CHAPTER 31

601 94 20
                                    

DEDICATED TO phauxy_S Amalsunusi and Ummulaleeya ina ganin COMMENTS dinku na gode da kauna sauran masu karatu kuma in matukar godiya.

.....

Ita kam daga taimako shikenan sai abu ya zama masifa ? Nana ne tace uwar....ai laila kallon ta munira tayi lokacin da take kai loma baki domin abin ci suke ci nana tace me ya sameki ne yau naga kamar gaba daya bakya fadar nan dukuda kina tare da mu. Ajiyan zuciya munira tayi asma ta fada wa nana me ya faru sanda aka bada labari duk ta kidime kai kace itace tayi abin idon ta kamar zai fado. Tace uwar daki ya zaki yi? Asma tace uwar daki ? Ban gane ba tsuru tsuru dukan su biyu sukayi.

Dan dariya nana tayi tace sqnda fa zamu zo nake mukayi wasa itace matar sarki nice baiwa toh sqi nake kiran ta uwar daki sai abin yabi jikina. Asma tace toh kuwa kibi a hankali dan idan wasu sukaji kina kiran baiwa da hwar daki zai zamo miki matsala.

WASHE GARI.

Da zawalin rana aka aika a nemo munira sarauniya hauwa na neman ta nace toh anzo wajen anan gizo ke saka. Munira dai tun tana tsoro har ta dena idan ma mutuwa ne ai ko ba'a kashe ta yanzu ba dole zata mutu wanda basu san a dago da zancen mutuwan shi yafi kowa shiga ruwa kuma duk yadda wani yayi kokarin giduwa mata bata lokaci yake yi domin ita mutuwa bata bin mutum karo kuke ci da ita. Saide kuyi kicibis a hanya ta dauke ka tayi gaba.

Koda ta shiga daga can baya ta tsaya tana mai kallon kasa ba tare da ta sauke kanta ba. Sarauniya tace ku matso min da ita bayi mata ne suka matso da ita. Nana dake gefe gumi sai karyo mata yake kamar ita tayi laifi. Sai raba ido take. Sarauniya tace ya sunan ki? A hankali munira tace laila.

Sarauniya tace bakya tsoron mutuwa ne? Kallon idon ta munira tayi kamin ta girgiza kai. Gira daya sarauniya ta daga tana murmushi tare da sake kallon munira tana mai kankan da idanu wannan wace yarinya ce ? Tabbas irin ta take bukata kusa da ita wacce bata damu ta dauki risk ba indai har abinda takeson cimmawa zai cimmu domin kuwa ko masu magani sun ki daukan hatsarin yin wani abu amma ita tayi saboda jarumta.

Shafa inda munira ta tsula mata bulala tayi tace wani hukunci zan yi miki? Shiru munira tayi sarauniya tace bazakiyi magana ba? Nana ce cikin bari kai kace zazzabi ne ya kamata tace ya shugaban mu yar uwata tana da matsalan harshe ne shiyasa take tsoron tayi magana dayawa a gaban ki. Wani dariya tayi nide dariyan bai kwanta min ba tace.

Abinda kikayi jiya ya burgeni kuma kin cece rayuwa ta saide fa hannun ki da kika daga a kaina bazai tafi a banza ba. Nayi niyan duk wanda ya cece ni zan bashi duk abinda yake so amma tunda kin taka doka dole zanyi miki hukun ci dan haka ba duk abinda kike so zan miki ba. So nake ki dawo fada ta da aiki ki zamto daya daga cikin bayi na masu yi min hidima na kusa dani kinga dama gurbin mutum biyu ne kuma dayar tayi aure yanzu halima ce kawai ke tare da ni.

A ka'idar masarautar ba wanda yakai mata bayi masu yiwa sarauniya hidima matsayi dukda suma akwai matsayi matsayi haka a  bayi maza ba wanda suka kai na mai martaba matsayi.

Shiru munira tayi tana nazaei idan ta bar bangaren bayi ta dawo nan akwai fadawa dayawa. Ba kasafai zata samu mukullin kofar baya ba. Hakan na nufin bazata dinga fita ba sai da sarauniya aidan ma ta fita bazai yuwu ta bar inda sarauniya take ba balle ta nemi yarima. Kuma idan ta tafi ta bar asma da nana suna wahala bata kyauta masu ba. Dagowa tayi tace aide mu dawo da an uwa na. Sarauniya tace toh ai gurbin sauran bayi masu karamin matsayi ya cika gudan hamsin ne ka'ida amma 55 nakai bangare na.

Saide zan barki ki dinga kai musu ziyara duk sanda kike so suma zasu iya zuwa wajen ki idan basu da yawa kallon ta munira tayi zata yi ja hade rai sarauniya tayi da murya na bada umar ni tace kije kiyi tunani sai ki tattaro kayan ki ki dawo nan.

Nace ah ah yo me anfanin tunanin tumda ko ta yarda ko bata yarda ba dai zata koma wannan kawai ce mata kike taje ta shirya ta kintsa kanta. Godiya munira tayi sannan ta saka takalmin ta ta tafi nana ce tayi sauri tazo kusa da ita tace uwar daki me yasa kike bakin ciki ke da kika yi sa'a baza'a kashe ki ba. Kuma ai naga karin matsayi kika samu ko da baban ki ya sami labarin baki zama kuyangar sarki ba zai damu amma in ya samu labarin nan zai danji sanyi.

Ajiyan zuciya munira tayi kamar zatayi kuka tace bajaki gane ba ca min ido ja'ayi. Nana tace karki damu ina tare dake. Koda suka zo daki kwanciya munira tayi a cinyar asma murmushi asma tayi dan daga yanda taga fuskan nana tasan ba matsala. Bata lanarin yadda akayi sukayi tace toh masha Allah dan ture kan munira tayi tare da fadin kai laila kede ba son jiki ba ku tashi muyi sallah mu koma aiki.

Nana tace mance da ita har kin mance yanzu banda ita aikin mu. Kasa kasa da murya asma tayi tace toh wani aikin ma ta iya kai kace a daji ta tashi.
Muntsinin ta munira tayi ta mike suka fita da gudu yayin da munira ta lalumo takalmin ta na fata ta biyo su da gudu suna dariya.

.......

Bayan la'asar yarima ya gama karance karance zuwa yanzu za'a iya cewa aski yazo gaban goshi a kaeatun da yake dan kuwa yaci karfin dayawa daga ciki dan maida hankali yayi dare da rana banda sallah da cin abinci ba abin da ke tada shi.

Dan haka bayan yayi sallan la'asar yace wa ali zai je wanka a tabkin dake gidan wanda aka gine sa ya zamto kamar pool haka tunda sanyi na gaba towa bazai samu dama dinga linkaya ba. Haka ko akayi aika wa yarima munir gaiyata yayi dukda a zahiri ko magana yarima bai son yi masa yayi ta gwalesa a can cikin ranshi yana son sa.

Ko da akaje baya barin sa yarima kabir ya kirasu shi da jabir mutumin mu😁🤭 yana basu labarin nana su kuwa sai washe vaki suke ganin yanda dan uwan nasu ya fada cikin kogi akan munira. Ko da dan sako ya fadawa munir jabir ma yace zai biyoshi dan shima ta dade bai shiga tafkin ba.

Kallon kabir sukayi cikin tsokana munir yace toh mu zamuje muyi nitso da linkaya a tafkin ruwa a linkaya lafiya a tafkin kauna. Ashuwakin dake hannun sa ya jefi munir din ai kuwa cikin sa'a ya kauce yana masa gwaliyo.
Koda suka shiga ruwan hira munir yake ta zuba musu da umm kawai jabir me matsalar kai ke binsa dukda kuwa yau lafiya lafiya dashi yayin da yarima umar ko jin sa bayayi.

Yarima munir din ne ya watsa masa ruwa bude ido yarima yayi yace bari mana kamar ana ziga shi ya fantsala masa shima fancama masa yayi suka hau fancame fancame. Jabir aka antaywa ruwa a hanci yace tashin hankali aikuwa ya fara watsa musu. Sai suka matsa taron dangi kewaya ruwan ya fara suna binshi.

A bangaren munira kuwa ganin ba abin take yasa ta sandi jiki ta fice tana kalle kalle da labe labe dan kar dogarai su ganta. Su kuwa suna ganin ta kawai sun barta ne dan yanzu ta fisu matsayi da shike ita ta saba gani take ta musu wayo basa ganin ta sai washe baki take batasan daga ta wuce itama suke mata dariya ba.

Wata hanya ta gani wanda bata taba bi ba hakan yasa da rawan kanta tayi sidif sidif tabi wannan hanyan karan ruwa taji kamar yana haniniya cikin jin dadi ta ruga da gudu zata hango dogarai tayi suna bakin kofa san haka ta labe. Ita duk tunanin ta ruwa me zubowa daga saman dutse ne wato spring water.

Wani zubin zaman daji yayi ba tare da ta bata lokaci ba kamar yar biri ta dale bishiyoyi sai tana zuwa wajen ruwan taga maza uku ba riga ihu zatayi tana shirin rintse idanu amma dai ta tsaya sake kalla da kyau tayi taga tabbas yarima ne. Ta mance a sama rake kawai ta saki reshe akayi asha ruwan tsintsaye da ita sai jinta tayi a ruwan fadam.....

YAU DE NAYI  MAI YAWA DAN HAKA NIMA AYI MIN COMMENTS ME YAWA. SORRY FOR LATE UPDATE KAR A MANTA DA SHARING

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CEDonde viven las historias. Descúbrelo ahora