CHAPTER 30

496 101 30
                                    

Gaishe sa asma tayi kamin suka ajiye kayan da suka kawo sannan suka fito su ukun suka a tare. Gyaran murya yarima yayi tare da miko hannun sa ta bayan labulen da ya raba parlourn sa da wajen wankan sa juyowa munira tayi kamin ta tsaya a take saboda zamewa da takalmin ta yayi daga kafar ta ( kun dauka ta gane hannun yarima ne? Kaniyar bai kai nan ba😛)

Sukayi tana ajiyar zuciya ganin de har yanzu bata hadu da yarima ba saide kuma bata eo ta tambayi asma akan yarima zata zargi wani Abu. Ban garen saurauniya suka nufa maman su kabir jabir da munir uwar gidan sarki kuma mai martaba abduljalal Mata mai makirci kissa da sanin ilimin iblisanci a lokacin da zata dinga yi maka wani murmushi me tafiya da zuciya ta kashe ka ba tare da an ga laifinka ba. Ta cutar da kai ta hanyar yi maka kirki da abin arziki. Ta talauta ka ta hanyar baka dukiya sannan tasa barayi su sace harda naka sannan a kashe ka sarauniya kulu kenan don kuwa gimbiya hauwa me sunan ta ne.

Tun daga bakin kofa asma ta fahimci cewa wani matsala ya faru ganin yanda ake shiga da fice cikin sassarfa. Suma daga kafa sukayi suka shiga. Wani dogon kaya ne ya makale a makokoron  sarauniya kulu anti duk wani dabara da za'a sa ya wuce ko ya dawo Abu yaci tura hasali ma ko da masu magani suka zo sun fahimci cewa kayar ya shige jikin makokoron ta ne tsoron su daya kar ya huda wani waje ya hana ta magana ana cikin wannan tsima ne fa su muniran suka zo Dan kuwa a karo na farko sarauniya hauwa ta fahimci abinda ake cewa "da ido na naga mutuwa" masu magani da ilimin lafiya dake aiki a fadan dukan su uku sun kene suna shawarar yadda za'ayi amma ba mafita sa guda daya asa Abu ta makokoron a zaro kayan amma tsoron su idan suka je suka riko wani Abu na daban fa sukayi ma sarauniya illa su ja wa kansu abin da yafi karfin.

Idon kowa ya raina fata numfashin sarauniya ya fara shidewa. Nazari munira take ta gwada ko kuwa domin maman laila yana da ilimin kiwon lafiya dan haka yasa ta koya wa laila amma tunda munira da tazo tace misu ta manta komai ga lokaci ya kure sai aka duba aka ga wasu abubuwa ne zata bukata a rayuwa kuma akwai yuwuwar ta shiga wannan yanayin sai ta koya mata a ciki harda idan mutum ya kasa numfashi saide ita damuwar ta wannan ba haka kawai ta kasa numfashi ba akwai abu a makokwaron ta ne.

Shahadar guda tayi domin kuwa a rashin tayi akan bar arha baki na rawa tace ku bani allura (warning: kar a gwada abinda zatayi yanzu a gida na maimata a kiyaye) kallon ta kowa yayi irin wacece wannan masu magani ma sun kasa komai sai ke? Toh amma ganin basu da zabi yasa suka mika mata wani lalume lalume tayi a wuyan kamin ta hadiyiyi wani yawu gumi na karyi mata ta saisaici wani waje ta soka. Kafewa aka ga sarauniya tayi bata motsa ko ina banda idon ta dukda ba jikin ta bane ya ya shanye.

Kunsan irin yanayin da mutum ke shiga idan ya hadu da wani abu da ya girgiza sa? Toh haka sarauniya ta kafe ta daina kakarin da take yi. Bulala munira ta karba a hannun wani dogari ta tsulawa sarauniya wani lafiyaiyar tsimagiya. Kowa bude baki yayi suna masu zare idanu masu kama baki nayi tabbas basu taba ganin mara tsoro da ya isa ya daki sarauniya ba ko a tatsuniya basu taba ji ba tabba wannan baiwa ta ballowa kanta abun da yafi karfin ta.

Ihu sarauniya tasa saboda yadda bulalan ya shige ta a kuwa sai gashi ya dawo ashe ba kaya bane kashi ne. Zare siririyar alluran munira tayi yayin da sarauniya taja wani dogon numfashi tana mai rike wuyan ta. Wannan dabara dai gadon gidan maman su laila ne ba wanda yake da ilimin abin sai su. Hakan yasa ba wanda ya taba sanin sa.

Shiru kake ji malam ba me magana kowa yana jira a hankali sarauniya kulu ta dago idon ta ja. Jakadiyar ta ta kalla da ido ta mata alamun tazo ta kaita cikin daki. Ji munira tayi kamar an hautsina kayan cikin ta. Don kuwa ba irin abinda yakai wannan sa mutum cikin garari har gara ka sani idan ma fishi ake da kai ko kuwa. In ma kawhe ka za'a yi ka dai sani ka san me ke tafe ba abarka yan hanjin ka suna sarkewa ba.

Jakadiyar ce ta fito.bayan.ta kai sarauniya kulu tace ki.jira sakamakon ki. Da sauri asma ta ajiye daurin kayan sarauniya har tana hardewa ta ja hannun munira suka fice daga wajen.

Koda suka koma nana suka tarar tana saka rigunan sanyi domin kuwa sanyi ya gabato kamr yadda kuka ji a baya ana ta kera rigunan sanyi da takalman fata domin su taimaka wajen jin dumi kuma nana tana daya daga cikin wanda suka iya saka. Domin kuwa ba wani aiki da  bayin gidan dan masani basu iya ba a fadan shi saboda tsaro badan tsoro ba.

Ko dare tayi an zuba musu abinci suna ci lokacin an raba wa su mhnira da nana da sauran matan da ba'a zaba ba kayan su na masu aiki. Saide kuma idan har an saka ki a cikin wanda za'a zaba koda ba'a zabe ki ba toh kinfi baiwa wacce kwata kwata ba'a kaita ba matsayi. Dan haka kayan da aka basu yasha ban ban da nasu asma. Kuma suma a bayin ko wani daki akwai shugaban sa wanda asma itace shigaban dakin da take hakan na nufin idan wani abu ya faru ita zata je ta fadawa shugaban bayi ko wata bata da lafiya sannan ita zata rufe kofan dakin su. Anyi haka ne saboda bayi masu zaran jiki da hujjan shan ruwa ko karban magani ko wani abu suna zuwa suna haduwa da fadawa masu gadi suna alfasha tare.

Don haka in kana bukata daga an shiga kwanciya toh fa shugaban daki ne kadai zata fita. Munira da nana ma dakin asma aka kaisu da nana ta lura da kamar wani abu ma damun munira ita kuwa damuwar munira daya kar a kashe ta bata hadu da minin ta ba gaskiya. Hakan yasa ta yanke shawara idan kashe ta za'a zata nemi alfarmar taga yarima ko sallama ne suyi.

Ita kam daga taimako shikenan sai abu ya zama masifa ? Nana ne tace uwar....ai laila kallon ta munira tayi lokacin da take kai loma baki domin abin ci suke ci nana tace me ya sameki ne yau naga kamar gaba daya bakya fadar nan dukuda kina tare da mu. Ajiyan zuciya munira tayi asma ta fada wa nana me ya faru sanda aka bada labari duk ta kidime kai kace itace tayi abin idon ta kamar zai fado. Tace uwar daki ya zaki yi? Asma tace uwar daki ? Ban gane ba tsuru tsuru dukan su biyu sukayi.

NIKAM KILA KAWAI NA AJIYE BOOK DINNAN NAGA KO DAN COMMENT MA YANGAR SA AKE MIN DUK YADDA NAKE TAKURA KAINA BANIDA LOKACI DA RANA MA AMMA IN DARE YAYI SAI NA SAMU LOKACI IYA KOKARI NA NAYI TYPING 💔 SHIKENAN AI YANZU YAN KADAN DINKU NE MA SUKE COMMENT

YAU BAZAN CE TAKUCE DIN BA MA, YAU KARAMARSU BABBARSU NE KAWAI😔

Miss untichlobanty

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CEWhere stories live. Discover now