CHAPTER 21

608 96 19
                                    

Wajen karfe takwas bayi suka rako munira zuwa bangaren a hankali ta bude kofa ta shiga ta Ganshi zaune akan gado dagowa yayi ya kalleta kamin ya Mike ya fara takowa inda take. Daf da ita yazo yana kara matso da fuskan sa kusa da nata kasa ta kalla tara da rufe ido.....

Murmushi yayi ciki ciki kamin a hankali ya rufe kofa Dan dama abin da ya kawo shi kenan....Shiru shiru shiru shiru shiru shiru hakan yasa ta bude idon ta me zata gani kawai ta hango mutumin tsaye a gefen taga (window) yana kaifa bakin alkalamin sa. Dama da hagu ta kalla a Dan rikice kamin ta sosa kai ta nemi guri ta zauna tana tunanin ko me yasa ta rufe ido oho🤷🏻‍♀️

Latsa katifar tayi dukda ba irin namu bane me laushi amma in kayi comparing dinshi da muhallin ta toh laushi ne dashi na masifa balle ma an shinfida amarya sule abinka da gidan sarauta. Tsalle tayi ta fada tana washe baki kamin ta sauke ajiyan zuciya.

Kamin minti 2 mutuniyar har bacci ya kwashe ta ko kayan jikin ta bata rage ba... cire Mata takalmi yayi da mayafin dake jikin ta sannan shima ya nemi waje ya kwanta domin gobe zasu dauki hanya shida fata yake Allah yasa karshen matsalan su yazo ya basu ikon komawa masarautar unto lafiya ni untichlobanty nace ina AI ban yarda ba wannan zance da sake.

Washe gari tsaf aka shirya musu dawakai tunda muniran ma ta iya tuka abin ta. Dogarai guda uku aka hadasu a ciki harda wannan dogaren da ya kula da ita sanda take karama saide bata gane sa ba. Da yake a gefen ta yake tafiya hakan yasa tace ya shugaba ta fatan kin rayu cikin farin ciki ? Juyowa tayi ta kalle shi kamin ta Dan rage tafiyar dokin ta.

Dan murmusawa yayi yace "me hancin kosai" da sauri ta zare ido tare da furta ha kaiyamu(ya kallamu) gyada kai tayi domin kuwa haka take kiransa ya kallamu me hancin kosai saboda tama da faffadan hanci dukda hakan baisa yayi muni ba kuma koda ma yasa yayi muni ana zam da mutum Dan halin sa kuma Dan shine shi ba wai Dan kamar sa ko wani Abu da ya mallaka ba.

Washe baki tayi tana so tayi masa surutu saide kash bata iya magana ba. Yarima Wanda yaji shiru ne yasa ya juyo yaga ta Dan rage kafa ne domin kuwa dukda bata iya magana suna tafe tana nuna masa abubuwa tana karance wasu ya gane wasu kuwa saide ace masha Allah😁

Tsayawa yayi har suka tarosa kamin ya kalli bafaden yace me kake cewa amaryar tawa ne? Kallon kasa bafaden yayi ba tare da ya sauke kai ba domin kuwa shima da ilimin sa. Yace shugaba na ina tambayar ta ne yadda rayuwa ta kasance Mata domin kuwa ni na kula da ita sanda take karama. Kallon shi da kyau yayi don yasan dogarai biyu yaga munira na kulawa a iya zaman su sanda suke kahana a hankali ya tamabaya ta hanyar cewa  kamilu? Murmushi bafaden yayi yace kallamu ne ya shugaba na.

Yarima yace fatan kana lafiya? Kallamu ya amsa da Alhamdulillah... daga nan yarima bai kara da komai ba suka cigaba da tafiya wani kauye suka iso Wanda ake Kira da "BANDA TSAYAWA MAZA KA WUCE" wanda sun zo daidai domin kuwa ranan cin kasuwan su ne yau. Da shike zuwa yanzu ya kamata ku fahimci yarima yana son yin siyaiya Dan haka sai yace su shiga kasuwa dukda kuwa garin nan tace musu banda tsayawa nide nace ba ruwa na.

Koda suka shiga kasuwan kusan komai akwai hakan yasa ya siya yaduka kyawawa masu kyau guda biyar. Munira ne taga wani warware me kyau ys birge ta domin bata taba ganin irin shi ba ba gwal bane kuma ba azirfa ba... ba karfe bane gamar glass amma ba glass ba.

Hakan yasa ta je wajen ta taba. Mai kayan yana mai kallon gefe yace Mata uwar gida me zan baki? Shafa warwaron tayi yace Mata ranki shi Dade wannan ba orin Kagan da zaki samu a ko ina bane domin daga birnin sin (china) aka kawoshi kaf kasan nan mu uku ne muke saida irinshi in hade miki shi ne? Girgiza kai tayi domin bata da kudi da tanaso zata dauke amma tasan hakan zai zamto wa yarima matsala Dan haka ta koma gefen yarima tana rike da linzamin dokin ta wato yimla Wanda tayi masa gargadi na cewa kar yaja Mata matsa ko ya sameta da surutu ga zul ma biye da su sai hade rai yake yi. Lokacin yarima ya biya kudin yace ta duba ko akwai abinda take so bayan ta dudduba ne taga ba abinda take so Dan haka suka kamo hanya suka ci gaba da tafiya....

Lokacin har la'asar yayi Dan haka suka tsaya sukayi sallah bayan sun idar ne sun sake daukan hanya kamin su hau dabbobin su ne yarima ya kamo hannunta da sauri ta juyo ta kalleshi domin ji tayi kamar an anti Mata yawo da zare a jikin ta Saide wannan tunain ya kau lokacin da taga yarima ya ciro warwarayen nan guda biyu fari da kore yasa Mata daya a hannun dama daya a hannun hagu. Sannan ya saka zobe na maza Wanda yake shine hadin warwaron

 Sannan ya saka zobe na maza Wanda yake shine hadin warwaron

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Tsalle ta daka ta dale shi tare da ce GODE GODE dariya kadan yarima yayi San shi rashin iya maganarta ma birge ahi yake yace nagode zaki ce tace YA GODE yace ba ya gode ba na gode tace na

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Tsalle ta daka ta dale shi tare da ce GODE GODE dariya kadan yarima yayi San shi rashin iya maganarta ma birge ahi yake yace nagode zaki ce tace YA GODE yace ba ya gode ba na gode tace na..go..de? Yace eh tace na gode. Yimla ne yace ba sai kin fada mana kinyi aure Ba dokin yarima yace Dan bakin ciki ya mutu me yakai idon ka wajen gyaran murya kwai tayi suka yi tsit shide yarima yaji dokunan sun yi kararraki tana yin gyaran murya kuma sukayi shiru.

Tafiya suka cigaba dayi suna wajen wani kauye da yake shine kauye na 4 kamin a karasa masarautar unto me suna KAUYEN KACALA. Basu ankare ba sai gani sukayi yan fashi sun kewaye su. Ashe garin da suka wuce yan fashi ne suka kafashi kullum sai suce ranan cin kasuwa ne mutane su sayo kaya kana barin garin sai su biyo ka su kwace kaga sun karbi kudin ka kuma kayan su yana nan. Saide kuma kayan da zasu sayar ma me kyau ne ba jabu ba.

Ba tare sun sauko daga kan dawakan su ba yarima ya ce ma munira ta koma gefe yayin da shi da dogaren nan suka hau fada kyal kyal kake ji takkuba suna karo zul kuma ya tsaya ta gaba yana bawa uwar dakin sa kariya domin dabbobi basa butulci. Mutanen sunfi guda hamsin amma kamin kace me su yarima sunyi wa sama da 30 rauni. Bai ankare ba wani ya zame jiki ya nufi munira gadan gadan zaiyi faruwa da iya hakan yasa dokin ta zabure Wanda bayan su rami ne domin a saman dutse suke a wajen...

Ihu ta kwala lokacin da zata fada hakan ya janyo hankalin yarima da sauri ya diro daga dokin sa tare da rugowa da gudu yana kwala sunanta saide kamin ya iso wani yasa wuka ya soki kafadan yarima hakan yasa ya gidana zuwa guiwowin sa kamin ya fadi yana me doke kansa da wani dutse

NA SANI NA SANI BAKUSO NA RABSU AMMA HAKURI ZAKUYI KOMAI DA DALILI AI IN BA HAKA NAYI BA LABARIN BA ZAI TAFI YANDA YA DACE BA KUDE KU BIYO NI DAN YANZU AKA SHIGA USULIN LABARIN DOMIN DAGA NAN NE KOMAI ZAI FARA....
NAJI RUWAN COMMENTS DA LIKE FA...

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

miss untichlobanty 💕

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CEWhere stories live. Discover now