CHAPTER 29

465 79 23
                                    

Kwanciya munira ta sake yi lokacin an gaggauto da me magani anan take tace kiwa ya fice kamin ta duba muniran inda ta gano taci abin da jikin ta baiso ne. Saide bata samu tayi wa muniran tambayoyi ba domin kuwa bacci ya dauki muniran.

A wajen zabe kuwa yan Mata sai zumudi suke nace a de yi a hankali. Ba a wani bata lokaci ba sarki yazo tare da zama a inda aka tanadar masa ba wani bata lokaci ba ya zabi guda 5 daga nan aka bawa sauran da ba'a zaba ba kyautan kaya Wanda aka zaba kuma aka basu gyalulluka. Da zai nuna matsayin su sannan aka rubuta sunan su.

Daga nan aka ci aka sha sannan aka fara wasanni na gargajiya Wanda basu sabawa Shari'ah ba. Har rawar kafa yarima kabir yake ya zari jiki ya nufi koma bangaren sa tare da bada umarnin a je a cewa nanan sa tazo. Nace taka ahankali bawan Allah matar wani ce.

Yarima kuwa ko fitowa wajen taron baiyi ba domin kuwa a ganin shi shiririta ne bayida lokacin wani zuwa wajen taro yana ta kokarin sake sanin abubuwan da suka kwanta masa dukda bai Manta yaren turanci ba amma dai abin da ya karanta kam ya mance.
Kwana biyu ko aliyu ma ya masa iyaka idan ba Abu mai muhimmanci bane kar ya dame shi.

A zuwa akayi akace yarima kabir yace nana taje nana tana jin haka ta shige kasan gadon munira ta lufga wa kanta kaya ta buya Dan kuwa yasan tsananin rashin imani irin na yarima kabir. Beman ta aka yi ba'a same ta ba Dan haka aka sanar  da Dan aikan yarima cewa ba'a ga nana ba.

Koda salon ya iso garesa bai ma saka takalmin sa ba ya fito cikin zafin nama bafaden shi na biye dashi da gudu rike da takalma a hannu yana fadin uban gida na baka saka dangalafen (usilin sunan takalmi a hausa) ka ba. Ban kada gate din bangaren bayi yayi ya shiga aikuwa da gudu kowacce ke shigewa daki domin na farko dai basu da mayafi na biyu kuwa basusan ya musu rashin mutunci dukda sun raina sa sunsan yafi karfin su.

Yana wani haki yace ina ne dakin nanan? Baki na rawa jakadan sa yace ranka shi Dade AI basu da daki kowa me zaman kansa hadasu ake ita kuma dakin Wanda za'a zaba aka saka su sai bata zo zaben ba kamar yadda ka nemi alfarma wajen mai martaba.

Yarima kabir yace rike bayanin ka, ka nuna min makwancin ta. Da yatsa shugaban bayi ta nuna masa ya shiga tare da turawa ya rufe. Ganin munira yayi a kwance ya wani sauke ajiyan zuciya yaje ya zauna a gefen ta yana kallon yadda fuskan ta yayi fayau. Dauke kai tayi saboda kar ya ketare ka'idar Allah na maza su saukar da idon su ba yarinya zata wuce ka kura mata mujiya kamar maye ba.

Nace toh na nawa kuma kai da kake kokarin kashe Dan uwanka. Amma dai Allah yasa ka shiryu ko Dan wannan kyakkyawan niya.

A ranshi yace lallai ma wannan yarinyar aji dadi ce kallon ta ya sake yi kamin ya Mike fice daga dakin nana dake kasan gado bata ga fuska ba kafan sa kawai ta gani. Shi kuwa koda ya fita kallon shugaban bayi tayi yace nan gaba idan ina neman mutum ko mutuwa zaiyi a aiko min shi. Da sauri ta am sa da angama yarima yana fita daga bangaren bayi ta tabe baki Dan in sabo ne bayin gidan sun Saba da hali irin nasa.

Wajajen magariba munira ta farka a hankali ta bude idon ta lokacin nana tana ninke wasu kaya  ganin munira ta tashi yasa da sauri ta iso tace uwar daki.... munira tace ruwa nana tace ruwa? Ina ruwa ina ruwa Dan duk a rikice take. A hankali ta bawa munira ruwan har wani ya Dan zuba ya bata Mata riga. Tsumma ta Nemo ta goge Mata tana Mata sannu tare da fadin ya jiki shugaba na? Kina jin aman har yanzu? Akwai wani Abu da kike so ne? Kai munira ta girgiza tana me kokarin zama taimaka nana tayi ta zauna bayan ta Dan dawo haiyacin ta sai ta Mike domin tayi sallolin da ta shige Mata.

......

Kuyangun da aka zaba dai sai rawar kai sukeyi Dan ma washe gari ko wacce za'a bata sashin ta saide iya matsayin ki iya girman sashin ki da ywan bayin ki. A cikin su dai ba wacce aka bawa ma wani matsayi amma kai kamar tsohon keke nace mudai je zuwa.

Bayan kwana uku munira ta mayar da ruwan jikin ta tunda ta harar dayawa yasa ta ga yakamata ta fara neman mijin ta Dan abin ya kawo ta kenan ga sanyi yana dosowa ga abokanta suna waje.  Nana kuwa ba ba'ayi har yau bata ji hujjan da yasa sarki yace kar tazo ba. Shi kuwa yarima kabir dalilin da ya hanashi neman munira wacce ya dauka sunan ta nana shine aiyuka sunyi masa Dan kuwa ko wani yarima yana da wani aiki da aka Alaskan ta masa koda kuwa ba shi ne mai jiran gado ba.

Saboda su zama a suma sun San dawar garin koda iftila'I zai fada wa yarima mai jiran gado AI ba sai lokacin ne za'a fara kaisu fada kuma ana kokarin akoya musu yadda abin yake.

Kamar dai ranan farko yau ma munira ta biyo asma domin kai wa ko wani sashe kayan su da aka wanke. Bangaren    gimbiya hauwa suka fara zuwa tana bacci bata ma tashi ba kamin suka wuce bangaren yarima munir (Dan autan su yarima Wanda suke shiri... duba CHAPTER 3 in kin/ka manta shi. )

Koda suka bashi kayan godiya yayi wa asma yace kin yi kawa ne? Tace eh cikin sabin zuwa take yace aiya yana murmushin sa da ya Saba Dan yadda murmushi ke tsada a fuskar yarima Umar haka take arha banza a fuskar yarima munir. Kamar yadda ya Saba tukuici ya bawa asma yace nagode sannan ya taje kansa ya fice daga bangaren yayin da suma suka ajiye kayan bafaden sa suka dauka suka shigar dashi ciki.

Bangaren yarima Jabir suka wuce suna shiga da assalam...... sukaji ance koma uban waye ya koma cikin tsawa da sauri asma tayi reverse suka koma inda  suka fito abin ya motsa kenan Dan kuwa duka yarimomi ukun nan kowa da zafin sa saide yarima Umar da kabir suna yin na masu hankali shi kuwa jabir akwai lokacin da mahaifin su ya dauka ko aljanu sun shafe shi ne Dan ana zaune lafiya kawai sai ya haukace muku ya dinga diri yana girgiza azaran daki.

Duk abinda ya samu kusa dashi barar wa yake yi wani zubin ya raruma ya jefe ka. Abinda ya fado kefe na ne yasani sauron dagowa daga typing din da nake naga yarima jabir yana harara ta yana huci kallon gefe nayi naga AI Kofi ya wullo min dauka nayi sanda na tabbatar kofa a bude na turbune fuska nima na jefe sa AI kuwa tsakiyar kansa ta fada tayi masa mangare ban bata lokaci ba ma cikawa zani na iska (dukda ban saka zani😁) yo wa zai tsaya mutumin da ake ganin yana da matsalar kai. Mai hankali AI sai mai hankali.

Ba wani bata lokaci su munira suka wuce bangaren YARIMA UMAR ita de munira bin asma take Dan tasan in tana tare da asma shine zata samu daman shiga ko ina. Sallama sukayi aka amsa tare da basu izinin shiga aliyu ne  a parlourn Wanda darduma ke shifide gwanin sha'awa yana dauko zani da yarima zai rufe jikin sa Wanda zamu iya cewa kamar towel haka.

Gaishe sa asma tayi kamin suka ajiye kayan da suka kawo sannan suka fito su ukun suka a tare. Gyaran murya yarima yayi tare da miko hannun sa ta bayan labulen da ya raba parlourn sa da wajen wankan sa juyowa munira tayi kamin ta tsaya a take

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

Gaskiya fa a dinga COMMENTS ko na koma update sati sati🤭

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CEWhere stories live. Discover now