CHAPTER 7

780 120 6
                                    

A garin banty kuwa mikewa sukayi daga cikin fada inda suka dangana zuwa gidan sarkin gaishe su nayi ke ta yi ya wuce gaban sashin matar sa da na KWARKWARAR sa wacce yake mugun so fiye da matar sa ta aure me suna marka.

Ba kamar sarauniyar masarautar unto ba wato maman su kabir. Ita marka in bata sonka zata nuna maka bata son ka amma idan aka zo gaban mijin ta wato sarkin garin banty toh malamin ta na farko shine hawaye. Zata nuna ko me ya faru ita aka zalina ko kuma ta nuna ta amshi laifinta sannan ayi Mata hukunci me tsanani shi kuwa sarkin garin banty saboda son da yake Mata sai ya dinga Mata uziri saide Sam Sam baisan yana kunnanwa gidan sa wuta bane Wanda  kashe ta Abu ne mai mugun wahala.

Daidai suna shirin shiga sashin dake gefe na marka sukayi arangama da ita ta karyo kwana ita da jakadiyar ta da bayi guda hudu. Wani birki taci kamin cikin murya me karya zuciya da nuna damuwa tace miji na mai martaba me nake gani?

Shin baka gane wacce ke gefen ka bane ko ka manta ta ne ko bakaji me mahaifiyar ta tace kamin ta mutu bane ? Nide ina tsoro kaga muna da yan yara yara a gidan kar ta kwashe mana su.

Murmushi yayi yace karki damu marka bazama su hadu ba na Riga na bada Umar ni an rufe ko wani washe babu Wanda zai fito daga nashi har sai ta fita. Dan leka fuskan yarima Umar tayi tace nikam ina ka samo wannan kamar nasan fuskan nashi.

Naga sai takam.... da sauri jakadiyar ta ta rufe Mata baki sannan ta rada Mata AI yarima ne baki ganeshi bane? Da sauri ta hankade jakadiyar tace toh me nace dama ai baki barni na karasa bane yarima barka da zuwa gidan mu ta fada tana russunawa kamar da gaske. Tace fatan dai ba muyi laifi ba dukda zuwan yarima alkairi ne a kowani lokaci.

Sarkin ne yace toh ya isa marka ke de ba iya magana ba da taryan Bali aje a shirya wa yarima abin sha a kawo sashin khadija. Tace an gama mai martaba. Yadda take magana da sanyi murya kai kace ko marinta kayi zata gode maka ne.

Shiga farfajiyan sukayi suka zauna inda sarki yace a cikin farfajiyan sashin nan Alif na 1932 kwarkwara ta mai suna khadija haifa min yarinya Wanda itace ta saka Mata suna muneera. Banyi wani farin ciki ba saboda a lokacin ma ina da yara maza da Mata sannan kwarkwarar ba wani sonta nake ba.
Kyauta ce aka aiko min daga masarautar kushma kawai de na dauke ta ne amma saboda sanyin halinta da hakuri yasa ta shiga raina. Nan dai sarki ya tsara musu bangare labarin sa da abinda ya sani.

USULIN YADDA ABIN YAKE..

Ranan da khadija ta haifi munira ba Wanda ya sanar da me martaba har akayi kwana uku ba'a kawo Mata komai na me jego ba iya ka ruwan zafi da ake tafaso Mata shima sai anyi tashin hankali da jakadiyar ta safiya. Sa saide khadija tace wa safiyan ko me zai faru kar ta fada wa mai martaba saboda kar ace daga zuwan ta ta fara hada guri Dan hatta cikin nan da ta Haifa sanda aka ce daga zuwa ta fara zubar da yara.

A takaice de mai martaba bai San ta haihu ba sai bayan kwana 5 ba abincin kirki ba kula da ita na arziki ko bayi ita ba'a bata ba sai gida biyu da jakadiyar ta sadiya. Ko da mai martaba ya ga yarinyar yace kai lallai khadija kina cin abinci dayawa ji yarinya katuwa da kika haifo shi duk a tunanin shi yarinyar kwananta 1.

Bai wani damu da ramewa da khadija ke yi ba a tunanin shi lailai da haihuwa ne shi a ganin sa ya tausaya Mata shine yace ta saka wa yarinyar sunan da take so. Itakuwa tags ba sunan da yake Mata sai munira.

BAYAN SHEKARA BIYAR DA HAIFAN MUNIRA(1937)

Da sassarfa jakadiya sadiya ta shiga madafan gidan wato kitchen da kaga fuskanta kasan tashin hankali zata je yi. Shugaban madafan ne tace toh toh toh uwar kaudi yaya akayi? Cikin bacin rai tace binta ni wannan abun ta ishe ni fa ya fita a kaina wallahi ko ku bawa shugaba ta gawayin da akace a bata ko kuma yau ayi tashin hankali. Kwano 8 akace a bawa kowa amma mu kwano biyu ake bamu kuma ace bamu isa muyi magana ba?

Karfa ku manta juna biyu ne da ita ga karamar yarinya wai ku bakuda imani ne? Sukace aikin kenan da anyi magana ku fara labewa a bayan ciki. Abu kadan kuce ciki ne da ita sai kace kanta aka soma haihuwa. Jakadiyar kwarkwara marka ne tazo tace ya naji ana hayaniya ne kun de San cewa uwar daki na kanta na ciwo tana bacci ko? Jakadiya sadiya tace dole tayi bacci an bar me ciki tana darin sanyi da tsakiyar rana ina ga dare kuma?

Jakadiyar marka tace kada kiyi mana sharri Dan uwar daki na bata da lafiya an samu matsala shine zaki ce laifin mu ne? Toh tunda ma abin haka ne mun dena kula da gidan zamu mayar wa mai martaba mukulli dama wannan aikin sarauniya ne ba mu ba. Kukan karya ta soma tace daga taimako shine za'a daura mana laifi...

Sadiya tace za'a bamu ko kuwa? Jakadiyar markan ne tace ke shugaba binta basu mana ki basu kwano 10. Tabe baki tayi tace ku de kuka sani kawowa akayi ta dauko Jakarta da take dauke da shi ta dibi kwano takwas abinta tace mu bazamu ci abinda bai halasta garemu ba domin ba koyarwar manzon Allah bane sannan bazamu ci amanar Allah ba.

Kama hannun munira tayi tace zo mu tafi lokacin da yake yamma ya gabato. Bayan sun isa Khadija ne tace sadiya ya akayi suka baki cikin sauki? Tace zuwa nayi na rokesu suka bani. Munira tace kai yaya sadiya ki fadi gaskiya. Da sauri sadiya ta rufe Mata baki tace zo muje kar mu dami mahaifiyar ki.

Tace toh mama mun tafi zamuyi wasa ni da yaya sadiya murmushi khadija tayi Mata tace toh ni zanje nayi sallah. Wajen karfe 7 suka zo cikin farin ciki zasu rura garwashi yau zasuyi kwanan sumi saide me suna fara rura shi ya bude masu dakin da hayaki.

Ba yadda suka iya dole su fita waje hayaki ya fita kamin su dawo. Saide kuma kamar ba sanyi ake ba Dan sauraye a wajen nan haka suka dinga susa. Kwanciya munira tayi a cinyar mahaifiyar ta tace mama wai me yasa ba'a son mu a gidan nan. Khadija hade rai tayi tace karki kara cewa ba'a sonki kinji ko? Kiyi hakuri komai lokaci ne.

Tace toh mama me zai hana ki fada ma baba? Khadija tace karki fada masa komai duk ranan da kika kuskura kika fada masa karki kara kirana da maman ki. Da sauri munira ta rungume ta tace kiyi hakuri bazan kara ba.

Shafa kanta khadija tayi tace Allah yayi miki albarka tashi mu koma ciki. Munira tace yunwa nake ji mama. Murmushi khadija tayi tace muje in baki kici abinci kinji. Wani gurasa guda daya Wanda sadiya ta Sato musu a kitchen ta bata tace gashi dukda cewa itama khadija batasan satowa sadiyan tayi ba.

Munira tace mama ke kinci abinci ne? Murmushi khadija tayi tace naci tun dazu AI ni na cinye ma shiyasa guda 1 ne yayi saura. Jin haka yasa munira tayi murmushi da sauri ta fara cin abinta taci rabi kamin ta mika wa maman ta Rabin tace ni na koshi zanje inyi bacci. Shiga daki tayi kamar ta kwanta ta leko ta kasan kofa tana hawaye ganin yadda mahaifiyarta ke sannan busasshen gurasa da ruwa.

.....to be continued

YAN UWA NAGODE SOSAI DA KAUNAR KU GARENI A CIGABA DA SAMBADO COMMENTS DAN ALLAH KO MUTUM BAZAI YI COMMENT BA YAYAI VOTING.

THANK YOU!

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CEWhere stories live. Discover now