CHAPTER 8

786 99 10
                                    

Shiga daki tayi kamar ta kwanta ta leko ta kasan kofa tana hawaye ganin yadda mahaifiyarta ke dannan busasshen gurasa da ruwa.

A takaice de yau ma cikin wani mugun hunturun sanyi suka kwana da zazzabi khadija ta kwana saide bata bari kowa ya sani ba haka ta dinga gumi har gari ya waye ya lafa mata.

Sadiya ne tace uwar daki na babu ruwan zafin da zaki yi wanka saboda bamuda itace da zamu tafasa. Mikewa khadija kuwa daki ta shiga ta dauko wata sarkin gwal yar karama Wanda tun na kakar ta ne ta bawa mahaifiyar ta, mahaifiyar ta ta bata itama tana so ta bawa yarta saide lafiya shine a gaba mikawa sadiya tayi tace taje ta siyar sai ta siyo musu gawayi da Dan kayan abin ci.

Sadiya tace bazan iya sayarwa ba uwar daki wannan ne kadai abin da ya miki saura duk kin sayar da kadarar ki. Murmushi khadija tayi tace idan da yawon rai wata rana zan siya abinda ya fishi ma. Turo baki munira tayi tace mama Dan Allah kar ki sayar kawai ki fadawa baba cewa ba'a bamu hakkin mu.

Khadija tace kinga duk yawan mutanen garin nan ? Daga kai tayi khadija tace toh dukan su baban ki ne me kula da su kinga be dace mu dameshi ba ko? Munira tace tohe yasa shi zai kula da su bayan kowa da baban shi? Mahaifiyar  tace saboda baban ki sarki ne. Kinga gone kije wajen babban mamar ki sarauniya ki yi Mata aiki karki dawo sai dare kinga zaki samu kici abincin safe Rana da dare.

Make kafada tayi tace ni gaskiya babu inda zani idan na tafi wa zai kula da ke. Dariya khadija tayi tare da mikewa ta tsaya tace neera kalle ni da kyau baki ga ni babba bace ? Bana bukatan a kula da ni saide ni in kula da ku yara. Tace ni de bazani ba. Bata rai khadija tayi tace in bakije ba karki kuskura ki kara min magana. Neera ne ta riko hannun maman nata tace toh kiyi hakuri mama zan je.

Murmushi khadija tayi Mata tace Allah yayi albarka maza jekiyi wasa da maimuna. Da gudu ta fita dukda ko ba wasan zata je yi da maimunan ba domin kuwa maimunan yar gidan marka ce Dan haka kuwa basa jituwa.

Hanya kasuwa ta nufa tana waige waige tana neman sadiya hango ta tayi tace yaya sadiya  duk da sadiya baiwar mahaifiyar ta ne ita ganin yar uwa take Mata kuma kamar kawaye dukda ko sadiyan shekaru 17 gareta neera kuma 5.

Tace yaya sadiya Dan Allah kar ki siyar da sarkan. Sadiya tace in ban siyar ba ya zamu yi mu samu muci abinci ? Tace akwai hanya mana kinga gawayin nan da aka bamu ko mukaiwa masu gasa nama da irin sa suke aiki mu kuma sai su bamu mara  hayaki rabi sai su bamu canji a canjin sai muyi kasuwan ci kinga yau ake cin kasuwa.

Cikin washe baki sadiya tace kaji yar dukurkura me tunanin manya shiyasa nake sonki hau baya na mu tafi. Rugawa sadiyan tayi da gudu suna dariya abinsu suka shiga kasuwa. Bayan sun canjo gawayin sadiya tace amma sana'a me zamu yi ?

Me zai hana in yi gyaran takalmi tunda sana'ar baba name kamin a maida mu bayi. Munira tace hakan ma yayi siyo kayan dinkin suka yi. Suna tafiya ta yan hatsi neera tace yaya sadiya muna da canji ko? Tace eh kallon munira tayi itama munira kallon ta tayi tace kina tunanin abinda nake tunani tace sosai ma.

Tafawa suka yi suka sayi harsin su kwano biyu Wanda iyakar kudin nasu kenan. A boye suka je suka hada kunu na kwano daya niki niki sadiya ta dauko suka koma kasuwa. Irin fatake sun kwaso yunwa su tsaya su siya, lazo gyara takalmi kaga ana siya kaima ka siya kamin kace me ya kare wani suka sake yi suka dawo shima bayan la'asar sun sayar shi kaf.

A gida kuwa khadija ta damu Dan taga dadewan sadiyan yayi yawa yukawa tayi a Kira mata munira aka ce AI bata bangaren sarauniyar tace kun tabbata ita da maimuna fa suka tafi. Baiwar ta tabbatar Mata cewa bata nan. Murmushi tayi Dan tasan dama ba shiri suke ba kuma itan ma bata son muniram tana hulda da maimunan saboda munafurcin ta saide bata so ace ta hada yan uwa fada ne.

Shiga daki tayi ta kwanta bayan ta sha ruwa Wanda shine abinda ke cikin ta tun gurasan jiya. Mutanen kuwa sai dadi suke ji Dan kudin da suka samu zai ishe su abinci da garwashi na sati.
Munira tace yaya sadiya in munje gida karki fadawa mama na kinga shiyasa ma muka rufe fuskar mu idan ba haka ba zata hanamu. Sadiya tace maman kin ne sanyin ta da tausayin ta yayi yawa.

Munira tace kamar kin sani wallahi kuwa gashi idan nayi magana sai ta gwabe ni wai zan jawa kaina matsala sannan.... sadiya ce ta karashe Mata da karkiyi fice a cikin saura. Dariya sukayi tace kema har kin haddace balle ni da ake maimatawa.

Guntun kunun da sukayi suka kawo wa khadija ta sha kudin da suka samu sadiya ta miko Mata tace ga shi na siyar amma sun karyar da sarkan kuma Rabin kudin suka bani khadija tace ki rike sadiya aike kike siyo abubuwa na yarda da ke. Godiya sadiya tayi ta fita suka tafa ta mutuniyar taku.

Bayan kwana uku rayuwa ta Dan ware musu baza dai ace suna shakatawa ba amma sun dena kwanan yunwa. Sadiya da munira sanye da sabin kaya domin yau ana bikin babbar yar sarki wato yar sarauniya. Kaf yaran baban dama ba Wanda suke son muniran sai zainab din kuma gashi zatayi aure shiyasa munira baki har kunne.

Bangaren sarauniya taje ta dale cinyan baban ta saboda ita ce karama sai raba ido take tana kalle kalle ana ta yi Mata wasa. Bayan a daura aure akace sarkin gaba daya masarautar wato masarautar unto yazo da yaran sa maza biyu Umar da munir domin ya fito zagaye kamar yadda ya Saba shine yace bara ya fara da garin banty tunda an aiko gaiyarar auren.

Wasanin al'ada ake lokacin da yazo Dan haka a farfajiyan ya zauna yana kallo. Munir na zuwa ba bata lokaci ya nufi wajen abinci, shi fa tun yana yaro shashasha ne. Umar kuwa gefen yayan munira me suna Adam ya zauna Adam cewa Adam shine Dan marka na farko sai maimuna dama yara 2 gareta.

Adam na da shekara 12 a lokacin yayin da Umar ke da 14. Adam ne ya kalli Umar yace mai zaka sha ruwa? Ko kallan sa Umar bai yi ba. Can yace yaya sunan ka? Nan ma be kula shi ba. Can ya sake cewa kai yaro na nawa ne a yaran mai martaba? Sai lokacin ne Umar ya juyo yace Kaine yaro sannan ya juya abin sa.

Abin ne ya batawa a dam rai baisan sanda yace muyi wasan doki idan ka ci ka kwashe sadakin yaya ta idan naci daga yau nine yayan ka. Umar yace idan wasan doki ne ko ban rike linzamin doki na ba zan ci saide ka zabi wani maimuna ne tace toh kuyi na mashi mana Umar yace bismillah. Adam da ya manta bai iya ba yace ba matsala. Ashe wani sankira yaji zancen su kawai ya bada shela. Gashi ba halin bangaren gidan su munira suce basu yarda ba za'a ga karanci su amma sadakin da aka basu ne na fitar hankali harda dawakai da gidaje.

Sarki kuwa abin ya burgesa hakan yasa yace idan har gidan su munira ne suka ci toh zai bawa Adam din mashin sa.

To be continued...

TOH FA KAKA KARA KAKA, SHIN WANI BANGARE NE ZASU CI? SU YARIMA KO SU MUNIRA? KU BIYONI DAN JIN YADDA ZASU KAYA.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CEWhere stories live. Discover now