CHAPTER 44

657 108 58
                                    

sisin gwal guda yarima ya bawa mutanen nan wanda sun zo ne daga wani kauye ya dale dokin sa dan shi a doki yazo yace wa munira kama ni tace na'am haniya dokin sa tayi saboda jan linzamin da yayi ba shiri munira ta damke shi suka fita a guje cikin ruwa iska yana cika musu kofan hanci.

Suna sukuwa iska me mugun sanyi yana dukan su yarima yace kina jin sanyi tace ka manta ni mutum ne? In nace bana ji ma ai kasan karya nake yi murmushi yayi kawai ya girgiza kai wai a kalli idonshi guda a masa bakar magana. A kusa da fada sukayi karo da su munir sun gama shirya amalanke me runfa zasu tafi dauko su da fadawa hudu da aliyu ko kallon su yarima baiyi ba dariyan dake fuskarsa ma ta dauke dan a hanya sai hiran shirme munira take masa.

Wani gumi ne ya karyowa munir dukda ruwa ake sanda yaji saukar ta😂 aliyu ne zai bi bayan su yarima dan komawa fada munir yace in kanaspn kanka ka rufa wa kankan asiri mu labe anan har a gama ruwa zuwa lokacin ya sauko. Daga yin abin arziki aliyu yace laifinka ne ai.

Su yarima kuwa suna isa an riga an bude musu kofa dan haka ya shige karkashin bishiya ya tsayar da dokin nasa sauka yayi ya mikawa munira hannu alamun zai taimaka mata ta sauka make hannun tayi ta diro ana ta lura da zoben sa tace yau baka sauke ni a waje ba yace haka ake godiya a garin ku? Ko haka ake yiwa shugaba magana ba ladabi. Cikin gatse kamar da gaske tace afuwa nake nema shugaba na. Dungure mata kai yayi tace ruku daure rai yayi yace ismi umar ba ba ruku ba tace ko ma menene inga zoben hannun ka. Yace me yasa? Tace ban taba ganin irinshi bane shine nake son gani.

Cirowa yayi ya daura a tafin hannunsa alamun bazai bata ta rike ba. Tace gashi me kyua wa ya baka? Yace nima ban sani ba na kasa tunawa amma gani nake ba bani akayi ba tace amma ya kake ganin alakarka da zoben ? Yace nakan ji kamar akwai wani abu mai mahimmanci da zoben amma na mance. Warcewa tayi da sauri ta fita da gudu tana fadin in ka tuna alakarku kazo na baka. Cikin daga murya yace ke ki dawo ki bani abina tace anki din ganin da gaske take yasa ya bita da gudu yana tunanin yanda mura zaiyi masa rashin mutunci anjima.

Binta yake yana fadin ki dawo nace zansa a miki bulala dariya take tana fadin ba sai ka iya kamani ba tukun. Haka suka dinga kewaya filin daga karshe ya zauna yana haki da mamakin yanda har yanzu munira kamar ba gudu tayi ba in aka ce a maimaita a shirye take.

mika masa zoben tayi tace gashi ya hada harda hannunta ya zaunar da ita kallon ta yayi sosai da alaman da gaske yake yace wacece ke kuma me yasa dabban nan ya taimaka? Wani ras taji dabmn bata san wani amsa zata bashi ba. Wacece ita? Yarinyar daji me jin maganan dabbobi ? Ko munira yar sarkin garin banty? Ko ku kuwa laila me yanci? Ko kuma laila baiwa? Ko wani lokaci in ta bide baki zata yi magana sai ta rasa wani amsa zata bayar abu daya da ta iya cewa shine sunan shi zul.

Yarima yace wa ? Tace dilan kar kace masa dabba. Shiru yayi kamin ya riko dayan hannun ta ya sake cewa wacece ke ? A hankali ta zare hannayen ta ta kalleshi a karo na karshe kamin ta ruga da gudu ta shiga bangaren sa sannan ta nufi sashin bayi inda dakin su yake.

Mikewa yarima yayi shima ya nufi sashin nasa dan ruwa ya ragu yana tafiya ba tare da ya kalli wajen  bishiyan da aliyu yake boye ba yace ka fito ina da magana da kai sannan ya shige ciki. Aliyu yana shiga yace shugaba kayi haku.... daga masa hannun yarima yayi yace na rage rabin albashin ka na watan nan. Da sauri aliyu ya rungume shi yace godiya nake shugaba na wallahi na dauka bulala zaka saka ayi min har na fara tunanin yanda zan rayu ba tare da na zauna na wasu kwanaki ba.

Aliyu yace kaje ka bangaren bayi ka isar da umar nina cewa............. aliyu yace angama kamin ya tafi bangaren bayi hansai yasa ta sanar kowa ya fito cikin isa hansai tayi hakan suka hau layi aliyu yace ba sai kunyi layi ba ina laila? Matsowa gaba tayi yace kwaso kayanki yau bazaki kwana a daki ba..... hansai tace maganin wasu kenan an taba yarima yaude sauro sun samu nama Allah ya kawo ruwan dare ma.
Aliyu ne ya daka mata tsawa yace wa munira dake rike da kullin ta da bargon kauna.(😂 kai jama'a ban ma san ya akayi nasa ma bargon suna ba)

Yace daga yau bazaki sake kwana a cikin su ba yarima yace na sanar kowa ya sani dakin can shine bangaren ki kuma kece shugaban duka bayi mata har hansai. A takaice matsayi na da ke daya. Hansai tace mene? Munira tace amma dakin mutane ashirin yamin tsayi aliyu yace ai ba a daki kadai za'a bar miki shi ba har wajen karban baki (parlour) za'a miki raba shi za'a yi. Shiru tayi wani abu yana cewa kar ta karba ganin fuskan hansai yasa tace na yarda.

Aliyu yace ko baki yarda ba ma ai umarni ne dole abi duk wanda ya nemi jawo hasuma da yarima yakeyi ya fada yana kallon hansai da kumatunta kamar ya fashe dan takaici. Yace yanzu za'a raba miki shi a saka komai. Tace dare baiyi ba? Yace sa'a daya ma ya ishe su suyi. Kowa ya koma daki maza zasu shigo.

Haka ko akayi ba'a bata lokaci ba sai ga bangaren munira ras dashi. Da daddare  bayan kowa ya kwanta ita daya sai safa da marwa take yi tana rike da warwaron ta tana shawaran ta fada wa yarima ko kar ta fada yayin da yarima kuwa ya kwanta amma sai juye juye yake yi yana tuna abinda ya faru yau ya manta rabon yaushe yayi dariya kamar yau mikewa yayi ya saka kayan sa sannan ya fita aliyu zai biyo shi yace masa kar ya damu yaje yayi bacci sannan ya nufi bangaren munira. 

Kwankwasa kofar yayi tace waye ya share ta sake fadin waye tayi amma shiru dan haka ta lalumo wukan ta ta  rike tana budewa yayi saurin rike hannun tare da daukota yaje ya ajiyeta a bakin gado. Komawa yayi ya rufe kofa kamin ya dawo ya zauna a gefen ta.......

😂NAJI COMMENT KO A JINI SHIRU TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕
 

DEDICATED TO hadizayakubu3, fatymahmusa

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CENơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ