SHURAKH

556 24 0
                                    

🏅🏅🏅🏅
🏅🏅🏅
🏅🏅
🏅

*_SHURAKH_*

_Daga alk'alamin 📝 jienie ďaya_

® _By_

_Sis Abeedah Tauhtah 😘_

*Da*

_Basira Sabo Nadabo 😘_

*_Anielurv Group Writes_* _{AGW}_
_{ZWA }_

Wattpad @ Basira_Nadabo


_Alhaji Admin A'Y Indabo, A'Y Indabo, A'Y Indabo wallahi harna rasa bakin magana domin kai na daman ne ko acikin mutane har yau banga irinka ba Allah dai yabar mu tare har karshen rayuwa Amin_

Dedicated to my self Basira Sabo Nadabo



@ Page Thirty_Five (35)

Ehye tanko kasan abinda kake fada kuwa kodai kayi mantuwa ne maryaman ce kodai maryamar baba waziri ne ah sunusi inaga subutar baki yayi yace maryamar manu ce

Kai tanko kalle ni nan wacece ta siya gidana

Yallabai ai gida ba naka bane gida nawa ne ai tuni na kawo maka kuďin gidan, gida kuma ya zama nawa kuma maryama matar usman maman zainaba itace ta siya gidan nan

Ehhe malam tanko kana hauka ne suwaye manya a garin nan da har zakayi abu kai tsaye batare da sanin mu ba shikenan sunusi maryama ta gama damu babu sauran wani hanya mai billewa shikenan ta fashe da kuka

Wato kai tanko sai yau nasan ashe kaima shugaban kanka ne ni dai bani da amfani a garin nan da har zaka siyar da gidan ka batare da sani na ba ko kinga farida kiyi shuru akwai hanya inta san wata bata san wata ba damu take zancen mu zuba muda ita shege ka fasa, kai kuma ka jiraye ni zan dawo gare ka badai ni kayiwa haka ba to shikenan tashi ka tafi zamu haďu ai dani kake zance jeka kawai tanko, kuma har kabata takardu ba tare da sanin mu ba

Yallab.....

Yi mun shuru tanko ni ka watsawa kasa a ido ba Baba sunusi ya katse shi

Shikenan na barku lafiya, malam tanko ya tashi don bin umurnin su

Yanzu ya zamuyi bamu da sauran wani hanyar musgunawa maryama gashi Shurakh tayi mana nisa balle mu huce a kanta kuma farid.....

Dallah malam yimin shuru har kana da bakin yimin magana yanzu gidan da muka bada jingina shine ka lallaba ta baya ka siyar dashi ba tare da sani na ba kuma tare da kai muka kulle shine ka warware a bayan idona ko sunusi aika kyauta, kayiwa Shurakh auren gata ni kuma kasa tawa 'yar ta mutu a wahala to tun wuri kasa ďanka ya sako min yarinya tun muna mu biyu to wallahi bari kaji duk abinda kake kullawa na sani da yake kai butulune mai manta alheri kaida waziri kukayi kutunswilar ku sai da kukayi kuka san yadda kuka kore usman daga garin nan ka hau mulki gashi tun hawarka baka kara waiwayar wazirin ba ni don kamin ai bazai dameni ba amma sunusi ka sani duk wanda yaci tuwo dani miya yasha kuma In Shaaa Allah duk wani mugun nufinku akan usman saina bi na warware su yanzu da usman ďin ne kan mulki bazai bari mu wulakanta ba wallahi

Amma yaya Farida ba haka ban.....

Rufe min baki yau ne nazama yayarka baka da bakin magana wallahi sunusi sai kayi kuka da idanunka wallahi sunusi sai kayi dana sanin cin amanata da kayi da farida kake zancen mu zuba ni dai kaje yamma ni kuma gabas nayi muga mai cin riba, ta shure takalmin ta tana tafe tana masifa kamar sabon kamu

Mai gari da tunda inna farida ta fara sababi baice komai ba sai zufa yakeyi kamar wanda ya haďiye kwaďo, hmm lallai na ďibo ruwan dafa kaina don kuwa nafi kowa sanin halin farida tunda tace zatayi to fa zata aikata kuma inna bari usman ya dawo garin nan bokan cikin bukka yace muna haďa ido koni na mutu ko waziri ko kuma wanin mu ya haukace kawai bari naje na bata hakuri, tab inbata hakuri kai ina'ina bazan bata ba taje tayi duk abinda zatayi kuma ni nasan wannan yarinyar Shurakh ba zaman lafiya takeyi ba to dan me zan tada hankalina taje tayi duk abinda zatayi, ya karkaďe malun malun ďinshi ya shige gida

Inna Farida tana tashi a gurin mai gari wani bukka naga tashiga nima da gudu na kara ina daga waje ina leken su gaban wani babban malami ta zauna agaban shi daga ganin malamin kaga malamin daya jiku da son Annabi babu shirka a tattare dashi kuma amini ga mahaifinta mai gari mai rasuwa, tace

Allah gafarta malam wato mai gari ne sunusi sukayi wa usman asiri yabar garin nan tun 'yar shi zainaba tana ciki wata uku kuma har yakawo yau bai taba zuwa gida ba balle ya tuna damu ya dawo ga iyalan sa sannan ya ďauki 'yar usmanu yabawa wani wanda bamu sani ba har yau itama bamu kara ganin taba nima kaina me laifi ce saboda dani ake musguna musu to yanzu na tuba nabi Allah

Yayi gyaran murya yace wato farida duk abinda kukeyi na zuba muku idone ina kallon ku amma tunda kin dawo hanya babu abinda zai gagare Allah nima dashi na dogora kuma In Shaaa Allah zamu dage da addu'a In Shaaa Allah komai zai dai dai ta In Shaaa Allah kema ki cigaba da addu'a Allah zai bamu sa'a In Shaaa Allah

To Allah ya yarda nima sai yanzu na gane hanya ta fashe da kuka

SubhanAllah ba kuka zakiyi ba godiya ga Allah ya kamata kiyi saboda yana sonki da rahama cikin hikima da ikon sa ya baki daman gane hanya Allah yasa mudace tashi kitafi ki daina kuka farida

To natafi sai anjima

Umman Shurakh sana'a ya amshe ta don har zuwa ake ana saran masara, gero, maiwa, shinkafar gwari, wake, waken system, kai harda tank ďin kalanzir ana zuwa saran jarka jarka abin gwanin sha'awa masu raďe raďin cewa da kudin data siyar da Shurakh ne take sana'a sai gashi gunta suke zuwa kaban bashi, wasu basussukan ma sai dai a kiyama don sunci sun hana kuma bashi ya hanata cigaban ssana'an ba ,sai dai muce umman Shurakh Allah ya kara dafa mana (a rayuwan mu na yanzu rayuwar tayi tsada sai dai godiya ga Allah kuma kar muce komai ya same mu muce shuwagabannin mune suka samu a'ah komai ya faru daga Allah ne babu wanda zai maka abinda Allah bai maka ba, kundai ga yadda umman Shurakh take damawa a dalilin hakuri da rayuwa da duk yadda yazo mata, Allah dai yasa mudace Amin Ya Allah )

Yayin da malam yake ta addu'a haka komai yake warwarewa a hankali

*KADUNA*

Baba mai gadi ne yake zaune da Al'qur'ani a hannun sa yana karanta suratul bakara dai dai lokacin da yake karanta aya ta 255-256 yaji kanshi yana juyawa addu'oi kawai yakeyi har kan ya fara lafa masa sai ya fara karanta wannan addu'ar maganin damuwa da bakin ciki ga addu'an kamar haka

_Allahumma innii abduk, ibnu abdik, ibnu amatik, naasiyatii biyadik, madin fiyya hukmuk, adlun fiyya qada-uk, as-aluka bikulli ismin huwa lak, sammaytaa bihi nafsak, aw anzaltahu fii kitabik, aw allamatahu ahadan min khalqik awis-ta'dharta bihi fii'ilmil ghaybi'indak, an ttaj'alal Qurana rabii'a qalbii, wanuura sadrii, wajala huznii wazahaba hammii_

*Da hausa kamar kace*
_Ya Allah! Ni bawanka ne, kuma ďan bawanka, kuma ďan baiwarka. Makwarkwaďata a hannunka take hukuncinka zartacii ne a kaina, kuma 'kaddararka gare ni mai adalci ce, ina rok'an ka da ko wanne suna naka wanda ka ambaci kanka dashi, ko ka saukar da shi a cikin littafinka, ko ka sanar dashi ga wani daga halittarka, ko ka kebance kanka da saninsa a cikin ilimin fake dake warin ka. Da ka sanya Al'qur'ani ya zama kaga zuciyata, haske da kirjina, da kwaranyewa ga bakin cikina, da kuma tafiyar da damuwa ta_

(wannan addu'an sadaka ce ga duk kan al'ummah Allah yasa ladan yaje kabarin iyaye na tare da al'umman Annabi Muhammad (S, A, W ) Amin Ya Allah )





_{AGW}_

_{ZWA}_

SHURAKH Where stories live. Discover now