CHAPTER 50

321 88 24
                                    

YEAH FINALLY NA DAWO GIDA ZAN RAGE TSAYIN LABARIN MU GAMA SHI DAGA NAN ZAMU SHIGA SABON LITTAFI NA ZA DAI KUJI BAYANI AKAN SA....

RECAP

Saboda hankalin ta yana kan sakan da take ta bayani, ita da take yar koyo karfin hali wai zata koyar. Can bayan kamar dakika goma yarima yace yan mata ba tare da ta kalle shi ba tace na'am yace bacci nake ji ki dumama min gado na da sauri ta mike ta tsaya tace ban yarda ba. Ashe surutun banza nake ta yi tun dazu na dauka ma kana jina.

Yace toh shikenan bara na dumama abina hawa yayi ya kwanta lekan shi ta tsaya take yi tace da gaske wai kayi bacci bai kula ta ba kuma dama idan shi a rufe. Matsowa tayi ta leka fuskan sa taga idon sa a rufe tace da sauri haka, kara tayi jin an janyota rufe bakin ta yayi da nasa, ta zare ido kamar mujiya.

Yace za ki kurmanta ni itakam ta kasa magana tayi lunkui kamar jaririyar kulya. Ba wanda yayi magan can yace farillan sallah guda bawa ne?

CONTINUATION

Bashi amsa tayi ya cigaba da mata tambayoyi dan ya tabbatar ta iya ibada na gabbai sanin cewa a daji ta taso yakan sa wani zubin ta sauka ta nuna masa ma kamar yadda ake sujjada tayi kokari saide ya sameta da kure sosai wanda ya gyaggyara mata domin yasan wajibin miji me kuma hakkin mata ne akan mijin ta ya ilmantar da ita idan ma bayida lokaci dole ne ya saka ta a makaranta.

Sannan mutum baya zama mai ilimi sai yana aiki da ilimin sa duk yawan littattafan da mutum ya karanta inde baya aiki dasu bashida ilimi ya karanta littatafai dayawa kawai za'a ce sannan dan mutum ya haddace Qur'an ba yana nufin yana da addini ko tarbiya ba. Qur'an kan zamo alkairi ko masifa.

In kayi aiki dashi ko baka haddace ba Allah ya maka alkawarin aljanna amma ko in ka haddace baka aiki dashi toh lallai zai zama hujja akanka ne kuma na daga cikin  mutanen da zasu fara  shiga wuta wanda suke da ilimi basa aiki dashi.

Sannan dan mutum yana aikin kwarai hakan ba hujja bace yayi na banza dan mutum yana zuwa makaranta, masallati ko wurin wa'azi ba hujja bace aje gidan biki ayi ta zubda mutunci ana sauraren madujala (ko dinner ko bridal shower ) ana casu yin hakan kamar mutum ne yayi bismillah yasha giya hakan bai halasta masa ko ya dauke haddin da za'a zartar masa ba.

Bayan kwanan biyu yarima kabir a bangaren sa yana cin abin ci wani tunani ya fado masa in ba kuskure yake ba kwanan sa uku baiga matar da aka aura masa ba. Tunowa yayinda yamda take bin gini da siraran sangalelen ta da alamu bata cin abinci yanda ya kamata.

Ganin yanda sanyi yakai iya sanyi shin an kai mata gawayi ma kuwa ?  Tashi yayi ya fita ya nufi hanyar dakin ta. Kamar an zungure shi ya fasa yasha kwana ya fita.

Haka rayuwa yaci gaba a kwana a tashi kauna me karfi ta ginu tsakanin yarima da munira ko wani dama in ya samu zasu yi karatu. Yana kula da harkokin masarautar wani zubin kabir kanje bangaren yarima wai a dole sai ya tafi da munira.

Sarauniya kuwa ta samu gu ta karya kafa tana jirsn rikici ya fara dan kuwa tasan sarai yarima yana tare da munira kuma dan leken asirin da ta dasawa mai martaba ya sananr da ita al'amarin da ya wakana lokacin da munira ko ince laila ta gamu da sarkin.

Bayan wani lokaci maimartaba ya dawo sun dibo hanaya tsakar dare suka dawo washe gari ana ta zuwa masa sannu da dawowa sai bayan kwana uku yarima ya samu daman ganawa dashi dkmin yi masa bayanin abubuwan da ya faru baya nan. 

Bayan sun gaisa yarima.na shirin magana waziri ya shigo yace mai martaba aikin da ka bayar da kaina nayi au ga yariman nan ma. Yarinyar nan tabbas daya daga cikin sabin bayi ne kuma yanzu haka tana cikin bayin yarima ne. Mai martaba yace Allah sarki.

Yarima yace abba lafiya dai ko? Mai martaba murmusawa yayi wanda ya dade be yi irin ta ba yace daya daga cikin bayin ka nake so ka bani yarima yace har ma.sai ka nemi izini mai martaba ko yamzu ma aje a taho maka da ita.

Mai martaba yace ba dai yanzu ba, gobe sai a dauko ta ai ko? Jinjina kai kawai tyarima.yayi bai wani dauki abin da mahimmanci ba dan ko wace baiwa aka dauka bashida damuwa kuma ya riga ya yanta munira dan haka ba baiwa bace a wajen sa shiyasa sam bai damu da tambayar wa ake so ba dan ko duka bayin sa ne zai iya bawa mahaifin sa da duk wani abin da ya mallaka.

Da daddare munira tana jera kayan ta taji an mata kukan kura a kunne tsalle ta daka zata tsala ihu aka rufeata baki sannan dariya yarima ya karade dakin ta. Cizon hannun sa tayi kamar zata yi kuka tace da kanka kamar lemon tsami so kake na mutu ba tare da annashuwan dake fuskan sa ya dauke ba yace na gaishe ki matar me kan lemon tsami.

Daga hannu tayi zata make sa ya zille ta sake kaiwa ya zille kamin ya arce ys dale gado tsalle tayi zata cafko shi tana fadin ka tsaya ka gani in ban cinye hancin ka.

Dariya yayi yace kazama.... saide kamin ya karashe maganar sa ta bige kafa da karfen gado da sauri ya sauko ya duba karfen ya dan yanke ta. Goyon ta yayi ya fita daga sashin ta zuwa nashi domin yasa mata magani.

Dama yazo ne ya kira ta su ci abinci yaji shiru bata zo ba. Bayanan sunci abinci ba wata wata suka kwanta ta basa haddan da ya daura mata aya biyu ne ba yawa daga nan ya fassarw mata ma'anar ayan dalilin sauko dashi da inda aka saukar dashi tayi lunkui a jikin sa kamar kulya tana gyada kai kamar kadangaruwa alamun ilimin yama shiga kuma tana nazari ba wai kawai shanye wa take ba.

Washe.gari da hantsi sai ga sallama aliyu ya sanar da yarima dake durkushe tsakanin kafan munira tana daura masa rawanin sa. Cewa anzo tafiya da baiwar ga alamu sarki so yake ya dauke ta a matsayin kuyanga saboda harda dokin daurata a kai. Daga cikin dakin yarima yace toh in ba kuyanga zai mayar ta ba me zaisa ya damu da wasu bayi ke kusa dashi inde zasuyi aiki ba cuta ba sata ai shikenan.

Tambaya mutanen sarki sukayi wacece laila a tare yarima da munira suka kalli kofa dukda mutanen suna can waje bawai ma suna sashin bane a take yarima ya mike yace mene?  Shafa kan munira dake zaune bakin gado yayi yace ina zuwa.

Bayan de yarima ya fita ya tabbatar ba shakku sarki so yake ya mayar da munira kuyanga baice komai ba kwai ya nufi fada saide kash aka sanar dashi mai martaba yayi badda kama ya fita yace yanzu zai dawo.

Ko da yarima ya dawo sashin sa an riga an tafi da munira kuma bawai sashin kuyangu aka kaita ba turakar sarki aka kaita wanda ke nufin yau sarki ke da niyar take ta a cewan aliyu. Ajiyan zuciya yayi yace shugaba kasan umarnin sarki ne babu yanda zanyi ina ji ina gani tana bori suka tafi da ita.

Da sauri yarima ya dafa gini amma ai ba komai har yanzu da lokaci zai samu mai martaba ya masa bayani sako ya bawa aliyu akan ya aika zuwa munira cewa tayi wani dabara ta hana mai martaba taya ta. Munira da uban bayi ke dirza ta tana samun sakon nan ta mike bata dami da kirjin ta da ya baiyana ba dan tasan babu wanda zai iya bawa bayin sarki aika sai jinin sarauta tana karantawa a baiyane tace har sai ka fada ma ai wallahi... bata idan zance ta ba aka sake dannata cikin ruwan wata dattijuwa na fadin yar nan ba sai ki fada mana ke budurwa bace muma nan da kike ganin shekaru baya kadan zam mike.

KAR A MANTA DA VOTING FA DA VOTES KE SAWA WATTPAD  SUYI SUGGESTING MA WASU 

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CEDonde viven las historias. Descúbrelo ahora