CHAPTER 41

431 79 19
                                    

Wani dariya ne ya kufce wa munira kawai ta fita ta nufi bangaren yarima kamar kura. Koda taje ta samu a rufe ne alama na sun fita wani bafade me gadin kofa ya sanar da ita yarima ya fita zuwa fada ba dan taso ba ta koma kallon hansai tayi tace toh ina katifa na?

Hansai tace sun kare Share ta kawai munira tayi dan idan ba rainin hankali ya za'ayi ace babu katifa? Ajiye kayan ta tayi akan gadon ta shiga sabgogin gaban ta.
Da yamma bayan ya dawo aliyu yana masa tausa munir ya zauna yana murmushi cikin tsokana yace yaya mutuniyar fa ta kauro yarima yace toh me yasa kake fada min aliyu ne yayi caraf baisan sanda yace saboda tana da muhimmanci juyowa yarima yayi ya kalleshi yana me daga gira yace me hakan ke nufi? Da sauri aliyu yace ina nufin duk abinda ya shafi uban daki na ai yana da muhimmanci tunda kai ka bada umarnin tazo kuma tazo ai abu ne me muhimmanci shiyasa aka sanar da kai.

Yarima yace me yasa hakan ke da muhimmanci a gurina? Munir yace saboda ita ta ceci rayuwar ka. Aliyu bai lura ba sanda yake fadin nikam da ace asma na ne da bazan iya boye tana da muhimmanci a guri na ba. Munir ne ya make kafadar sa yace kai bakuyi auren ba tukun yaushe ta zama naka? Aliyu yace kar ka damen ina na tsaya ? Munir yace asman ka. Aliyu yace yauwa. Ni dai in ina son mace zan iya bata komai na yi mata komai da zai saka ta farin ciki indai bai sabawa Allah ba domin farin cikin ta shine farin ciki na. Shiyasa dole ne mutum ya san matar da fada soayaiya da ita domin in ka zabi matar da ba daidai ba ka rushe rayuwar ka baki daya da na zuri'ar ka.

Yarima yace zancen me kuke yi ne ko zaku min karin bayani? Kama hannun aliyu munir yayi suka fice da gudu yana fadin sirrin mu ne ? Shiru yarima yayi yana nazarin me ya faru. Yace tausan bayan nawa fa? Jin shiru yasa yayi ajiyan zuciya yace yaran nan me suka mayar dani mikewa yayi ya fara rage kayan sa domin shiga wanka.

Ko da munira zata kwanta domin yin bacci ta da daddare ga mamakin bayin suka ga ta zaro bargon yarima daga jaka ta shinfida sannan ta dane abinta. Hansai ne tayi kokarin laka mata sata kamin wata baiwa ta rada mata a kunne cewa ba sata tayi ba bata aka yi hakan ya ingiza bayin sosai domin  su kokari suke hankalin yarima ya karkatu a kansu dukda juwa ba irinbyan matan zamani na bane basa aiki da tsiraicin su domin janyo hankalin da namiji saboda sunsan darajar kansu a matsayin su na mata. Dan a lokacin su in kaga mace tayi shiga ta yafa guale a kafada ko ta bar gashi a waje toh karuwa ce kuma ko karuwai basa karin gashi a lokacin hasali ma basusan da shi ko yadda ake yin sa ba saboda tsabar tarbiyar musulunci da suke da shi.

Washe gari tun safe yarima yana ta rubuce rubuce da karance karance kamar tsohon dan boko( disclaimer: ni ma yar boko ce kar ku dauka ina da wani abu ga boko ne) yayin da munira kuwa tana baccin ta a nitse kamar yanda ta saba mika tayi kamin ta fito domin tayi wanka ganin hansai tayi a kofa kamar ita take jira miko mata soso tayi tare da nuna mata abubuwan da ake tara ruwan datti da na wanke wanke kamar daro haka yake da kwanuka da abin shan ruwa a ciki tace ki wanke su tas bana son ji wani riha (sansano zai iya zama kamshi ko wari) daga garesu da su zamu ci sanwar rana.

Mikewa munira tayi tace ba damuwa na nayi aikin bane damuwa kina min magana da izza hansai daga kai tayi cikin isa tace kina da ja ne ? Daga kai munira ma tayi tace sosai ma kuwa tana tunkaro ta. Bayin ne suka taho suma suna jan ido wai zasuyi wa munira duka munira tace indai nine zan wanke abin cin sanwa toh saide yunwa ta kashe kowa ta wular da sosan ta fice zuwa wajen su asman ta.

Ko da ta shiga da fara'a bayi dayawa suka zo jin labari kadan daga cikin su gulma ne ya kawo su ko wacce da tambayar ta. Kin ga fuskan yarima da kyau? Da ruwan zafi ko sanyi yafi son yin wanka? Kin share masa dakin sa? Kwatanta mana kalan gadon sa? Hijabin (labule) dakin sa wani launi ne?  Wani irin turare yake kunnawa a dakin sa? Kin taba jin muryar sa? Ya taba kiran sunan ki? Fashewa da kuka munira tayi yanda yara keyi tace da bacin ran takaicin bayi zanji ko da tambayoyin masoyan yarima da na hadu da shi ai da sai na falla masa mari ina cikin zaman zama na dasu yimla na ya janyo min matsala yasa na shiga cikin gari aka daura ma...... tsayawa tayi da maganan da kukan taga kowa ya tsaya da abinda yake ita yake.kallo har wanda basu zo wajen ta ba ma sun tsay.

Masu aiki a can gefe ma kallon ta suka tsaya yi suna jiran su fahimci inda ta dosa. Mikewa tayi taci gaba da kuka tace ko na fada ma bazaku gane baaaaa😭 tana kokarin ta waske ta gudu. Asmee ne tayi caraf ta riko hannun ta tace zamu gane sosai ma kuwa. Kowa ya jinjina kai kamar kadangare hadiye yawu tayi tana kuka kamar yara sun kawo korafi tace ina cikin jin dadi na a bangaren sarauniya da gado na me laushi da mulki na da mutunci na ina daraja na kasa dani yasa aka kaini cikin marasa mutuncin bayi. Basu san kimar mutum ba.

Labarin duk abinda aka mata tun daga shiga bangaren yarima tayi wata tace wallahi har naji na tsanesu kiyi hakuri lailan mu wata rana  kece a sama da su. Asma tace muje naga inda suka sa kina kwanciyan ai ga katifar ki na da ba'a bawa kowa ba tunda kika tafi kuma sabuwa ce ke kika fara aiki da ita kinga nan bamu da gado kawai zamu dauka miki mu kai. Saura ma suka ce wannan haka ne yanzu ya za'a yi da shugaban bayi? Nana tace na san yadda za'a yi yanzu tana daki anjima zata fito dan suba mu toh tana son koko na dan haka kunun koko zanyi na kai mata dan na ja lokacin fitowan ta kuma zai kashe mata jiki kamin ta shaye ta fto kun fitar da katifan.

Haka ko akayi sanda nana ta tafi hada kunu asma ta kamo hannun munira tace zo muje can mu jira isowar su. A kofan gate din shiga bangaren yarima suka ci karo da aliyu yace barka da zuwa shuwagabanni na guda biyu harara asma ta aika masa tare da yi kwafa har sunyi gaba munira tayi baya tace shuwagabannin ka? Gyara zaman rigan sa yayi yace bara yarima yace na taho da dokin sa yau bai gita da wuri ba  kar ya fito ban fito da samir ba.

Yana wucewa gaba ya make bakin sa yace kai ali me ke damun ka ne kwana biyun nan. Wani abu ne yace baka de yi  karya ba shugaban zuciyar ka asma da kuma masoyiyar shugaban ka yarima saide bazai taba yadda sonta yake ba amma shekara nawa ina tare da shi idan zuwa yanzu ban fahimce shi ba yaushe zan fahimce shi?

TAKABBALAL LAHU MINNA WA MINKUM ALLAH YA MAIMATA MANA YAN UWA TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CEWhere stories live. Discover now