allah duk wani wanda yake gidan haya ka hore masa nashi ko ya huta da matsalar gidan haya, in ɗan taɓa rera muku waƙar gidan haya, Baban Gida Kaka Dawa ya ce gidan nan ba gida ba ne matsala daine zaman haya, Allah dai ya kyauta Amin Ya Allah )


        Ku yi hakuri labarin ne ya zo a hakan gajeren feji ne da shi.

Basira Sabo Nadabo Ce.

SHURAKH Where stories live. Discover now