CHAPTER 23

504 76 8
                                    

Mikewa mai kudi yayi yace nide ba wannan ba da kika gudu kike nema ki ci min mutunci ba ni kika yiwa ba kanki kika yiwa yar uwar ki malika yarinya mai hankali hade rai maman laila tayi ...

Dan masani yace malam bashari yace danshi bazai auri yarinya da bata da kamun kai ba Dan haka na cika miki warakan fada (yana nufin form) ki shirya nan da mako biyu za'a yi koyan tarbiya da karatu a fada kamar yadda aka Saba duk matan da suka yi shekara 16. Sarki zai zabi guda 3 su zama kuyangu saura kuwa su zaba ko su zama bayi ko su dawo gida. Idan kuwa suka dawo gida ba zasu aure ba sai bayan shekara 2. DAN HAKA DOLE KI ZAUNA HAKA AL'ADAR MU TAKE.

Yana kaiwa nan ya bar wajen yana kara bata rai saboda baison kayan takaici. Don kuwa laila ta sha ballo musu masifa tun yana dauke kai har daga karshe ya fara Mata fada har ta kai ga duka domin ko guduwa nan da tayi sati daya da ya wuce wani matashi suka nemi auren ta amma iya Wanda take so daban hakan yasa kwana biyu da suka wuce sukabi dare suka gudu toh daji suka shiga suka 'buya sukayi kwana daya.

Washe gari suka ji wasu mafarauta suna hiran guduean su da neman su da ake hakan yasa sukayi kokarin barin garin saide daidai wajen da su munira suka tsaya suka yi wannan fadan itama a wajen ta subule ta fado saide gefen da ta fada duwatsu ne ba bishiya ba hakan ya daki kanta a wajen me hadari ga ta zubda jini dayawa hakan ya kawo ajalin ta. Batun saurayin lailan kuwa ko ni misa untichlobanty bazan iya Baku wani takamammen bayani ba.

Bangaren yarima kuwa wannan mafarautar bayan sun gama farautar su ne zasu koma gida tunda sanda su laila sukaji hirar su wajen la'asar ne kamin su yarima suzo bayan zasu koma kuwa magariba ne suka tsinci yarima a take suka gane shi domin kuwa an taba gaiyatar su wasan farauta da sallah.

Inda yarima ne ya shirya Dan haka kuwa sarai sun sansan kuma dam asun Sami labarin tun hatsarin da yayin nan dsn haka ba tare da bata lokaci ba suka dauke sa basu tsaya ko in aba sai masarautar unto wajen biyun dare suka isa a take aka basu masauki bayan sun bada yarima Wanda a take aka fara kokarin yi masa magani.

Gari na waye wa aka kawo musu kyautuka masu yawa yayinda ake tambayan su abin da ya faru.  Suka ce sude iya abinda suka sani suna dawowa daga farauta suka ga yarima kuma sun gane shi Dan haka suka hanzar ta wajen kawo sa gida.

Nan dai sukayi bankwana suka bar garin. Wajen sha biyun Rana sarki ya na tattaunawa da mai magani mai martaba yace yaya ake ciki da yarima ajiyan zuciya mai maganin yayi yace mai martaba saide godewa Allah Dan kuwa yankan takwabi guda biyar ne a jikin sa 1 akan kirjinsa sauran kuma a hannun da baya saide bai taba masa wani Abu a cikin sa ko zuciyar sa ba. Dukda dai ta taso masa da wannan gubar da yaci tun baya kuma da alamu karfin ta ya dawo sabo. Sarki yace subhanallah Da fatan dai baya cikin hadari yanzu?

Ajiyan zuciya mai maganin ya sake yi yace wannan dai bazan iya cewa komai ba domin kuwa ya doke kansa sosai kuma jini ya cure masa a kwakwalwa Dan haka idan aka ci sa'a bai Sami tabin kwakwalwa ba toh koh ma me ya same sa kar ayi korafi Dan sa'a da ikon Allah ne kawai zaisa bazai samu tabin kai ba.

Salati sarki yayi yace nagode amma ina neman alfarmar ka. Mai maganin yace ba sai ka nemi alfarma ta ba mai martaba. Murmushi kawai sarkin yayi yace fatan bazaka fada wa kowa wannan magana ba ko sarauniya har sai ya farka mu ga yadda abin zai kasance.

Mai maganin nan yace an gama ya shugaba na sannanr ya dauki jakan sa ya tafi. Zaman dirshen sarki yayi yana mai addu'a kar Allah ya bari wani Abu ya Sami dansa.

Bangaren munira kuwa lallabata mahaifiyar laila ta dinga yi kan ta hakura ta je fada sannan tabi a hankali kar tayi laifin da zaisa a fille mata kai ko a Mata bulala. Suna cikin zancen ne cikin lanbun nan sai ga yayarta ko yar uban ta tazo sai murmushi take kyakkaywa da ita na fitan hankali har tafi munira da lailan ma tunda kamar su daya.

Murmushin ta ko kai mace ka kalla sai ya tafi dake balle namiji. Hakan yasa baban su baya bari ta fita saboda gudun fitina. Tace yake yar uwa ta nayi farin cikin dawowan ki fatan kina cikin koshin lafiya? Kin tatar min da hankali na. Me yasa kika bar gida?

Munira tace wanne zan fara amsawa ? Maman ta ne tayi yake tace kinga yar uwar taki ta sha gajiya ki barta ta koma ta huta.  Sunkuyar da kai tayi tace toh sanna ta rike hannun munira tace anjima zanzo muyi hira murmushi muniran ma tayi ta koma dakin ta bayan ta tafi maman laila tayi yake tace a dinga yi a hankali kinji ko? Ta amsa da toh Dan kuwa ta gane gargadi take Mata da ta kiyayeta ka tayi wani Abu ma yarta laila wacce taje munira.

Tashi tayi itama ta koma dakin ta tabar maman laila zaune a lambu tana rufe dakin ta tayi murmushin nan nata mai dauke ido tare da fadin SANNU DA DAWOWA LAILA.

KAR A MANTA A SAMBADO COMMENTS FA.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CEWhere stories live. Discover now