CHAPTER 36

427 86 20
                                    

Sanda ta gama magana ne yarima munir ya saki baki yace manzon allah yayi gaskiya da yace mu dinga saka mata a harkokin mu kar mu ware su ashe de kwakwalwar ki sabuwa ce. Tace toh yanzu ina muka nufa yace kasuwa.

Kasuwa suka tafi munira ta zauna a gefe tunda ita mace ne yarima munir ya tara mutane ya fada musu gasan ai kuwa sunji dadi kamin kace me gaba daya gari an hada halka halka da majalisai mai sayan kaya na kokarin ya fi wanda yake siya a wajen shi dan ya larbi warakar sa shima dayan bangaren haka wajajen faduwan rana sun tara dubu 10 cif cif. Wanda yarima munir shine na dubu goman saka ta sukayi a jakukkunan fata suka boye saboda gusun irin abin jiya wanda har yanzu basu ma fadawa yarima umar ba.

Guda 1500 munira ta rike a hannun ta yayin da 8100 ke hannun munir ga kuma 400 dake gida a kan waraka. Sauti suke sosai dan bai wuce sa'a daya rana ta fadi ba kuma daga rana ta fadi shikenan. Suna cikin tafiya mutanen yarima kabir suka zo wai a nuna musu imda suka boye warakar ido yarima munir yayi wa munira cewa tayi gaba yayin da ya dauke hankalin mutanen.

Ihun barayi yayi musu hakan yasa suka hanzarta suka gudu dan kar ya bata musu suna ko yarima kabir ya samu labarin abinda sukayi. Isowa zuwa ga yarima umar munir yayi tare da bashi jaka cike da himilin warakoki. Bayan an lissafa kaf aliyu yace ba guda 1500.

Yarima umar ne ya kalli munir hakan ya saka shi sosai kai kadan yana dan yake yace yaya sauran kanwata zata taho dashi ya kamata ace ta iso ma bansan me ya tsayar da ita ba. Kallon sa yarima yayi da kyau yace munir ban san cewa kana bukatan magani ba ai. Ya za'a yi kabar abu mai mahimmanci irin wannan a wajen wacce manifar ta a kan mu ma bamu sani ba. Bamu san inda ta dosa ko daga ina ta fito ba. Hatta shugaban ta bamu sani ba a gidan nan domin kuwa ban yarda kabir ne uban dakin ta ba.

Ali ne ya shigo da sauri munir yace ta iso ko ? Jinjina kai ali yayi yana haki munir yace dama nasan zata zo. Aliyu yace yarima kabir ne ya iso. Murmushin dake fuskan su ne ya dauke wanda dama can yarima baya yi.

Da fara'a yarima kabir ya shigo yana fadin yarima maji dadi ina littafin da aka rubuta sunayen mu fara irgawa ko? Murmushi yarima umar yayi a nitse dukda kuwa gaban sa yana tsinkewa yace ai saboda kaunar da suke min kowa da hannun sa ya rubuta suka tara mana.
Murmushi yarima kabir yayi yace hakan ma na da kyau yanzu tare da kallon bafaden sa yace bismillah fara mana qirge.

Munira kuwa tazo shiga bangaren yarima fadawa suka tare ta da takubba domin sun tuna yanda aka sa suka cilla ta kurkuku kamar yadda ake cilla kaza a akwaki yanzu kuma tace tana da muhimman ci ga yarima saboda abinda ke wajen ta hakan bai kwanta musu ba. Ta rokesu ta rokesu har ta gaji hakan yasa ta yafa da sauri tare da cewa la ku ga al-huda huda na furewa da sauri suka kalli sama ita kuwa kafa me na ci ban baki ba ai ta ari na jaki kawai ta bankada zuwa bangaren yarima ta nufi sashin sa tunda a bangaren kowa akwai sashin sa akwai na bayi da masu aikin sa.

Da goma goma ya lissafa bayan ya gama yace babu 1500 yarima kabir yace dan uwa yana mai kallon yarima umar har yanzu akwai rabin sa'a kamin rana ya fadi tunda naga al'umma na son ka sosai zasu hado maka 1500 din kamin fadu....

Bai karashe maganar sa ba saboda munira da ta shigo tare da cewa na iso na iso guda dubu daya da dari biyar sai de kash gudun da ta shigo dashi yasa iskan hijabin ta ya kwashi waraka guda daya ba tsaya ko ina ba sai cikin kofin shayi. A kan idan su ya narke yarima kabir yace har yanzu de da alama babu guda daya.

Da sauri munira tace akwai yarima kabir yace na wa? Har munir ya saka nasa shi kuma dan uwa mai jiran gado ba zai iya sa nasa ba don kuwa dama kowa yasan zai zabi kanshi ne. Munira tace nawa mana ko ni ba yar daular nan bace? Hade rai yayi yace toh ai shikenan dan uwa... ya kalli yarima umar yace kasha sai mun hadu a gaba sannan ya tattara tawagar sa suka fita.

Suna fita yarima ya kalli munira yace me kika tsaya yi baki kawo da wuri ba bayan kin riga munir tahowa? Bude baki tayi zatayi magana yace yimin shiru kamin nasa..... munir ne yayi saurin janshi waje cikin muryan koradi yace yayaaaa kar mu yi haka dakai.

Munira kuwa cewa tayi ji min mutumin nan ka tamabaye ni dalilin bata lokaci na zanyi bayani kace nayi shiru ko ma me kake boye wa ai sai ka fada min ni matar ka ne kuma umma (tana.nufin maman laila) tace bai dace ma aurata su dinga boye wa juna abu ba.

NOTE maman laila tayi mata nasihan nan ne sanda zata zo fada saboda suna sa ran sarki ya zabe ta.

Yarima munir kuwa kallon yarima farouq yayi yace yaya kamata fa yayi ka bawa kanwata kyautan ban girma domin kuwa ita ta taimaka aka tara ma sa hannun al'umma ni nan da kyar na tara maka 2000 yarima yace me yasa zata taimaka? Munir yace haka de tace duk abinda yake da magimman ci a wajen ka itama yana da mahimman ci a wajen ta.

Yanzu de kar ka mata tsawa ni zanje inyi wanka kace ina mata ban gajiya da godiya yana kaiwa nan ya balli wani fure dake gefe make masa kai yarima yayi yace banason zalinci baka san suma suna da rai ba. Dariya munir yayi yace a haka de ake cinye su a kwano in sun zama tuwo yarima yace abinci daban munir yace ai suma shuka ne yarima yace amma su anyi su ne dan aci munir yace fure kuma dan ayi ado a sanyaya zuciya da kawata idanu.

Da gudu ya fita ganin yarima na kokarin jifan shi da takalmi. Shiru yarima yayi a ramsa yace kanir me kake kullawa ? Menene halakar ka da yarinyar nan? So kake ta kashe ni ko yar leken asirin ka ce. Daga alamu dai kana son yarinyar dan haka ya kamata na jefi tsuntsu biyu da dutse daya kuma masu jan kunne na fadin keep your friends close and your enemies closer.

Mayar da yarinyar nan kuyanga na zanyi hakan zai sa bazaka samu daman samun ta ba kuma zan ajiye ta a kusa dani duk da bazan bari kowa ya sani ba sai shugaban ta idan kuma kaine shugaban ta toh sai in sanar da mai martaba. Itama kuma zanga me ta kullo me kuma take nema. Kofan dakin shi ya kalla yace YARINYA DAGA YAU KINA KARKASHIN SHUGABANCIN YARIMA UMAR ABDULJALAL.

MASU YI MIN COMMENTS INA GANIN KU KUMA INA JIN DADI RASHIN SAMUN LOKACI YASA BANA IYA MUKU REPLY AMMA KUCI GABA DA YIN MIN COMMENTS INSHA ALLAH ZAN DIGA LURA DA MASU YIN SHARHI INA MUSU KYAUTAN CHAPTER.

ALLAH YA BAR KAUNA TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CEWhere stories live. Discover now