CHAPTER 22

618 91 12
                                    

Ihu ta kwala lokacin da zata fada hakan ya janyo hankalin yarima da sauri ya diro daga dokin sa tare da rugowa da gudu yana kwala sunanta saide kamin ya iso wani yasa wuka ya soki kafadan yarima hakan yasa ya gidana zuwa guiwowin sa kamin ya fadi yana me doke kansa da wani dutse tare da rufe idon sa.

Munira kuwa sa'a taci ta fada kan bishiya hakan yasa hannun ta ya Dan kurjine kamin ida riganta ya makale a bishiyan ya karye Dan haka ta tiko kasa Tim jin kamar gumi yana bin fuskarta tayi ko da ta taba taga jini ne bishiyan ya karjene Mata harda fuska. Jiri ne ya Dan kwashe ta hakan yasa ta tsuguna tana mai dafe kai kamin ta sake tashi ta tsaya.

Ji tayi ana nishi da kuka kuka hakan yasa ta nemi inda take jin kukan dukda tana tsoro ga dokin ta yimla a gefe da alamu yayi targade a kafan sa na baya zul kuwa ba abinda ya same sa illa yankewa da shima yayi a fuska. A bayan wani dutse taga wata budurwa me kama da ita sak tunda taga kamannin ta jiya a madubi saide wannan budurwa rufe take da jini.

Itama budurwar da take kwance tana haki Dan bude ido tayi ganin mutum me kama da ita sak. Tsugunawa munira tayi tare da riko hannun ta yarinyar tace mama na ki kula min da mama na. Munira tana son yin magana amma ta kasa. Budurwar tace sunana laila yaya ta yaya ta karki yad..... la ilaha illallah .

Kawai sai ta mutu a hannun ta munira taga wani sarka hakan yasa ta dauka tare da kalla a jiki an rubuta Dan masani amma bata iya karantawa ba. A daddare ta dawo gefen dilanta kamin jiri ya kwashe ta ta fadi. Baifi minti Goma ba wasu tawadan mutane daga ganin su masu gadi ne Dan suna da uniform rike da Karen farauta saga gani neman mutum suke koda suka iso inda munira suke daya yace gata nan mun same ta amma sai suka ga wannan Karan yana kokarin cigaba da tafiya domin shi yana jin kamshin laila a bayan dutse ne su kuwa ganin munira yasa sukayi tunanin ko itace laila Dan haka suka dauke ta.

Tare da kokarin tahowa da dokin ta shakuwa zul buya yayi sanda ya jiyo su saboda shi dila ne za'a iya tunanin shi yaji Mata ciwo a kashe shi.

AN FARA.....

Hakan rana da munira taji dalle Mata fuska ne yasa ta bude ido tare da tarewa kara nitsewa tayi cikin katifa domin taci gaba da bacci fuskan laila ne ya fado Mata a lokaci daya ta tuna da duk abinda ya faru da sauri tayi asha ruwan tsuntsaye ta diro daga gadon. Yan Mata guda hudu ta gani suka durkusa tare da furta barka da tashuwa karamar uwar daki.

Harde gira tayi tana kallon su a rashin fahimta tare da ce musu tashi. A kwakwalwar ta kuwa tunani take karamar uwar daki? Su yarima sun tsunceta sun kawo ta fada ne ko a ina take....Tashi sukayi tare da godiya sai taga abin wani iri Dan bayin gidan su basa durkusawa. Kalle kalle ta fara wata daga cikin bayin me suna nana ta matso tace shin kina neman wani Abu ne uwar daki?

Da sauri ta girgiza kai nana tace na hada miki ruwan wanka ki shiga ki watsa... dan cizon yatsan ta tayi tace umm shugaba da ranshi ya Dade suna jiran ki. munira tace "waye cu(su)?" Kifkifta ido nana tayi cikin mamaki kamani ta cewa bayin nan suke an sallame su. Suna fita da sauri ta zauna a gefen munira Wanda yanzu za'a dinga kiran ta da laila tace uwar daki na laila ya naga kamar kin canka muryar ki ma ta sauya.

Shiru munira tayi nana tace ni de a iya sani na ke mutum ce me yawan surutu fadi ba'a tamabaye ki ba. Kinga ranan ma sanda ranshi ya Dade ya mare ki. Da badan shugaba da uwar daki babba sun tare miki ba da ya Zane ki. Ajiyan zuciya munira tayi na farko de munira bata gane ko Abu daya da nana take fada gashi magana bai nuna a bakin ta ba. Gashi tana da tambayoyi dayawa kuma tanaso ta fada wa nana amma tambayar anan shin zata iya ajiye sirrin?

Munira ne ta nuna kanta tace "magana kadan " Jan numfashi nana tayi tace uwar daki kinga irinta ko sanda nace miki kar ki bishi kar ki bishi kika bishi yanzu gashinan kinji ciwo bazaki iya magana ba... ta karashe maganar tana fashewa da kuka.

Rike hannun ta munira tayi tana shafawa ta Dan turo baki tace "waye ci (shi) din?" Dago kai nana tayi daga cinyan munira tace na shigo uku karkice min kin Mata shi ? Munira tayi shiru nana tace kin manta komai ? Ta fada tana zare ido Shiru munira tayi kamin ta daga kai sake fara kuka nana tayi kuma da sauri cikin jin dadi ta Mike ta tsaya tare da fadin hakan ma yayi kyau ba sai kinyi ta fada da baban ki ba kenan.

Munira tace "ba Gaye ba." Nana tace haka zaki ce ban gane ba. Sake matsowa kusa da ita tayi ta zauna tace kar ki damu zan fada miki abubuwan da kike bukatan ki sani amma yanzu ba lokaci Dan haka idan kika je wajen su shugaba ko me suka ce miki kice kin amince kinji? Munira ta daga kai. Nana cikin wake tace Mata ni sunana nana yarinya mai kyau da tarbiya, tun muna yara muka shaku, dare da safe muna jojjone dalili kuwa Dan ni baiwar ki ce.

Cikin dariya munira tace na gane. Nana tace yi sauri sauri suna jiran ki a kasa da minti talatin nana ta shirya munira tas tana gyara Mata gashin ta ne take cewa sunan ki laila munira tace toh sunan mamanki bazan iya fada a fili ba Dan ni baiwa ce nuna kunne munira tayi. Nana ta rada Mata sunan maman laila sannan tace abban ki sunan shi Dan masani mai kudi da yamutse fuska munira tayi nana da Dan dara tace baban shi ne ya sa masa saboda ilimin da kuke da shi a gidan ku. Mai kudi kuwa saboda kaf nahiyar nan banda gidajen sarauta ba Wanda ya kaisa kudi.

Jinjina kai munira tayi alamun fahimta. Nana tace yauwa sai batun Bello saurayin ki ne Wanda kuka gudu tare kwana biyu ana neman ku sai jiya da yamma aka samo ki amma shi ba'a Ganshi ba. Munira tace oho dauko babban zanin da munira zatayi hijabi da shi nana ta dauko Dan lokacin su ba a dinka hijab irin na mu mai zare kawai babban yafi zaka nada. muje ko nana ta fada lokacin da ta gama nada wa munira hijabin ko nace jilbabin ta. Fitowa sukayi nana tace kai uwar daki gani nake kamar cikin kwana biyun da kika gudu kinyi haske sosai sannan gashin ki ya ninka a tsayi. Munira tace a ranta na saka kaina a matsa ta ya zan cigaba da nuna kamar nine laila ? Kode na fadi gaskiya? Idan na fada kuma mahaifiyar laila zata yi bakin ciki ban cika alkawari ba kenan.

A zaune a lambu ta iske su fuskan Dan masani yanda kasan ya tauna fulajin 😂 sai hura hanci yake shi a dole yana jin haushin yar sa laila saide kash be San wanna muniran yarima bace. Mahaifiyar ta kuwa murmushi tayi tana mikewa saide ga mamakin su gani sukaji laila(munira) tace "ina...wuni ?" Da mama ki suka kalleta mamar ta cikin jin dadi tayi saurin zaunar da ita tana fadin lafiya lafiya yata lafiya fatan ba abinda ya sameki.

Nana ne cikin rawar murya zata durkusa zuwa kasa munira ta riko ta tare da girgiza kai tace "haram" tana Mata murmushi sakan baki Dan masani yayi ko kyafta ido bayayi. Cikin rawar baki nana tace ya ku shuwagabanni na uwar daki na ta Dan ji ciwo a harshen ta hakan yasa bazata iya magana sosai ba ko kuma ta furta wasu kalmomin ba daidai ba.

Shide dan masani gani yake ana kokarin a cuce sa ne kode ta hado wani makircin ne ta nuna ta bada kai Dan ta samu kofa ta sake guduwa. Kwalla ne ya cika idon mahaifiyar laila Dan kuwa ita daya ta Haifa hakan ya sa ta shagwaba ta sosai har ta zamto baza'a iya control din ta ba.

Mikewa mai kudi yayi yace nide ba wannan ba da kika gudu kike nema ki ci min mutunci ba ni kika yiwa ba kanki kika yiwa yar uwar ki malika yarinya mai hankali hade rai maman laila tayi ... dan masani yace malam bashari yace danshi bazai auri yarinya da bata da kamun kai ba Dan haka na cika miki warakan fada (yana nufin form) ki shirya nan da mako biyu za'a yi koyan tarbiya da karatu a fada kamar yadda aka Saba duk matan da suka yi shekara 16. Sarki zai zabi guda 3 su zama kuyangu saura kuwa su zaba ko su zama bayi ko su dawo gida. Idan kuwa suka dawo gida ba zasu yi aure ba sai bayan shekara 2. DAN HAKA DOLE KI ZAUNA HAKA AL'ADAR MU TAKE.

KUNGA YAU NAYI MUKU TYPING ME MUGUN TSAYI GASKIYA AYI MIN COMMENTS SANNAN A TAYANI SHARING KUMA DON ALLAH A DINGA ZUWA ANAN VOTING MA TA WATTPAD SANNAN A DINGA SHARING

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CEWhere stories live. Discover now