CHAPTER 10

712 93 22
                                    

Ba musu ya karba ya danna a baki Dan kuwa bayida buri sai ya aureta dan tun suna yara gimbiya hauwa ke damun sa yasan idan ya auri wata toh gimbiya hauwa bazata yadda ta zama kwarkwara ba ai. Saide danika biyar da cin wannan kwaro ya yanki jiki ya fadi warwas a kasa.

Dariya munira tayi tace kai yarima ashe kana da abin dariya toh na yarda kana so na amma ni yarinya ce fa ba abinda na sani ta karashe tana saka yatsa a baki. Ganin bai motsa ba yasa ta durkusa a gefen sa tace ko de baka da lafiya ne? Rike hannun shi tayi taje jikin sa yayi sanyi da sauri ta Mike Dan ta tuna sanda taji maman ta na fadin duk sanda jikin mutum yayi sanyi toh ya mutu ne.

Kuka ta fara tace ka tashi mana ba nace maka na yarda ba toh shine zaka mutu da gudu ta ruga ta koma fili. Tare tana haki cikin fashewa da kuka tace wa mai martaba kai mai martaba ya Umar ya fadi nayi ta masa magana baya kulani.
A take kowa ya Mike dakarai suka hanzarta wajen dauko sa aka nufi wajen mai magani.

Ajiyan zuciya mai maganin yayi bayan awa daya da yayi yana yiwa yarima magani kamin ya samu yayi aman kwaron. Fitowa yayi yazo wajen mai Martaba ya mika masa hannu sukayi musabaha. Tsayawa kallon su aka yi saboda ganin abin ake banbarakwai Wanda kuma shine abinda yafi dacewa saide al'umma dayawa bazasu gane ba. Ai shi sarkin da ya zama sarki bayida maraba da sauran mutane kuma AI ba wayon sa bane.

Da Allah yaga dama da ya bawa wani masarautar shi karuwa ce ma zata haifeshi ta yar saide Dan Adam mai karamar tunani Dan ganin yana mulkar al'umma shine yake jin kamar shi wani ne. Saide ko fir'auna gidan mulki kinga inda ya kare balle wani sarkin da ko a jahar su ba kowa ya sansa ba.

Mai maganin nan yace mai martaba na duba jikin yarima yanzu haka dai baya cikin wani hatsari ajiyan zuciya sarki, sarauniya da mai martaba sukayi Dan su uku ne a wajen. Likitan yace saide wani hanzari ba gudu ba. Wannan kwaron da yaci tana da matukar illa ko ince akwai babban matsala.

Wannan kwaron ba'a samun su sai sau daya a shekara biyar sunan su kwarin ba so wato duk Wanda ya ci su toh lallai kar ya kuskura zuciyar sa ta buga da niyar so. Wato dai bazai yuwu yayi soyaiya ba kuma ko tunanin Wanda yake son yayi toh lallai gubar zata doki zuciyar sa. Har yau ni de ban San maganain guban ba kuma bansan daga inda kwarin ke fitowa ba.

Baki na rawa mai martaba yace toh amma idan bazai yi soyaiya ba kenan bazai yi aure ba ta ya zai samu magadan sa? Kana so kace min babau wata hanya da za'a cire guban? Shafa gemu mai maganin yayi yace ranka shi Dade wannan hanyar tana da tsauri gara a barta kawai. Sarki yace fada min dai ko zamu iya. Mai maganin yace toh banki taka ba.

Hanya daya ce idan ya samu Wanda yakeso tsakani da Allah itama take son sa zuciyar zatayi zafi na wani lokaci toh sai ta dena toh anan dayan biyu ne bayan wani lokaci zatayi suka mai azaba wanda ya kai zafin haihuwa na wasu sa'o'i toh ko yayi aman bakin Abu wanda shine guban ko yayi aman Jini.

Idan har na biyu ne ya faru kar ma ku bata lokacin ku wajen neman magani dole sai ya mutu domin kuwa guban ce zata yi taurin kai taki fita sai ta huda masa zuciya hakan ne zan janyo jinin da zai amayar.

Godiya akayi masa aka saka delaria suka takashi ya fita. Wajen magrib yarima ya bude ido. Rike hannunshi sarki yayi yace Dan timati sannu kaji. Ya akayi kaci kwaron nan ? Kasan illar sa kuwa? A hankali yace me ya faru. Sarki yace kaci wani kwaro ne yanzu bazai yuwu ka yi aure ba har sai an samu magani.

Ya akayi ka ci kwaron? Shiru yayi saboda ya San gidan akwai munafukai tanzi idan ya ce itace za'a kunna Mata zafi Dan haka yace ban lura bane ya shige min makokoro Muryan munir aka jiyo rike da rake a hannun sa yace kai ya Umar ka fadi gaskiya na ga me ya faru fa.

Sarki yace me ya faru ? Munir yace ina cikin tafiya ta rike da kaza a dayan hannuna daya kuma rake na kawai sai naga ya Umar da mace me kamar maza suna magana labewa nayi naji duk abinda yace. Yaya sai yace wai ta aureshi ita kuma tace bazata aure shi ba sai ya ci kwaron.

Tafe kai yarima yayi ya ma juya musu baya shi matsalar sa da munir kenan ko me aka tambaya baya ma tsayawa yayi aiki da kwakwalwarsa waken ganin ya dace ya fada ko baj dace ba. Inde ya sani toh fada zaiyi. Hakan yana burge yarima a lokaci daya kuma yana bashi haushi.

Sarki baban munira ne yace wai munira nakeson kace min? Munir yace ni bansan sunan ta ba amma itace tayi wasan mashi... kaiiiii ya fada yana karasowa ya rike hannun yarima yace yaya na ashe sunan mu daya da ita. Ni munir ita munira ko ka manta sunan ta in ka tuna ni zaka tuno ta. Dariya akayi masa sai de fa baban munira murmusawa kawai yayi.

Ganin haka uasa mai martaba ya ce masa sarki karka damu kasan shirmen yara. Aikin gama ya gama dukda cewa kai Umar kafi karfin wannan shekaranka 14. Amma de kar ayi wa yarinyar wani Abu kawai a nuna Mata illar cin abinda ba abinci bane Dan kar taje ta ci itama.

Sarki yace insha Allah mai martaba mun gode da alfarmar ka. Washe gari aka yi wa mai martaba dakiya zuwa gari na gaba yayin da yace yarima Umar ya zauna har sai ya sake samun karfin jikin shi. Da daddare ranan da mai martaba ya tafi sarki ya nufi bangaren mahaifiyar munira sadiya ce ta fara jiyo takun su Dan haka da gudu taje ta samu khadija ta fada Mata.

Janyo munira khadija tayi tace me yasa mahaifinka ke zuwa bangare na ? Rabomda da nan tun ciki na yana da sati biyu yanzu wannan sa 10 Me kika biye min bayan wasan mashi kinyi wani Abu ko? Muryar ta na shirin karaya tace munira kullum ina fada miki kar kiyi fice kar kiyi fice ba wai Dan bana son kiyi fice ko bana son ki bane. Saboda bakida Wanda zai kareki, yan uwa na sun kasa karenina balle diyar cikina...

Sallamar sarki yasa ta yi shiru tace ranka shi Dade barka zuwa sannan tayi wa sadiya alamar ta kawo Masa ruwa da shayi. Amsawa yayi amma ya tsayar da sadiya tare da fadin ba wannan ya kawo ni ba AI khadija. Fatan baki da wata matsala? Tace ba komai na gode da kulawa. Jinjina kai yayi yace ina MUNIRA? yanda Kira sunan kawai kasan kashin munira ya bushe.

PLEASE AYI RUWAN COMMENTS INA NAN ZUWA IN ANSA KOWA. JIYA AN JINI SHIRU YAR ZAZZABI NAYI AMMA NA WARKE ALHMDLLH

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CETahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon