CHAPTER 46

513 81 20
                                    

Wani bafaden yarima kabir ne ya daga hannu ya dauke ta da mari. Cikin zafin nama aliyu shima ya falla masa mari yace na haramta maka taba mata ta kana ji ko? Dafe baki yan mata sukayi bai ma lura da mai yace ba asma dake kuka tsayawa tayi tana binsa da ido shin ta sake fashewa da kuka ne ko ta fara zubo masifa ne wato itama aura mata aliyu aka yi? Toh nana kuma ko wa aka aura mata oho ? Bata san aliyu yayi maganar bane cikin kare abin da yake so.

Fitowa yarima yayi farfa jiya ya bada umarnin mutum daya ta shigo daga cikin matan. Rabi ce ta shigo tare da gaishe da yarima. Yace yimin karin bayani tace ya shugaban mu yarima kabir ne ya auri nana kamar yadda nasan ka sani shine da mukaje daukar ta domin a mata gyare gyare sai aka ce ta fita da gudu da muka tambayi habu shi da sabo sukace nan ta nufo lokacin muka ga asma sai muka biyo ta.

Rike hannunshi munira tayi bata ma ankare da hakan ba tana girgiza kai idon ta har ya fara yin ja. Shafa kanta yarima yayi a kunnan ta yace barta taje zan sami kabir nayi magama dashi nasa ya sake ta kar ya takura mata kinji? Ba dan taso ba haka ta falfala da gudu ta shige dakin yarima fada gado tana me kara matsar kuka harda sauti tare da yin cilli da hijabin ta.

Nana kam ta jika hijabin da asma da rufa mata. Kama nana sukayi wacce ta zama abin tausayi ta ma dena sauti kawai hawaye take yi irin anci ta da yakin nan. Asma kuwa gardama ta soma tana kokarin tare hanya aka riko ta tana fincika ana janta.

Wani mikewa munira tayi ta zauna a zabure kamin ta fito da gudu da karfi tana fadin nana ki yafe min ki yafe min. 😭 dan Allah ki yafe wa uwar dakin ki lokacin har anyi nisa da nana tafiya akayi da asma yarima ma ya ja munira suka koma daki. Aliyu kuma ya rufe kofa bayan kowa ya fice zuciyar shi na kunan ganin yanayin yan matan.

Dama ita rayuwa haka take yau kana farin ciki gobe kana kuka saide tawakkali kawai da yarda da Allah shi ne zai baka mafita. Haka aka sa nana yon wanka aka mata shafe shafe. Ba'a ankare da lokaci ba har anyi walima anan aka kaita gaban sarauniya cikin lullubi sarauniya ta shafa kanta tare da saka mata albarka anan aka barta tayi sallah kamin aka dauke ta aka dangana da ita bangaren yarima kabir ko wani taku yana bugawa ne da zuciyar ta. Hakanan kamar wasa aka ajiye ta a bangaren yarima kabir a matsayin amarya wani zubin ji take kamar in ta fashe da dariya za'a ce ai wasa ake mata.

Abinda yasa ta hakura ta zo shine sanin baza'a rabata da uwar dakin ta ba amma abu daya da ke damun ta shine yanzu fa tafi uwar dakin ta matsayi tunda tana da yanci kuma yarima take aure? Wannan wani irin wasa ne haka? Hannun ta taji an riko tare da murya sananniya ga kunnuwan ta aka ce uwar daki na daga yau nice zan dinga yi miki hidima daga gyalenta tayi suka hada ido da lantana bata san sanda ta sake fashewa da kuka ba.

Yanzu kam bata ma san kukan me take yi ba. Iso da taji ana yiwa yarima ne yasa lantana goge mata hawaye tare da sauke mata lullubi tace kar kiyi kuka ki bata wa shugaba rai ya ke uwar daki na. Da sallama yarima kabir ya shigo sai murmushi yake yi yana wani gyara zaman rawanin shi sallama bafaden shi yayi masa ya sallame sa.

Sallaman lantana yayi ya kasance daga shi sai hajiya nanaaaa. Zama yayi a gefen ta tare da cewa matar kabir da sauri nana ta toshe kunne jin yanda ya kira sunan sa ga tsau ba kara ba karantawa wanda doka ne yasa wai ya haramta a ambaci sunan sa ko da kuwa zancen sa ake saide ace yarima babba da yake ta saba sanda take baiwa sai ta dauki lokaci kamin ta saba da wannan sabon rayuwar.

Dan dariya yarima kabir yayi kamar fa ba mutumin ku ba ya sa hannu ya cire hannun ta da tasa a kunnen ta. Shide yana dan mamaki gyaran da aka yi mata ne yasa tayi haske lokaci daya ko yaya dan kuwa nana zabiya ce dan haka tafi munira haske nesa ba kusa ba saide inda Allah ya taimake ta da yake baban ta ne zabiya sai ta dauko kamannin mahaifiyar ta kalan gashin ta kuma sai ya kasance ja me duhu wanda aka fi sani da maroon.

Yace kinga na miki ba zato ko na aure ke ko sanar dake banyi ba hakuri na kasa yi saboda lokaci daya sanki yayi min illa. Ki tashi kici abinci kizo ki kwanta kuma ki dena kokarin kwace hannun ki ba abinda zanyi miki dan nasan a tsorace kike.

Duk da nana bata san dalili ba amma jin haka yasa hawayen ta tsayawa cak harda sakan murmushi da sauri ta mike cikin jin dadi tana me yaye mayafin dake kanta wanda ba ko dankwali ko kitse mata basu yi ba da suka wanke ranta wasai tana jin dadi saide fa dai dai wannan lokacin ne annurin da ke kan fuskan yarima ya dauke cikin zafin nama ya riko hannu nana ya lika ta da gini tare da kai wuka kusa makokoron ta har bari yake da wani mugun tsawa yace wacece ke?

Nana bata ma san saki fitsari ba tanajin kamar zuciyan ta a makokron ta yake. Cikin wani tsawa yace zakiyi magana ko kuwa? Bakin nana sai bari yake gumi na digo mata kawai ta kafe shi da ido ta kame duk jikin ta. Bafaden shi ne ya kwankwasa kofa tare da fadin shugaba na kana bukatan wani abu ne?

Ai cikin tsawa akace mai bace daga nan hakan yasa nana fashewa da kuka me sauti tana fadin uwar daki na uwar daki na bana son na zauna anan. Zare mata ido kabir yayi yana toshe kunne daya wai bayason jin muryarta.

Da sauri ta rufe bakin ta tana gunjin kuka, cilli yake son yi da ita amma musulunci ya hana cin zali juyawa yayi ya fita tare da danna wa bafaden sa kira da gudu shamsu yazo.

(na manta sunan shi kuma banida lokacin dubawa dan haka zamu kirashi shamsu)

Da gudu ya sheko kabir yace a nemo min rabi ba bata lokaci rabi ta iso daga gani ta fara bacci a gigice tazo yace ina matata? Baki na rawa tace shugaba karde guduwa tayi da tsawa yace wa kuka sa min a daki na tace nana aisha kamar yadda ka yi umarni ya shugaba na.

Hanya ya nuna mata tana shiga yace wacece wannan rabi tace itace nana wanda ka aura shugaba na yana jin haka yace kowa ya koma ya kwanta dan zuwa lokacin bayi dayawa sun leko ganin yanda aka zo aka fafuri rabi wanda ita ce shugaban bayin barin su za'a iya cewa matsayin ta daya da ladidi.

Rufe kofa yayi ya nuna guri a kasa yace maza zauna zama nana tayi yace suna. Tace na...nah hhh yace nana nawa ne a bangaren bayi tace ni daya ce ake cewa nana. Yace toh ita ina take nana dake share hawayen dake zubo mata tace wa..ce? Yace ita nana tace wa? Cire rawanin shi yayi tare da yin tagumi tabbas wannan tambaya ce me muhimmanci wa?  Can de yayi shiru yana nazari ko aljana ya gani?

Kai hakan bazai yuwu ba ai su shamsu ma sun ganta lokacin kuma ranan zabe ma ai ya gan.... hakane fa da sauri ya kalli nana yace wacce tayi jinya ranan zabe shiru nana tayi kamin tace ranan suna da yawa ai... akwai.... bilki...laila...nafisa...hindatu...jummai...lami...amatu bayan an dawo daga zaben... ni ni kaina bansan adadin su ba wata ... har suma ta yi dan... ba'a zabe ta ba..

Tsaki yayi yace asarar banza me yasa lokacin da na aika jar a barta taje bata je ba. Kara shigewa lungu nana tayi tace....ance min kar naje ku...ma ban ban je bbba. Naushin kwanukan abincin yayi ya fice daga dakin tare da shigewa daki na gaba ya ma rasa me zaiyi ji yake kamar ya jashe nana dan bakin ciki. 

Bangaren su munira kuwa ko sanda yarima ya mayar ta daki rike hannun sa tayi gam tare da kallon idon sa tace.....

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU wato

Miss untichlobanty 💕

KWARKWARAR SARKI MATAR YARIMA CEWhere stories live. Discover now