CHAPTER 12

656 100 7
                                    

Yace shikenan sai su tafi da ke ba ni kuma...... kofar da aka turo yasa suka jiyo lokaci daya suka zaro ido naman da ke hannun munira ma sanda ya fadi.

Ajiyan zuciya yarima ya sauke yayin da munira ta turo baki sadiya kuwa ta fashe da dariya tace kai matsoraciya. Toh nice munira cikin shirin kuka tace harkinsa na fara tunanin adadin bulalain da za'a yi min ashe ma kece ni na dauka fa dogarai ne me yasa kika saka wannan kayan?

Sadiya tace kina ganin in suka ganni zasu bari na shigo ne? Kuma ko sun barni na shigo AI za'a zargi wani Abu shiyasa na saka rigar dogarai. Zama tayi tace ba Dadewa zanyi ba maman ki ne wai tayi kewarki shine tace na zo na duba ki.

Nan de sadiya ta bawa munira abinci sannan ta sake saka rawani da babban rigan ta rike hannun munira tayi tace muje yarima yace ina zaki kaita? Tace a cikin dakin nan akwai daki karami a kasa ko wani bangare akwai irinsa a dakin mai bangaren anyi shi ne saboda ko da yaki ya balle iyalan mai martaba zasu iya buya.

Boye ta tayi sannan tace kar ta dinga yawan zuwa wajen yarima saboda shi namiji ne. Munira tace toh me yasa ba ina zuwa wajen ya Adam ba ma? Dungure Mata kai sadiya tayi tace ni matsala na da ke bakida wayo.....

Idan kina zuwa kusa da shi AI dogarai zasu ji kamshin ki a jikin sa. Zaro ido munira tayi tace da gaske? Sadiya ta daga kai. Munira tace toh ba sai yayi wanka ba? Tsaki sadiya tayi tare da cewa shinshini jiki na, shinshina muniran tayi sadiya tace yayai kama da kamshin maman ki ko mai martaba? Munira ta girgiza kai sadiya tace toh haka shima yarima idan kamshin ki ya hau jikin sa ko yayi wanka sai anji.

Cikin jinjina kai munira tace dama haka abin yake ? Shiyasa duk sanda muke wasan buya kike gano inda nake ko? Toh nima yanzu na San kamshin ki kuma sai na gane kamshin kowa a gidan nan. Sadiya tace toh yanzu dai kinji me nace ko? Banda fita banda barna sannan karki damu yarima gadon sa yana ta saman ki kinji? Munira ta daga kai.

Sasiya tace toh ni na tafi munira tace toh amma zaki zo gobe ko? Sadiya tace ya dangana ga duwatsu na kawo miki ki dinga yin yar carafke ga tsolan rake ki hada yar tsana ki Mata kitso idan kin gaji ki leka kuyi hira da yarima kamar yadda nace kar kije wajena kar ki bari ya shigo mabuyan ki. Sake jinjina kai munira tayi alamun ta fahimta ficewa sadiya tayi.

Tana tafe tayi karo da kuyangan marka, kaf gidan ba annamimiya irin ta Dan haka tana ganin sadiya ta soma waka a haiye wasu de anji kunya, abin nema bai samu ba, na farko ya bace Wanda bai zo ba ma zai koma. Zaman mu gidan nan dole su o'o dole ayi gaba.  Ita duniya dama haka take ta kasa ma Zuma ta karbe In kaga ta lasa ma dayawa toh kofar ragoo tayi maka. A haiye wasu an kusa kada su zama da mu sai an shirya. Ko shedan dole girmama Dan yasan mun fishi.

Sadiya dauke kai tayi kamar bata ji ta ba ita kuwa jakadiyar marka ganin sadiya bata kulata ba yasa ta mangaje ta har sanda ta fadi taji ciwo, dadin abin tayi dabara tana fitowa bangaren yarima ta buya a lungun da ta sanya babban rigan ta tube shi tare da boyewa dan haka ba Wanda ya gani.

Akan idon jakadiyar sarauniya jakadiyar marka ta mangaji sadiya jakadiyar khadija Dan haka ta hanzarta ta sanar da sarauniya AI ga can fada ya barke tsakanin jakadiyoyin gida biyu. Nan fa take sarauniya ta ce a Kira mata su.

Bayan an kawo su tasa a Nemo mata me magani mai magani dai koda aka nemoshi zuciyar sa yankewa take tana faduwa Dan kuwa ba abinda yafi tashin hankali ace wani jinin Sarauta konme hadi da me sarauta ya mutu a hannun ka. Yanzu yanzu baka ji ba baka gani ba kuma an San mutuwa a hannun Allah take amma sai a kawar da kai.

Jin mace ce yasa matar sa Wanda ta Dan San ilimin magani amma tafi kwarewa a karban haihuwa tace bari take ta duba Dan ita ke duba Mata. Bayan ta duba hannun sadiya inda ta fa fadi taga ashe targade tayi Dan haka tayi Mata dauri.

Gurfanar da su sarauniya tayi tace me ya faru shiru sadiya tayi Dan tasan jakadiyar marka munafuka ce amma yau ta sha alwashi zata nuna Mata ba su kadai ne suka iya hada guri ba Dan haka jakadiyar marka wato TANI tace ranki shi Dade ni fa kawai ina tafe domin karbo sakon uwar daki na shine naga sadiya nake Mata jaje shikenan sai cewa tayi wai mi muka sace gimbiya munira shine ta sheke ni ni kuma garin an kare kaina na hankade ta ta fadi.

Sarauniya tace haka ne sadiya? Sadiya tace Allah ya kara nisan Kwana nima ina tafe bayan na kwaso kayan wanki uwar daki na sai ga tani jaje tayi min nayi Mata godiya zanci gaba da tafiya bansan kaya ya zazzago ba sai na take bakin anan ne ya kada ni amma ba ita taji min ciwo ba. Tana kokarin taimakawa ta daga ni domin ta kaini bangaren su yayin da ba kafe Dan nasan zasu iya kashe ni idan naje anan ne aka ganmu.

Da sauri tani tace sarauniya karya take me tayi mana da zamu kashe ta. A ranta kuwa fadi take ban taba ganin mara wayo kamar sadiyan nan ba. Itama sadiya kamar ta jita tace ban taba sanin abin ansu wayo ba hankali bane sai yau. Sadiya tace wallahi gani nake zasu lashe ni Dan sun kashe nayi dayawa kuma naji tani tana cewa yau bayan naji ciwon nan zata kashe ni kuma ko uwar dakin ta bata sani ba.

Da sauri tani tace karya kike da sanin uwar daki na kuma bata ce in kashe ki ba cewa tayi na tabbata na fidda miki jini duk inda na ganki.... da sauri ta rufe baki bayan ta ankare da subul da bakan da tayi saide kash magana tanandaya daga cikin Abu uku da da ba a iya maida su baya wato lokaci, magana da kuma mutunci. Sarauniya tace wa jakadiya a Nemo mata takwabi yayin da ta kalli tami tace SAI ME KUMA KUKA AIKATA KE DA UWAR DAKIN TAKI?

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU GASKIYA NAGODE SOSAI DA ADDU'AR KU DAN ALHAMDULILLAH NAJI SAUKI SOSAI INSHA ALLAH NA DAWO DUKDA KUWA NA KOMA MAKARANTA ZANYI KOKARI IN DINGA SAMBADO MUKU UPDATE

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CETempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang