CHAPTER 3

1K 136 23
                                    

Isan sa fada sallama ya bude makokoro tare da sanar wa cewa yarima ya iso fada. Shiga yayi ya tarar yan uwansa maza duka uku sun hallara.  Yarima Kabir da yarima jabir sai yarima karami wato munir mahaifiyan su daya yayinda shi mahaifiyar sa daban.

Yarima farouq Dan amaryar sarki ne kuma tana haifansa ta koma ga mahaliccin ta. Hakan yasa mahaifiyar su kabir wato sarauniya hafsa ita ce ta raine sa tare da jabir Wanda ya bashi kwana 3 kacal.

A takaice de yarima shine Dan sarki na 3 amma kuma shine zai gaji sarki hakan yasa har yau ake tirka tirka a masarautar. Wuri ya samu ya zauna tare da fadin barka da hutawa abba. Tashi sarkin yayi yace barka de asad kaide baka canja hali yau kuma mai ya sa ka jinkiri?

Dan Sosa kai yayi amma bai murmusa ba saboda yan ubansa dake zaune a wajen yace mai martaba kenan ban farga da lokaci bane. Sarki yace kaide fadi gaskiya Dan timati (wato fatima), yake nufi haka yake kiran mahaifiyar umar domin tana yarinya ya aure ta, duk soyaiyar su a tsokana da wasa ta kare.

Ba ruwan ta da fadanci , matan sarki ce amma zata biyo kaza ayi ta tsere, ko fadawa sunyi kokarin kamo Mata tace bata so. Har sai taji ba siga tukun take yarda su kamo. Shiyasa kowa ya so ta Dan indai tana guri dole kayi farin ciki ko baka so. Timatin sarki kenan, sarauniyar murmushi

Murmushi ne ya sufcewa yarima jin sunan da sarki ya Kira shi da shi saide kash. Ko mutum maye ne bazai gane murmushi yayi ba. Kai ka dauka Abu ne zai fada masa ido ya Dan kane hakan yasa kumatun sa motsawa.

Sarki yace tunda kowa ya hallara sai mu karasa fili ko? Yarima ne ya fara fita tare da tsayawa a bakin kofa yana mai kallon bishiya. Ko da yarima  kabir ya fito wani kallo ya watsa masa kamin ya tsaya a gefensa, haka ma yarima jabir din. Yarima Munir kuwa bai ma wani damu ba Dan yasan bazai ma samu ba yana da yayi uku ai saide ikon Allah.

Shi yasa shi bai dauki mulkin a bakin komai ba koda ya fito ma gyadan sa yake ci abin sa ya tsaya a gefen yarima ta hagu sabanin biyun da suka jeru a dama. Taba hannun yarima yayi ba tare da yarima farouq din ya kalleshi ba yace "uhm" irin ya aka yi?

Yarima munir yace Dan uwa zaka koya min wannan zilliyar da kake yi da doki in mun gama wannan yakin? Yarima umar yace yaki kuma ? Matsowa kusa da kunnan sa munir din yayi yace kai baka taba lura cewa su kabir ba'a wasa suka dauka ba? Da badan idon sarki ba da tuni sun.... yayi masa sautin an kashe mutum.

Yarima Umar yace bana son gulma. Kawai Dan ba ma shiri ba yana nufin zasu kasheni bane, me yasa kake son koyan zilliyar ya karashe zance yana mai juyowa tare da aika masa kallon tuhuma. Sosa kai yayi yana Dan dariya yace so Nike dama gobe, gobe da yamma.

Dauke idonsa yayi daga kan munir din yace in bazaka fada min ba ka ga tafiya ta. Da sauri ya riko hannun shi yace haba mana Dan uwa jinin jiki, wangale baki yayi yace zance fa zanje. Karo na farko da sukayi magana me tsayi da yarima farouq kenan.

Biye masa yarima yayi cikin Muryan rada yace kai ne zaka je zancen ko zaka raka yayan ka? Kasa kasa munir yace ni ne mana wata yarinya ce ta min amma bansan yadda zan fadawa mai martaba ba. Gashi wanna shekaran tana cikin kuyangun da za'a kawo ka dai gane me nake nufi.

Umar Yace toh idan sarki ya zabeta fa? Munir yace kamin ayi zabe zance ina so. Tabe baki abduljalal yayi yace shekarunka nawa ne ma?munir yace 19 abduljalal yace na sani ai. Munir yace toh menene na tamabaya?

Daidai lokacin dawakan su suka iso Dan haka suka fara yin gaba kamin mai Martaba ya je shi.
Isowan mai martaba yasa aka fara za'a hada kowa da sakon sa ne. Duk Wanda yaci sai shima yayi da dayan duk Wanda yaci shikenan.

Farko kabir da jabir ne sukayi fada yayi fada kabir yaga jabir zai ci sa hakan yasa yayi masa alama da ya fadi ya bar mai. Haka kuwa jabir din ya fadi akace kabir ne zai kara da na gaba. Umar da munir ma sukayi ana farawa Munir ya fita da gudu ba dogarai ba hatta sarki sanda abin ya bashi dariya. Shi Dama kullum yana cikin kawo dalilai da zaisa bazai yi ba.

Wani zubin yace ciwon ciki yake ko sai yaga saura kwana uku ko biyu sai ya tsiri tafiyar karya. Wannan karan ma sanda yaga ran sarkin ya baci ne yasa ya zauna.
Fadawa ne suka cacumo shi aka dawo da shi ba Dan yaso ba suka fara fadan,  farouq ya barsa ya ci. Bakin sa har kunne ranan da ya zauna a waje ko cikin bayi ko dogarai toh fa fariyar sa shine ya ci yarima Umar Farouk a wasan wuka (swordsmanship).

....

Washe gari da sassafe kamar kullum yarinyar ta tashi ta zauna tare da yin mika firgita tayi lokacin da ta bude idanunta taga idanuwa masu tarin yawa kowa ya tsira Mata su.

Mikewa tayi da sauri ta kalli zul, zul yace yau kinyi lattin tashi har hantsi yayi (8:00am) da sauri ta sauka daga kan katifar ta na ganye Wanda kullum in ya bushe maimakon a fitar sai a libga wani ganyen a kai yanzu har ya zama gado.

Fita tayi da gudu tana riko riganta Wanda a bakin gari ta dauka irin Wanda ba'a so ta har hada ya zama kaya sai mayafinta. Ita a dole technology yazo Mata domin a baya fala fala ganye take sutura da su.

Da sauri ta rufe baki cikin mamaki tace toh ya akayi haka? Zul yace dama yunwa ke tashin ki, Mu din ma haka amma ina ganin kamar in an dafa abinci yafi kama cikin kuma yafi yawa. Shewa kowa yayi suma sun samu cigaba sun gano wani Ilimi.

Hankaka yace yau kowa in ya fita Abu mai dadi zai samo yau kayan itatuwa kawai za'a ci. Saboda an samu sabon Ilimi dole ayi biki da farin ciki kowa na jin wannan ya bazama ya kama hanya itama wanka tayi cikin teku sannan ta shirya kamar kullum ta shiga cikin gari.

Yau Allah ya sa ta biyo ta wajen masu saida dankalin hausa aikuwa sum sum ta dauka tayi gaba kuma ba Wanda ya kalleta. A kan hanya ta tsinci madubi amma a kife yake kawai sai ta dauka tana wasa da shi ya yanke ta. Ko a jikin ta taci gaba da yawo jinin na disa.
Tare da yin sauri ta zura madubin a jaka.

Bayan ta koma gida ne ta ciro madubin sai taga yana nuna hotan Abu sake laluman jakanta take yi tana nazarin yadda akayi wannan abin ya shiga jakanta.

Juya shi tayi sai taga ai abin fuskokin sa ba iri daya bane. Kallon madubin tayi taga mutum a ciki da sauri ta washe baki tare da daga hannu tana tunanin shikenan tayi kawa Wanda ake iya gani a cikin abun kuma yana da kaifi Dan haka zata dinga yanka Abu da shi.

Bangaren yarima kuwa...........

SHIN KUNA SON MUNIR? YANA DA ABIN DARIYA? A GYARA ZAMA FA DAN YARIMA YA KUSA YIN ARTABUS DA MUTUNIYAR KU.

DONT FORGET TO VOTE AND SHARE!

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CEWhere stories live. Discover now