CHAPTER 54 (FINALE)

525 107 36
                                    

Baiwar tace mene? Suka ce eh mai martaba ya gaiyace ta. Baiwar tace in haka ne toh ai labari ya canja kuma magana ta girmama kenan sabuwar kwarkwarar sarki , laila TANA DA KW*RTO?

Ranta dadi domin tasan cewa in ta kawo labarin nan za'a bata kyauta me tsoka. Komawa tayi da labarin ta gari na waye wa ta dawo nan fa ta sanar da dayar mantar sarki mai suna suraiya.

Cikin jin dadi suraiya ta ma kasa zama tace aiko yanzu zan koma na sanar da me martaba da sauri bayin ta suka ce ya shugaba bamu da sheda kinsan in bazamu iya bada shedu 4 ba bulala ta hau kan mu. Suraiya tace kuma kun fadi gaskiya toh yanzu ya zamuyi?

Daya daga cikin su tace me zai hana a sa mata ido duk maotsin ta ai dole ta bamu wani abin zargi. Suraiya tace haka za'ayi da kaina zan dinga zuwa mata yini ta Allah ba nata ba.

A take ma ta tafi bangaren munira bata dawo ba sai dare bayan ta tabbatar ta sanar da yan sa ido su saka daga yazo su kira mai martaba su garkame kofofi.

Saide fa kamar yarima ya sani har kwana 13 ya wuce bai zo ba sau biyu yazo da rana amma jin muryan sauran matan baya kwankwasawq in de yaji muryan munira ya tabbatar lafiyan ta kalau shikenan.

Saide hakan ya damu munira gashi yanzu bata da sakat kamar da inde zata fita sai da bayi dama ko taje wajen yarima ko su asma ne toh suna zuwa wajen ta.

Gashi bata da sakat dan kullum kafar siraiya yana gidan gata da kaudin tsiya. Munira kuma batason tace zata fita suraiya taga kamar ta wulakan ta ta. Itako suraiya ta dage dan gani take randa bata zo ba ranan zaizo. Toh amma in daya daga cikin fadawan fada ne fa?
Bazai zo ba ai tunda yasan tana nan mai zai hana kar tazo gobe ta mike zata yi wa munira sallama munira ta sake rugawa ban daki da gudu tana harar wa. Wani abu ne ya fadowa suraiya idan ta lura jiya da daddare munira tayi amai bayan sunci abinci sai suka barshi a cewa man shanun dake ciki ne.

Yau sau uku tana harar wa duk sanda zata yi alwala suraiya bata lura ba amma yanzu kam. Wani ras taji kar de cikin mai martaba ne da ita? Wannan wani irin shan layi ne haka?

A zauce ta fita ta ma rasa me zata yi bayan sun iso barinta baiwarta tace me zai hana mu rubar da sauri suraiya ta mare ta tace ke mahaukaciya duk rsshin imani na bazan iya yin kisa ba bazan iya yin shirka ba ai kishin ba hauka bane.

Da sauri baiwar ta russuna kai tace tuba nake shugaba ta subutan baki nayi. Niko nace kaji yar air bata gari banza. Wannan maganan ds baiwar tayi yasa suraiya taji jikin ta yayi sanyi tayi nadamar sa idon da tayi wa munira toh amma namijin da aka ji a dakin ta fa? Da sauri ta kalli baiwar tace kar ki ce min batun nan ma kazafi kika mata?

Da sauri ta girgiza kai tace wallahi gaskiya na fada shugaba ta . Kwafa suraiya tayi bata de gama yarda da baiwar ba. Amma ta sha alwashin ta cire hannun ta daga al'amarin kami ta kife da ita. A hakikanin gaskiya ma munira tana dan burgeta dan duk zuwan su dukda munira tasan takurar ta suke bata taba nuna musu gajiyawa ba.

Bata taba nuna ta gaji ba tana da kawaici. Suraiya haka ta dunga nazari toh yanzu ta zauna da zuciya daya da munira taje da gaske mazinaciya ce ya kwabe da ita? Tayi shiru ne ko ta fada? Tagumi tayi tace Allah ka yafe min rashin Ilimi na jahilci mugun abu ne yanzu dubani ban ma san me ya kamata nayi idan ana zargin mutum da zina ba.

Bari nayi shiru kawai.... toh amma fa abu daya da na sani shine ko mata zina tayi da de dan mijin ta ne. Dan haka.... da sauri tasa aka nemo mai magani ba bata lokaci suka tabbatar mata da zargin ta ba shakka munira tana da ciki ai bata yi wata wata ba dare yana yi ta nufi wajen mai martaba dukda ba'a kira ta ba.

Tana shiga ya kalle ta da murmushi yace surwiya lafiya dai ko ? Kina da wani matsala ne ? Girgiza kai tayi tace albishir na zo maka dashi mai martaba yace toh Allah yasa muji me kyau. Zama tayi a gefen sa tace zamu samu karuwa murmushin dake fuskan sa ne ya fadada yace kina da juna biyu? Girgiza kai tayi da sauri tace ba ni bace yace wace?

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 13, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CEWhere stories live. Discover now