CHAPTER 27

497 83 18
                                    

Makwanci aka basu bayan an duba lafiyan su kowa na zumudi da kuma tsoran aje ba'a zabe su ba. Zamu iya cewa banda munira a cikin masu zumudi Dan kuwa ita gobe aniyar da ta daura shine ta tafi neman yarima. Yaya zatayi hakan ? Allah shine masani. Da wannan tunani bacci ya daukesu.

Tsul kamar an mintsine ta ta bude ido tare da zama dan dama bacci bai dauke ta ba. A ranta tace toh an saka bata shiga ba AI Dan kuwa kamin dai na samu daman fara neman mijina za'ayi zanen in aka zageni kuwa lokacin kowa zai sanni tashin hankali.

A hanakali ta Mike cikin sanda ta bude kofar dakin da suke ta shiga daki na gaba domin dakuna dayawa ne a wannan bangaren Dan ko wace baiwa anan suke saide Wanda suke da iyayen daki toh bangaren iyayen dakin su za'a Gina musu dakunan su.

Kuma taga dakin da shigabannin bayin suke shiga Dan haka tasan wanne ne nasu. Shugabannin bayin de sune bayin da suka Dade a gidan ba tare da sun nuna suna son yin aure ba balle a yanta su ko a hada su aure da wani bawa. Dan haka daga sunyi shekara 40 toh sai a yanta su sannan a basu matsayin shugaba shima kuma shugabancin matsayi matsayi ne.

Sannan kuma akan saka musu wani albashi haka tunda an yanta su. Wanda aka zaba Dan akaiwa sarki ya zaba dakin su daban sannan akan Abu me laushi kamar katifa zasu kwanta yayin da bayi kuwa Wanda ba'a zaba ba kawai shinfida za'a yi musu a hakan ma an karama su sosai da ba a kasa suke kwana ba domin kuwa ana maganan kusan shekaru 100 ne da suka wuce.

Wata baiwa wacce sukayi alwalan kwanciya tare ta gani tana sallah ita kadai kowa ya kwanta zama tayi a gefe ta jira ta. Bayan tayi sallama tace Mata asma'u ko? Daga kai baiwar tayi tace laila ko? Itama daga kai munira tayi tace  idan....banso....zaba..ni... me zanyi? 
Gira a Dan harde saboda jin yadda munira tayi magana da kuma shakku ko ta fahimci me muniran tace yasa asman tace idan bakyaso a zabe ki? Daga kai munira tayi tace dama a duniya akwai Wanda bayaso a zabe sa? Dake daga kai munira tayi.

Sake rage murya asma tayi tace ba yadda za'ayi baza'a kaiki wajen zaben nan ba saide idan baki da lafiya. Munira tace an gama. Asma tace kul karkiyi karya wa sarki idan ba haka ba za'a miki bulala 5 Dan hakan yana nuna rashin amana ne. Munira tace baja'a(baza'a) gane ba. Asma tace toh amma me yasa bakyaso a zabe ki?

Munira taso ta fada amma ganin bata Santa ba yasa tace karki damu... an fata mici watayan (Zan fada miki wataran)  tana kaiwa nan ta koma dakin su tare da kwanciya a makwancin ta tana mai kallon sama. Tana tunanin wani irin rashin lafiya zatayi da zaisa baza'a kaita gurin zaben ba. Can dai ta tuna a iya zaman ta daji idan taci tufa apple yakan sa ta yin amai da Wanda har sai ya harkar Mata da jiki.

Dan haka ta kudi ri niyan neman apple gobe da asuban fari da a dauka tun cikin dare aman ya kamata. Amma wani hanzari ba gudu ba Dan kuwa an gudu ba'a tsira ba. 'Ka'ka ankayi? Batasan sunan apple din ba.😁

Nazarin duniya ta gama bazata iya tuna ko sau daya da ta taba jin sunan sa ba a haka har bacci ya kwashe ta tana ta juye juye. Da asuba ko da aka tashe su  bayan tayi alwala kin komawa tayi nana ta lura hakan yasa tace uwar daki da sauri munira ta girgiza Mata kai tace au yar uwa ta laila akwai abind kike nema ne? Munira tace ka ki damu ki yi shirin tafiya masallati ina zuwa.

Haka yake a gidan sarkin kowa da kowa a masallati ake haduwa ayi sallah suna rayuwar su a dmfadan Lamar suma gari ne me zaman kansa domin in aka hada kowa da kowa harda dogarai da bayi maza da Mata da jakadu da masu aiki toh zasu kai dari bakwai wannan kuwa ba karamin al'umma bane.

Nana tana shiga daki kamar hakan asma ke jira ta fito ganin munira yasa tayi murmushi sannan ta tsuguna a gefen ta itama tare da yin bismillah sannan ta fara yin alwala bayan ta kammala ne ta kalli muira tace ya nagan ki lafiya ko kin yarda zaki je ne?

Matsowa daf da ita munira tayi ta dauki kara ta zana apple ta nuna shi tare da fadin ina an samu? Asma cikin rashin gane me munira zatayi da tufa tace Mata wajen jinin sarauta? Suuu... kadai suke ci mu sau biyu a shekara ake bamu kuma wata biyu da ya wuce aka bamu Dan haka sai nan da wata shida.

Munira tace kamai(r) wa? Asma tace kamar sarki,sarauniya, yarimomi, naji ance gimbiya hauwa ma tazo. Munira tace wanne yafi caukin tamu(saukin samu)? Asma tace gimbiya hauwa Dan nice me kwaso kayan wanki a kowani bangare yau ma zanje da hantsi. Munira cikin magana irin nata tace bari na shirya sannan ta shiga daki. Bayan sunyi sallah aka kada su a fara layin wanka.

Da sauri sauri munira tayi nana dai sai kallo ta take italuwa saurin ta kar asma ta tafi dibo kayan wanki bata bita ba. Nana dai kallon ta kawai take yi. Kayan da kowa zaisa ya ciro itama ta ciro nata amma bata saka shi ba da kayan ta na jiya ta fita daga bangaren bayi ta buya a bayan bishiya tana jiran asma. AI kuwa asma ta fito tana tafe tsuluf taga mutum a gefen ta. Salati tayi tace munira naga alamu kamar gidan iyayen dakin ki na da basu da tsauri nan fa fada ne in kika fiya irin haka za'a ga kamar aiko ki aka yi Dan ki cuta r da wani kuma filled miki kai za'a yi.

Da sauri ta rike wuyan ta yayin da take tunowa da zul da yimla. Ta sanar da su su biyo ta amma kar su shiga fada akwai wani lambu a gefen fada su zauna anan suna rayuwa duk sanda ta Samu ta hadu da yarima zata sa a shigo da su tunda yarima ya sansu ma. Yanzu in ta mutu aka cutar da su fa? Wani yawu ta hadiye amma de taci gaba da bin bayan asma tana tsula ido.

Ajiyan zuciya asma tayi tace toh amma duk abinda kika hawa kanki ni de ki cire ni Dan bana so na mutu wa zai kula da mahaifiya ta? Shiru tayi tana so ta fada wa munira AI kawo ta akayi da yancin ta amma dai sai tayi shiru Dan basu Saba da munira ba.

Koda suka isa bangaren gimbiya hauwa kuwa ga nan kwandon tufa da kwandon lemo da tanjirin. Shiga ciki sukayi suka kwaso kaya ta gefen tufa din munira tabi da gangan tayi Tuntube  tare da zuba kayan wanki domin ta samu ta dauki guda daya saide tayi rashin sa'a sai lokacin gimbiya hauwa ta tashi yin sallah Dan haka cikin zafin nama ta dauke ta da Mari tare da fadi wacce dabba ce wannan da ko tafiya bata iya yi? Ya za'a yi a kawo min sabi dasu ki zuba min kaya a kai? Asma ne tayi sauri tace kiyi hakuri shugaba tana cikin bakin da aka kawo jiya ko darasi ba'a koya musu bu.

Tana son fadar nan ne yasa tace zata biyo ni ta fara aiki. Tace menene sunan ta? Wata daga cikin bayin ta tace naji ance sunan ta laila. Tsaki tayi tace ku tattare ku zubar.. munira ne ta matso tace ki bawa sabin....bayi.. jai kaya miki dayaja. Yatsine fuska tayi tace ke kina da wani cuta ne? Me kike cewa? Asma kamar zatayi fitsari tace ta taune harcen ta ne tana karama cewa tayi ki raba wa bayin hakan zai kara miki daraja a idon su kuma abin ba zai zama asara ba. Murmushi ta danyi tace dukda kin taune harshe ashe de kwakwalwar da sauran ta. Tabe baki tayi tace ku raba musu.

Wani dadi munira taji yanzu zata ci da hujja godiya sukayi tare da yin mar marza suka fice. AI kuwa suna ta canja kaya suja ga an shigo dasu kwanduna uku... bude baki tsaffin bayi sukayi suka ce ince wata biyu da ya wuce aka bamu wani Abu ne ya faru? Bayin gimbiya hauwa sukace wannan yar iskan ce ta wulla kaya akai shine gimbiya hauwa tace a Baku raba musu akayi sannan suka fice suna fita kowa ya matso yana tambayar munira ya sunan ki? Wasu na Mata godiya wasu na fadin gaba ta kaimu AI me abin kiran ta yar iska AI abin arziki ta janyo mana Allah yasa kullum tayi tuntube 😂

Dauka munira tayi tana kallon sa tace ya kai tufa kar ka bani kunya sannan ta gutsira cikin sauri sauri nace toh fa ana wata ga wata.

MUJE ZUWA MUGA DE KO ZA'AJE WAJEN ZABE DAJE KO KUWA DAI ZAKI SHA MU HADE GOBE KAWAI FANS. JIYA NETWORK MAWA BASHIDA KYAU... KAMAR KUMA YANDA KUKA SANI BANA SAMUN TIME SAI DARE .

KAR KU MANTA DA LIKING, FOLLOWING TARE SAMBADO MIN COMMENTS

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CEOnde histórias criam vida. Descubra agora