CHAPTER 52

311 79 10
                                    

Washe gari ko sa munira ta tashi ba kowa a dakin da sauri ta diro daga gadon tayi asuba kamin mai martaba ya dawo ya tarar da ita saide har rana ya bullo bata ganshi ba.

Wata dattijuwa ce ta shigo suka gaisa da munira tace bangaren da mai martaba yasa aka hada mata an kammala idan.taci abinci ta yi wanka za'a kaita can.

Nan de munira ta hanzarta ta bar wannan kaddararren wajen sanda ta tashi tafiya ne ta lura da yanda aka kwata shi da abubuwan auduga ko ina ka taba laushi amma ba ta wannan take yi ba...

Tana isowa ta samu asma da gimbiyar kabir suna jiranta. Runguman juna sukayi kamin suka shiga ciki.
...

Haka ko akayi washe gari da la'asar yarima ya fara bi daya bayan daya harda kai musu kyautukan rigan sanyi wanda alkayi da al hariri da fata.

Yana zuwa bangaren munira ya same su su uku suna yar carafke munira tana basu labarin sabon ilimin da yarima ya koya mata. Nana tace gaskiya kinji dadin ki. Asma ne tace ai wallahi mijin ki de Allah  wadai da badon darajar me martaba ba da mun samu 'kadi(mai shari'a) ya raba auren nan.

Munira tace nana ta me zai hana ki saita sa yanda kike so? Nana tace kamar ya? Munira tace kinsan shi namiji kamar yaro ne. Yanda ka masa tarbiya haka zai taso in baka nuna masa abinda baka so ba ya saba da yi sanda kake son ya dena ba zai dena ba.

Asma ne ta kama baki tace iye munira wannan ilimi daga ina haka ? Munira tace ni ban magana da gauraye dariya nana tayi tace kuma kin kawo shawara asma tace ji min su ko yaushe ma suka yi aure har zasu kirani gauruwa oho.

Dariya munira tayi tace haba tawa kema kinsan wasa muke miki ai shi ilimin zama da mutane wani zubin koyan sa kake yi ba sai an koya maka ba.

Asma tace nan de kin fini gaskiya ana cikin haka ne yarima ya shigo yana mai sallama. Ko wacce suturta jikin ta tayi banda munira da ta mike murmushi ne ya kewaye fuskan ta amma fuskar yarima ba sauyi.

Jikin ta ne yayi sanyi a tunanin ta ko yayi fushi ne da ita sai de ta lura yana kallon bayin dake gefen ta da sauri ta sallami kowa dake haraban asma ne taja hannun nana suka bar wajen. Munira na ganin haka da gudu ta ja yarima zuwa sabon dakin ta suna shiga ta rungume shi tana me shirin yin kuka ajiyan zuciya yayi ganin sun je tudun mun tsira.... well not really.

Ya shafa kanta tare da fadin ya kika kwana jiya tace ba dadi. Yace duk kaushin gadon abba na? Tace ai baka nan kuma ba a dakin ya kwana ba. Yarima yace anya kuwa maganar ki gaskuya ne yanda naga kina murmushi ya fada cikin tsokana.

Mintsinin shi tayi tace toh ba dan kazo bane yasa nake murmushin? Yace wasa nake miki ai kar aga na dade bari nayi abinda ya kawo ni duba kasan gado yayi ya bude wani hanya suka bi hanyar yaga ta bullo dasu bayan fada yace toh naga ta inda zan dinga shigowa idan kika ji an kwankwasa kasar gadon ki nine?

Suna komawa dakinta ta kasan kasa yake fada mata haka dama yasan ko kasan gado ko jikin gini anan ake yin kofofin sirrin. Dariya munira tayi tace sai kace fatakin dare? Amma me yasa baka so na fada masa gaskiya yace abin da ya kawo ni kenan.

Mahaifina yana matukar son mahaifiya ta kuma kina kama da ita sosai wanda hakan ke da abin mamaki. Kuma duk soyaiyar da yake mata yana kokarin daura miki dan haka so nake ki dinga saba mata ta ko ina kar kiyi wani abu da take yi. 

Abindq basu sani ba shine khadija mahaifiyar  munira da kuma fatima yan uwan ne ko ince wa da kanwa ne lokacin da aka ci masarautar su da yaki ne aka rabasu bayan an kashe iyayen su inda sarki ya siyo fatima sanda yayi badda kama  ya fito yawon zaga gari yayin da aka bawa baban munira khadija wanda take kanwa.

Kewan juna ya saka gaba dayan su basu da kwakkwaran lafiya ga kulli da ake musu safe da yamma har sanda aka kaisu lahira. Bayan mai martaba ya siya  fatima da wajen shekara 8 ne aka bawa sarki kyautan fatima daga wani masarauta. Kuma fatima bata haihu da wuri ba hakan ya taimaka sosai wajen ratan shekarun dake tsakanin munira da yarima.

Mai martaba kuwa abinda ya hana shi kwana a dakin da munira take shine yana tsoran wani abu ya shiga tsakani take tayi ciki ta mutu irin yanda fatims ta rasu.

Dukda yasan mutuwa daga Allah ne amma de haka kawai yaji a ransa idan ba ya zama dole ba bayason munira ta haihu saide in ita take so. Dan a tunawan sa babu abin da fatim ake tsoro kaman haihuwa kuma abinda ya kashe ta kenan. Saide fa baisan me munira da yarima suka shirya masa ba.

don't forget to VOTE

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

miss untichlobanty 💕

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CEWhere stories live. Discover now